2025-08-05@19:26:00 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1835
«Yan Siyasa»:
Sashen cinikayyar samar da hidimomi na Sin ya ci gaba da bunkasa yadda ya kamata cikin watanni shida na farkon shekarar nan ta 2025, inda ya karu da kaso takwas bisa dari kan mizanin shekara. A cewar ma’aikatar cinikayya ta Sin, darajar hidimomin shige da fice a wannan wa’adi ta kai kudin Sin tiriliyan 3.89,...
Matar Shugaban Karamar Hukumar Giwa, Hajiya Hadiza Ahmad Sama’ila Yakawada, ta kaddamar da Makon Shayar da Nono na Duniya na bana, tare da kira ga iyaye mata da mazajensu da su ba wa jarirai nono kacokam na tsawon watanni shida na farko. A yayin kaddamarwar, Hajiya Hadiza ta bayyana cewa shayar da jarirai nono na...
Rundunar ’yan sandan Nijeriya reshen Abuja ta sanar da cafke wasu mata ’yan gida ɗaya da ake zargi da kitsa garkuwar ƙarya da zummar karɓar kuɗin fansa na naira miliyan biyar a wurin mahaifinsu. Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar. Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda...
Tosin Demehin ta nuna godiya da jin daɗinta, tana mai cewa wannan girmamawa daga jiharta na ƙarfafa mata gwuiwa da sauran ’yan mata masu burin taka leda a matakin duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Wata tawagar jami’an tsaron Isra’ila da suka yi ritaya su 600 ciki har da tsaffin shugabannin hukumomin leƙen asiri sun aika wa Shugaban Amurka, Donald Trump wasiƙa domin neman ya matsa wa Isra’ila da ta gaggauta kawo ƙarshen yaƙin da ake a Gaza. Jami’an sun ce “tunaninmu ne cewa Hamas ta daina zama wata barazana...
Gwamnatin Tarayya ta gabatar da karramawar kasa da kuma tukuicin kudade ga kungiyar kwallon Kwando ta mata ta Najeriya, D’Tigress, bayan nasarar da suka samu a gasar cin kofin kwallon kwando na mata ta FIBA karo na biyar a jere. A wata liyafar karrama su da aka yi a fadar shugaban kasa, mataimakin shugaban...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da karin kudin da gwamnatoci a matakin jiha suke samu daga asusun tarayya, ’yan Najeriya da dama suna korafin ba sa gani a kas. Manazarta dai sun ce ko kafin karin ma ya kamata ya yi a ce ayyukan da gwamnatcin jihohi suke yi sun fi...
Rundunar sojin kasar Sin (PLA) ta yi sintiri a yankin tekun kudancin Sin daga ranar 3 zuwa 4 ga wata. Kakakin rundunar PLA ta kudancin kasar Tian Junli ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin ta dauki matakin ne biyo bayan matakan Philippines na sanya kasashen dake wajen yankin cikin abun da ta kira...

Sojojin Somaliya Sun halaka Mayakan Kungiyar Al-Shabab Fiye Da Hamsin A Kudu Maso Yammacin Mogadishu
Sama da mayakan kungiyar ta’addanci ta Al-Shabaab 50 ne suka halaka a yankin kudu maso yammacin birnin Mogadishu fadar mulkin kasar somaliya Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka a Somaliya ta sanar a ranar Lahadin da ta gabata cewa; Sama da mayakan kungiyar ta’addanci ta Al-Shabaab 50 ne suka halaka a wani samame...
Sakamakon wannan mummunan ta’annuti, Mataimakin Gwamnan ya jagoranci wata ƙaƙƙarfar tawaga, wacce ta haɗa manyan ma’aikatan gwamnati da jami’an tsaro zuwa Banga da sauran wurare uku da waɗannan hare-hare ya shafa, don a jajanta masu, tare da ba su tallafi na abinci da kuɗaɗe. Mataimakin Gwamnan ya kuma tabbatar wa da waɗannan al’ummu cewa...
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun...
Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya tuhumi sabon Sarkin Gudi, Alhaji Ismaila Ahmed Gadaka da ya jagoranci zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban al’ummar masarautar sa, jiha da kasa baki daya. Gwamna Buni ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin gabatar da takardar nadin sarauta ga basaraken a hukumance a...
