Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya
Published: 11th, October 2025 GMT
Kasar Venezuela ta yi kira ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya tabbatar da cewa Amurka tana yin barazana zaman lafiyar duniya
Kasar Venezuela ta yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya amince cewa; Lallai Amurka tana yin barazana ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, saboda yadda sojojin Amurka suke shisshigi a tekun Caribbean, wannan batu ya zo ne a yayin zaman gaggawa na majalisar a jiya Juma’a.
Wakilin dindindin na Venezuela a Majalisar Dinkin Duniya, Samuel Moncada, ya ce: “Suna ba da shawarar ayyuka uku ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya: Na farko, amincewa da barazanar zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa da sojojin Amurka suka haifar a cikin tekun Caribbean. Na biyu, daukar matakan da suka dace don hana ci gaba da tabarbarewar al’amura. Na uku, a amince da wani kuduri da ya wajabta wa dukkan mambobin su mutunta ‘yancin kai da daukan Venezuela a matsayar kasa mai cin gashin kai”.
Jami’in diflomasiyyar na Venezuela ya zargi Amurka da aiwatar da kashe-kashen gilla, yana mai cewa “gwamnatin Amurka ta amince da kai hare-haren bama-bamai kan kananan jiragen ruwa guda hudu a tekun Caribbean, inda suka kashe fararen hula 21 da ba su dauke da makamai.” Ya bayyana wadannan ayyuka a matsayin “kisa ba bisa ka’ida ba” ba na kare kai ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyoyin Falasdinawa Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 11, 2025 Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta October 11, 2025 Putin: Natanyahu Yana Son Warware Matsaloli Da Iran Cikin Lumana Ba Tare Da Yaki Ba October 10, 2025 Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha October 10, 2025 Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa October 10, 2025 Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka Rusa A Arewacin Yankin October 10, 2025 Rahotanni : Isra’ila ta fara janye dawa wasu yankuna na Gaza October 10, 2025 Amurka ta kakaba wa wasu kamfanoni 50 takunkumi saboda sayen man Iran October 10, 2025 Isra’ila ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki October 10, 2025 Mohajirani: Iran na goyon bayan shawarar Falastinawa kan batun dakatar da bude wuta October 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ba Zata Halarci Zaman Taron Sharm El-Sheikh Ba Saboda Wasu Dalilai Da Ta Byyana
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana dalilin da ya sa Iran ba za ta halarci taron na Sharm el-Sheikh ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana dangane da rashin halartar jamhuriyar Musulunci ta Iran zuwa taron na Sharm el-Sheikh cewa, ba za su iya tunkarar wadanda suka kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Iran da kuma ci gaba da yi musu barazana da kuma sanya musu takunkumi ba.
Araqchi ya rubuta a shafinsa na yanar gizo a dandalin X da sanyin safiyar yau litinin cewa: “Iran ta nuna matukar jin dadin ta ga gayyatar da shugaba Sisi ya yi wa Iran na halartar taron na Sharm el-Sheikh. Duk da Muradin Iran din na tattaunawa ta diflomasiyya, Araqchi ya ce shi ko shugaba Pezeshkian ba za su iya tunkarar wadanda suka kai wa al’ummar Iran hari da kuma ci gaba da yi mata barazana da kuma sanya mata takunkumi.”
Ya kara da cewa: Duk da haka, Iran tana maraba da duk wani shiri da zai kawo karshen kisan kiyashin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a Gaza da kuma bukatar kai wa ga janye sojojin mamaya daga yankin.
Araqchi ya jaddada cewa: Falasdinawa suna da ‘yancin fahimtar ainihin hakkinsu na cin gashin kansu, kuma dukkan kasashe, fiye da kowane lokaci, suna da alhakin taimaka musu tare da goyon bayan wannan bukata ta doka da ta dace.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Gayyaci Mukaddashin Jakadan Kasar Oman Zuwa Ma’aikatar Harkokin Wajenta October 13, 2025 Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta October 13, 2025 Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje October 13, 2025 Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk October 13, 2025 Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza October 12, 2025 ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar October 12, 2025 Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice October 12, 2025 Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci