A yayin yanke hukuncin, kotu ta bayyana cewa: “Na farko (INEC) da na biyu (Farfesa Mahmood Yakubu) an yanke musu hukuncin tura su gidan gyaran hali saboda rashin bin hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Osogbo, Jihar Osun, ta bayar a shari’a mai lamba FHC/OS/CS/194/2024 a ranar 17 ga 5 Fabrairu, 2025.

Kotu ta kuma umarci Sufeton ‘yansanda na ƙasa da ya kama Yakubu tare da tabbatar da fara shari’ar hukuncin raina kotu cikin kwanaki bakwai daga ranar da aka yanke hukuncin.

Bugu da ƙari, kotu ta ci tarar INEC da Yakubu Naira 100,000 domin biyan masu shigar da ƙarar saboda raina umarnin kotu.

Masu shigar da ƙarar sun haɗa da Action Alliance, Farfesa Julius Adebowale, Injiniya Olowookere Alabi, Barrista Chinwuba Zulyke, Oladele Sunday, Simon Itokwe, da Araoye Oyewole, waɗanda suka wakilci kansu da shugabannin jihohi 30 na jam’iyyar.

A halin yanzu, Farfesa Yakubu ya sauka daga kujerarsa a hukumance a ranar Talata, inda Misis May Agbamuche-Mbu, kwamishinar INEC, ta karɓi ragamar shugabancin hukumar a matsayin shugabar riƙon ƙwarya.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin October 9, 2025 Siyasa Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu October 9, 2025 Manyan Labarai Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya October 9, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan sanda sun kama masu laifi da 34 a Kaduna

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta bayyana sabbin nasarorin da ta samu wajen yaƙi da laifuka a jihar, ta hanyar holen mutum 34 da ta kama da aikata laifuka daban-daban.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Rabi’u Muhammad, ya ce wannan ci gaba ya samu ne saboda sabbin dabarun aiki da kuma bayanan sirri da aka samu daga al’umma da hukumomin tsaro.

Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000

A Anguwar Barnawa da wasu wurare a Kaduna, rundunar Operation Fushin Kada ta kama mutane 13 da ake zargi da aikata fashi da makami da satar wayoyi a otel-otel da gidaje.

An ruwaito sun taɓa kashe ɗan sanda a shekarar 2024, kuma suna samun bayanai daga dilolin miyagun ƙwayoyi a wuraren shaƙatawa. A

An ƙwato bindiga ƙirar gida, gatari da adduna 13, mota, kwamfuta huɗu, wayoyi 13 da talabijin huɗu.

Haka kuma, a Nunbu Bashayi da ke Sanga, an kama mutane bakwai da ake zargi da garkuwa da mutane tare da neman kuɗin fansa.

Dukkanimsu sun amsa laifinsu kuma ana neman ragowar waɗanda suke tsere.

A wani samame daban, ’yan sanda sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da aikata fashi, fyaɗe da damfara.

Sun saba kai hari gidajen mutane, ɗaukar kuɗaɗen mutane, aikata fyaɗe sannan su riƙa ɗaukar bidiyo tsoratar da mutane.

A Zariya kuwa, an kama wasu mutane tara da suka haɗa da maza da mata waɗanda ake zargi da yi wa direban Adaidaita sahu fashi ta hanyar zuba masa magani a abin sha.

Rundunar ta kuma kama wani likitan bogi mai suna Adamu Abubakar Muhammed wanda ya yi wa mutane tiyata ba tare da shaidar karatun likitanci ba.

Ya yi amfani da takardun bogi wajen yin aiki na tsawon wata guda kafin a gano shi.

Kwamishinan, ya ce duk waɗanda aka kama suna hannun rundunar, kuma za a gurfanar da su kotu bayan kammala bincike.

Ya gode wa jami’an tsaro da al’umma kan haɗin kai, inda ya yi da a ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin inganta tsaro a jihar da ƙasa baki ɗaya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki
  • Jihar Jigawa Za Ta Rufe Karbar Kudaden Aikin Hajjin 2026 Ranar 24 Ga Watan Disamba
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi da 34 a Kaduna
  • Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS
  • Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • Faduwar Darajar Kuɗi Na Kara Tsananta Kalubale Ga Kotunan Shari’a — CJN
  • ’Yan Majalisar Kudu sun roƙi Tinubu ya yi wa Nnamdi Kanu Afuwa