Shugaban kungiyar malaman addinin musulunci ko –Council Of Ulema-na Tafawa Balewa a jihar Bauchi na tarayyar Najeriya Sheikh Dan’azuki Musa tafawa balewa, yayi kira ga kasashen musulmi da kuma sauran kasashen duniya da su dauki darasi a jajircewar JMI da turjiyarta ga HKI, a kuma matsayin hanya tilo ta kawo karshen HKI. Kamfanin dillancin labaran...
Akalla mutane 11 ne aka kashe a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a unguwannin Kagara da San-Isa da ke karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara. Majiyoyi daga yankunan biyu sun shaida wa wakilinmu cewa an kai hare-haren ne a unguwannin Kagara da San-Isa tare da wasu kauyukan da ke kewaye. Waɗanne Ƙasashe Ne...
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta tarayya Kabiru Amadu (wanda aka fi sani da Mai Palace) ya shirya taron addu’a na musamman ga jihar Zamfara da Najeriya baki daya, domin neman zaman lafiya da cigaba mai dorewa. Taron addu’o’in wanda ya gudana a babban masallacin Juma’a na Tudun Wada da ke Gusau,...
ADC ta ce, duk da cewa an tsara filin jirgin ne don karbar fasinjoji miliyan 14 a cikin shekara guda, amma rahotannin da ake da su sun nuna cewa, filin jirgin ya karbi fasinjoji miliyan 6.5 ne kawai a shekarar 2024, kasa da rabin karfinsa. Don haka, ADC ta yi kira ga daukacin ‘yan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ga alama kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu a fafutukar da ake yi ta ganin iyaye mata sun shayar da jariransu nono zalla a wata shida na farko. Rahotanni sun ce duk da daɗewar da aka yi ana wayar da kai har yanzu matan da suke shayar da...
A cewar sanarwar, AIHS za ta taimaka wajen haɓaka tambarin dangote da haɓaka dabarun haɗin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki. Kodinetan shirin Barista Festus Adebayo ya shaida wa manema labarai cewa, za a iya cike giɓin gidaje a ƙasar ta hanyar haɗin gwiwar Haɗin kan Jama’a masu zaman kansu (PPP). Ya ce: “Kwarewa...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da babban shirin dashen bishiyoyi miliyan biyar a shekarar 2025. An fara dashen ne yankin Yanbawa da ke Ƙaramar Hukumar Makoda. Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Najeriya — El-Rufai Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi Gwamnan ya ce wannan shiri na nufin...
Auwalu Labarina, wanda ke cikin matasa jarumai da tauraruwarsu ke haskawa a Masana’antar Kannywood, ya fito a manyan fina-finai da dama da suka hada da darasi, Kwana Casa’in, Gidan Sarauta da kuma shirin nan na Labarina, ya kuma samu kyautuka da dama da suka danganci wannan sana’a tasa ta fim a lokuta daban-daban. Kazalika, ya...
Sojojin HKI sun kashe falasdinawa 62 daga safiyar jiya Asabar zuwa lokacin bada wannan labarin a yau Lahadi. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa mafi yawan wadanda aka kashen masu neman abainci ne, a cibiyoyin karban abincin wadanda HKI da Amurka suka kafa. Kafafen yada labarai daga asbitocin Gaza sun bayyana...
Minista Idris ya bayyana damuwa da irin martanin da al’umma da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai suka nuna dangane da lamarin. Amma ya jaddada cewa hukumar da ke da hurumin dakatar da lasisin gidajen rediyo da talabijin ita ce Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), kamar yadda doka...
Ya danganta mutuwar ta ƙanana da matsakaitan sana’oi a ƙasar, kan rashin samun rancen kudaɗen da za su ci gaba da ka kasuwancin su da rashin kayan aiki, da rashin kasuwa da ba a samu sosai da kuma rashin gudanar da ingantaccen shiri, kafin su fara gudanar da kasuwancinsu. Ya sanar da cewa, ya zama...
“Kazalika sarkin ya bayyana cewa, mun kuma duba yanayinmu. Me muke da shi? Me za mu iya yi? Me ya kamata mu yi domin inganta rayuwar mutanenmu? Allah ya albarkaci ƙasarmu, ƙasa ce mai faɗi sosai, kuma ta dace da ayyukan noma. Mun kuma yi la’akari da fannin ilimi. Jihar Neja, an san tana gaba...

