Ministan mai na Nijar ya gana da Jakadan Iran a Yamai
Published: 10th, October 2025 GMT
Ministan albarkatun mai na Jamhuriyar Nijar Sahabi Oumarou, ya gana da Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Nijar.
A yayin ganawar, bangarorin biyu sun tattauna kan muhimamn batutuwa da suka shafi alakoki da ke tsakanin kasashe biyu da kuma yadda za a kara inganta su.
Sannan kuma sun yi musayar ra’ayi kan hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta fuskar cin moriyar juna.
Jamhriyar Nijar da Iran suna da kyakkawar alaka ta diflomasiyya, kamar yadda kuma suna yarjeniyoyi da dama da ayyukan hadin gwiwa a fagage daban-daban na diflomasiyya, cinikayya da bunkasa harkoki tattalin arziki da kimiyya da fasaha.
Bangarorin biyu sun jaddada wajabcin ci gaba da tuntubar juna domin aiwatar da dukkanin yarjejeniyoyi da aka rattaba hannu a kansu a tsakanin kasashen biyu a dukanin bangarori, musamman ta fuskar harkokin makamashi da cinikayya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Trump ya gabatar October 10, 2025 Guterres ya jaddada wajabcin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza October 10, 2025 Madagascar: An Yi Kiran Gudanar Da Yi Wa Shugaban Kasa Zanga-zanga October 9, 2025 Jagora: A Yi Amfani Da Hanyoyin Sadarwa Na Zamani Domin Koyar Da Muhimmancin Salla October 9, 2025 An Fara Aiki Da Zango Farko Na Tsagaita Wutar Yaki A Gaza October 9, 2025 Shugaban Kasar DRC Ya Kira Yi Takwaransa Na Rwanda Da Ya Daina Taimakon M23 October 9, 2025 Jagora: Dole Ne Ga Hukumomin Da’awa Da Malamai Su Kula Da Batun Tsayar Da Sallah A Tsakanin Al’umma October 9, 2025 Babban Kwamandan IRGC Ya Jaddada Batun Wurga Makiya Cikin Mummunar Nadama October 9, 2025 Hamas: An Cimma Yarjejeniyar Karshen Kan Dakatar Da Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Gaza October 9, 2025 Kungiyar Jihadul-Islami Ta JInjinawa Al’ummar Falasdinu Kan Juriyarsu A Lokacin Yaki October 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Shirin Zaman Lafiya Da Ya Hada Da Kawo Karshen Kisan Kiyashi A Gaza
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Iran tana goyon bayan duk wani Shirin zaman lafiya da ya hada da dakatar da kisan kiyashi a Gaza
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana goyon bayan duk wani mataki ko wani yunkuri da ya hada da kawo karshen yakin kisan kiyashi a Gaza, janyewar sojojin mamayar Isra’ila, shigar da kayan agajin jin kai, sakin fursunonin Falastinawa, da kuma tabbatar da dukkanin hakkokin Falasdinawa.
Haka kuma ta kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na mai goyon bayan halastacciyar gwagwarmayar al’ummar Falastinu samun tabbatar da ‘yancin kai, ta yi amfani da dukkanin karfinta na diflomasiyya a cikin shekaru biyun da suka gabata, musamman a matakin yanki, kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da Majalisar Dinkin Duniya, wajen matsin lamba ga yahudawan sahayoniyya da magoya bayansu da su dakatar da kisan kiyashi da kuma janyewar ‘yan mamaya daga Gaza.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi juyayin tunawa da manyan shahidan gwagwarmaya, inda ta jaddada nauyin da ke wuyan kasashen duniya na hana duk wani cin zarafi daga ‘yan mamaya, tare da yin kira ga dukkan bangarorin da su yi taka tsantsan da yaudara da karya alkawari da sahayoniyya suke yi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Faransa Da Jamus Da Kuma Birtaniya Sun Bayyana Aniyarsu Ta Ganin An Farfado Da Tattauna Da Iran October 11, 2025 Kungiyoyin Falasdinawa Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 11, 2025 Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya October 11, 2025 Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta October 11, 2025 Putin: Natanyahu Yana Son Warware Matsaloli Da Iran Cikin Lumana Ba Tare Da Yaki Ba October 10, 2025 Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha October 10, 2025 Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa October 10, 2025 Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka Rusa A Arewacin Yankin October 10, 2025 Rahotanni : Isra’ila ta fara janye dawa wasu yankuna na Gaza October 10, 2025 Amurka ta kakaba wa wasu kamfanoni 50 takunkumi saboda sayen man Iran October 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci