’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno
Published: 11th, October 2025 GMT
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar wasu sojoji huɗu, bayan ’yan ta’adda sun kai hari yankin Ngamdu na Jihar Borno.
Jihar Borno ta daɗe tana fama da hare-haren ta’addanci, musamman daga ƙungiyar Boko Haram.
Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno An yi jana’izar sojojin da ’yan bindiga suka kashe a KebbiKo da yake wasu mazauna yankin sun ce sojoji 10 ne suka mutu, sai dai mai magana da yawun rundunar Operation Haɗin Kai, Laftanar Kanar Sani Uba, bai tabbatar da hakan ba cikin sanarwar ya fitar a ranar Juma’a.
Amma rahotanni sun bayyana cewa sojoji huɗu ne suka mutu, yayin da wasu biyar suka jikkata a yayin harin.
A cewar Kanar Sani, ’yan ta’addan sun yi amfani da roka, jirage marasa matuƙa, da bama-bamai wajen kai harin.
Sai dai sojojin sun mayar da martani, inda suka kashe da dama daga cikin ’yan ta’addan.
Ya ƙara da cewa wasu motocin yaƙi na sojojin sun lalace, amma duk da haka dakarun sun yi tsayin daka wajen yaƙar maharan.
Bayan harin, ’yan ta’addan sun yi ƙoƙarin hana bin hanyar Ngamdu zuwa Damaturu, wanda hakan ya tilasta rufe hanyar na ɗan lokaci.
Daga baya,sojoji sun cire bama-bamai guda uku, sannan suka sake buɗe hanyar ga matafiya.
Laftanar Kanar Uba, ya ce an ƙara wa dakarun kayan yaƙi da harsasai domin ci gaba da fafatawa.
Rahotanni sun nuna cewa gawarwakin ’yan ta’adda kusan 15 aka samu a kusa da ƙauyen Bula Wura.
Rundunar Sojin Najeriya ta yaba wa jarumtar dakarun, tare da tabbatar wa jama’a cewa zaman lafiya ya samu a yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda hari yan ta adda
এছাড়াও পড়ুন:
Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya maƙale a Guinea-Bissau bayan da sojoji suka yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar.
Jonathan da sauran baƙi baƙi masu sanya ido kan zaɓen da aka gudanar, ba za su iya barin ƙasar ba domin sojoji sun rufe iyakokin ƙasar baki ɗaya, tare da dakatar da zaɓen gaba ɗaya.
Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniyaLamarin ya samo asali ne bayan manyan ’yan takara biyu sun yi iƙirarin samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana.
Ba jimawa wasu dakarun sojin ƙasar suka hamɓarar da gwamnatin farar hula ta ƙasar.
Sun kuma sanar da dokar hana fita da kuma kama manyan jami’an da ke da alaƙa da zaɓen.
“An hamɓarar da gwamnatina,” in ji Shugaba Umaro Sissoco Embalo cikin wata tattaunawa ta waya da gidan talabijin na ƙasashen waje.
Jonathan ya je Guinea-Bissau ne a matsayin shugaban tawagar West African Elders Forum (WAEF) domin sanya ido kan zaɓen.
Ya ziyarci wasu rumfunan zaɓe a ƙasar kuma ya wallafa bayanai a kafafen sada zumunta kafin juyin mulkin.
Mutanen da ke tare da shi sun ce yana cikin ƙoshin lafiya, amma ba shi da damar barin ƙasar.
Sojojin suna kuma ƙoƙarin katse Intanet, lamarin da ya sa ake samun tangarɗa wajen sadarwa a ƙasar.
Hakan ya sa ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa suka fara nuna damuwa kan tsaron manyan ’yan siyasa da jami’an zaɓe.
A cikin wata sanarwa, Jonathan da wasu shugabannin Afirka sun yi Allah-wadai da juyin mulkin.
“Mun yi Allah-wadai da wannan yunƙuri na daƙile tsarin dimokuraɗiyya, kuma muna kira ga Tarayyar Afirka da ECOWAS su ɗauki matakin dawo da tsarin mulki,” in ji su.
Sun buƙaci mutanen Guinea-Bissau su kwantar da hankalinsu, tare da kira ga sojoji su saki dukkanin jami’an da suka kama domin a ci gaba da gudanar da zaɓe cikin lumana.