Fim Na Kisan Kiyashin Nanjing Ya Mamaye Kasuwar Fina-Finan Sin Bisa Samun Kudin Shiga Yuan Biliyan Daya
Wani fim mai suna “Dead to Rights”, wanda aka shirya game da kisan kiyashin da aka yi a birnin Nanjing, ya mamaye kasuwar fina-finai ta lokacin zafi ta kasar Sin, inda kudin shigar da aka samu da shi ya zarce yuan biliyan daya, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 140 cikin kwanaki takwas kacal. Wanda aka yi...

Babban Jami’in MDD: Kokarin Sin A Fannin Samun Ci Gaba Mai Dorewa Na Da Matukar Alfanu Ga Yanayin Duniya
Fiye da shekaru goma da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dora samun ci gaba marar gurbata muhalli a matsayin wata muhimmiyar manufar raya kasa. Ya taba fitar da manufar raya kasa ta hanyar bayar da muhimmnci ga “Muhalli”, wadda ta yi nuni da cewa ingantaccen yanayin muhalli abu ne mai matukar daraja don samun...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna fatan haɓakar musayar kasuwanci tsakanin Iran da Pakistan ta haura dala biliyan 10 Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bar birnin Tehran a wannan ranar Asabar din zuwa Islamabad na Pakistan a wata ziyarar aiki a kasar bisa gayyatar da fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif ya yi masa....
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da barazanar kungiyoyin ta’addanci na ISIS da Al-Qaeda a nahiyar Afirka Wani sabon rahoto da kwararrun Majalisar Dinkin Duniya suka fitar ya yi gargadin karuwar barazanar da kungiyoyin ‘yan ta’adda ke da alaka da ISIS da Al-Qaeda suka yi kan kasashen nahiyar Afirka. Rahoton ya yi nuni da...
A cewar NANNM, sun dakatar da yajin aikin ne domin ci gaba da tattaunawa bisa alƙawarin da gwamnati ta ɗauka na aiwatar da buƙatun cikin ƙanƙanin lokaci. Takardar ta ce, “Kwamitin zartarwa na ƙasa ya yaba da matakan da gwamnatin tarayya ta fara ɗauka, musamman yadda ta bayyana lokacin da za ta aiwatar da buƙatunmu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiya ya yi juyayin shahadar Isma’ila Haniyya marigayi shugaban kungiyar Hamasa a nan Tehran shekara guda kenen. Ya kuma jaddada cewa JMI ba za ta taba manta da shi ba. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana bayyana wannan juyayin a ranar da Haniya yake cika shekara guda da shahada,...
An yi jana’izar Marigayi Sarkin Gudi da ke Jihar Yobe, Alhaji Isa Bunuwa Madugu Ibn Khaji, ranar Juma’a a Abuja, inda ya rasu a wani asibiti bayan fama da jinya. Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya ranar Juma’a ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar wajen hakartar taron. Sanarwar da Mamman Mohammad daraktan yada labarai na gwamna...
Bincike a kan zargin da ake wa Hukumar Raya ƙasashe ta Amurka (USAID) da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da na ƙasa da ƙasa game da tallafa wa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP da sauran masu tayar da ƙayar baya a Nijeriya har yanzu bai kammala ba. Kawo yanzu babu wata ƙwaƙƙwarar...
daga ƙarshe, kwamitin ya tabbatar da cewa zai miƙa dukkan shawarwarin da al’ummar yankin suka bayar gaban Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina Malam ɗikko Raɗda don daukar matakin da ya dace. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana naɗin Saidu Yahya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa (PCACC), bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, a watan Yuni. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta...
Gwamnan Jihar ta Gwambe, ya tunatar da cewa; a lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya tsaya a gabanmu a matsayin ɗan takara a yaƙin zaɓen 2023, ya yi wa Arewacin Nijeriya alƙawura na musamman. Kazalika, Arewa ta amince da manufofin shugaban ƙasar, ta kuma yi tsayin daka wajen zaɓensa, inda suka bayar da gudunmawa na...
Akalla ’yan gudun hijira miliyan daya da dubu 400 da ke Arewa maso gabashin Najeriya ne suke fuskantar barazanar yunwa bayan yanje tallafin da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ke bayarwa. Wani rahoton majalisar a kan abinci da tsaro wanda gwamnatin Najeriya, Shirin Kula da Abinci na Majalisar (FAO) da sauran masu ruwa da tsaki a...
Ya nuna rashin jin daɗinsa da rabon ayyukan tituna kamar yadda aka samu a cikin wata sanarwa da ma’aikatar ayyuka ta fitar a watan Mayun 2025, wanda a cewarsa, an ware Naira tiriliyan 1.394 wa yankin Kudu-maso-Yamma, yayin da ɗaukacin yankin Arewa-maso-gabas suka samu Naira biliyan 30, sai kuma yankin Arewa-maso-Yamma Naira 105 biliyan. “Rashin...
Tauraron dan wasan gaba na Super Eagles, Victor Osimhen, ya kammala komawarsa ƙungiyar Galatasaray ta ƙasar Turkiyya daga Napoli, a wata yarjejeniya ta dindindin da ta kai Yuro miliyan 75. Ƙungiyar Galatasaray ta sanar da kammala ɗaukar Osimhen a shafinta na yanar gizo a ranar Alhamis, inda ta bayyana cewa yarjejeniyar ta fara aiki daga...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Kwanturola Janar na Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa, Bashir Adewale Adeniyi na ta shan suka daga mutane daban-daban. Yayin da wasu ke ganin abin da shugaban ya yi da cewa ya dace, wasu kuwa na...
Yayin da yajin aikin gargadi na kasa baki daya da kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) ta kira ya shiga rana ta biyu, iyalai sun fara kwashe ‘yan uwansu daga asibitocin gwamnati zuwa masu zaman kansu a jihar Filato. A Asibitin Kwararru na Jihar Filato, dogon layin masu amsar katin asibiti don neman...

Zargin Da Wasu ’Yan Siyasar Amurka Ke Yi Wa Sin Na Fitar Da Hajoji Fiye Da Kima Ya Sabawa Hujjoji Na Hakika
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A nasa tsokaci game da batun, wakilin musamman na kasar Sin a yankin kahon Afirka Xue Bing, ya ce Sin ta dade tana goyon bayan matakan wanzar da zaman lafiya da ci gaba a yankin. Ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa ta fuskar shawo kan tarin kalubale dake addabar duniya. (Saminu...
Melaye wanda shi ne dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaben jihar Kogi a 2023, har yanzu bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba a nan gaba. Sai dai rahotanni na nuni da cewa, yana iya sauyawa zuwa jam’iyyar ADC – wata gamayyar jam’iyyar adawa da a baya-bayan nan ta jawo hankalin wasu jiga-jigan...
Ministan harkokin waje na kasar siriya ya isa birnin Mosco a yau Alhamis don bude sabon shafi da kasar Rasha bayan kifar da gwamnatin Bashar Al-asad a shekarar da ta gabata. Shafin yanar gizo na larabai Arabnews na kasar Saudiya ya bayyana cewa Asaad Hassan al-Shaibani tuna ya gana da ministan harkokin wajen kasar Rasha...
Tawagar kananan yan wasan damben gargajiya na kasar Iran sun zama zakara a wasannin da aka gudanar a na wannan shekara ta 2025 tare da Zinari guda, azurfa guda da kuma Tagullah 4. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an gasar wasan na damben gargajiya na kasar Iaran suna fadar haka a...
Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin wa’adin shekara guda ga shugaban hukumar Kwastan ta Nijeriya, Bashir Adewale Adeniyi. Kafin wannan ƙarin wa’adin, aikin Adeniyi zai kare ne a ranar 31 ga Agusta, 2025. Sai dai sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya...
Tsohon ɗan wasan tsakiyar Barcelona, Carles Perez, yana kwance a asibiti a ƙasar Girka bayan da wani kare ya cije shi a al’aurarsa yayin da yake yawo da nasa karen a Thermi, a wata unguwa a Thessaloniki, ranar Talata. Perez, mai shekaru 27, yana ƙoƙarin raba karensa da wani da suke fada lokacin da ya...
Binciken likitoci da ‘yansanda ya tabbatar cewa gubar ce ta yi sanadin mutuwarsa. Haka kuma, kotun ta yanke wa wani mutum mai suna Sani Sa’adu hukuncin ɗaurin shekara biyar saboda ɓoye gaskiya da ya yi dangane da wata Gift Bako, wadda ake zargi da hannu a kisan. Lauyoyin waɗanda aka yanke wa hukunci sun nemi...
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta saki tare da hada wadanda aka yi garkuwa da su talatin da biyar tare da iyalansu. Sun kunshi mata goma sha shida da yara goma sha tara daga Kagara, Tegina da Agwara, bayan sun shafe makonni a hannun ‘yan sanda da ke tsare da kuma kawar da hankalinsu...