2025-06-29@18:14:18 GMT
إجمالي نتائج البحث: 494

«Miliyan Dari Da Shadaya»:

    Jirgin da ke ɗauke da mutane sama da 200 daga Bali a ƙasar Indonesia zuwa Ostireliya, ya yi juyawar dole bayan wani fasinja ya yi yunƙurin buɗe ƙofarsa yayin da jirgin kamfanin Jetstar ke shawagi a tekun Indiya. “Mun samu wani jirgin sama ya koma Denpasar (filin jirgin sama na Bali) a daren Talata bayan...
    Jami’an tsaro sun jiran kayan ado na ’yan kunnayen zinare su wuce ta na’urar binciken fasinjan jirgin sama kafin a gano kayan da aka sace a hukumance. An kama wani mutum mai shekara 32, mai suna Jaythan Lawrence Glider bisa zargin satar ’yan kunne biyu na zinare na sama da Dala Amurka 769,000 kwatankwacin Naira...
    Hotunan faifan bidiyo da ke fallasa kisan da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi wa likitoci 15 a Rafah, ya tilastawa “Isra’ila” ja da baya kan labarin da ta kirkiro, tana mai cewa karyar da ta yi “ba da gangan ba ce”. An kara da’awar kuma daga baya an karyata ta ta hanyar shaidun bidiyo,...
    Yana kuma havaka sabon nau’in alakar kasa da kasa, ta hanyar kaddamar da shirin Raya Duniya, da shirin Tsaron Duniya, da shirin Wayewar Kai na Duniya dake aiki a matsayin ginshikan wannan tunanni. Haka ma hadin gwiwa mai inganci karkashin tsarin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya mai amfani wajen aiwatar da wannan hangen nesa,...
    Yayin ziyararsa kasar Sin kwanan nan, babban mashawarcin gwammatin wucin-gadi ta kasar Bangladesh, Muhammad Yunus, ya tattauna da wakiliyar CMG, wato babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, inda a cewarsa, a matsayin kasa ta farko a kudancin nahiyar Asiya, wadda ta rattaba hannu tare da kasar Sin kan takardar bayanin hadin-gwiwa game...
    Direba da kwandastan motar bas sun tsere domin tsira da rayukansu, inda suka bar fasinjoji a ciki yayin da wata motar bas ta BRT ta kama wuta a Maryland da ke Jihar Legas da safiyar ranar Asabar. Majiyar Channels TV da ke wajen da lamarin ya faru, ta ce motar ta taso ne daga yankin...
    daukar Ciki: Wannan na nuna yadda wanda za a lura da ‘ya’yan da aka haifa. 3- A Ina Ya Fi Dacewa A Sayi Sa? Za a iya sayen Bijimin Sa, a wurare daban-daban da ake bukata, amma ana so kafin a saya, a yi taka-tsan-tsan. Ana kuma so a tunbubi kwararru a fannin ko kuma...
    Tsohon Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Kano kuma tsohon Mashawarci na Musamman ga Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, CP Muhammad Wakili (ritaya), ya jaddada cewa dole ne ’yan sanda su yi amfani da ikon da suke da shi cikin gaskiya da adalci, don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa. Da yake jawabi a wani...
    Shugaban kasar Burundi ya yi gargadin cewa Rwanda na da shirin kai wa kasarsa hari, bayan da sojojin Burundi suka taimakawa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC) a yakin da take yi da ‘yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda. Shugaban kasar ta Burundi Evariste Ndayishimiye ya bayyana cewa, ya samu “sahihan bayanan sirri” da...
    Masu ababen hawa da dama sun maƙale a gadar Namne da ta rufta daura da hanyar Jalingo zuwa Wukari a Ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a da aka yi ranar Laraba. Ruwan sama ya kawar da gadar da aka gina ta wucin gadi a hanyar da aka...
    Yanzu da ya rasu, Hauwa ta ce ba ta da tabbas kan yadda za ta yi rayuwa da ‘ya’yanta. Lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar 27 ga watan Maris, lokacin da wasu matafiya 16 ‘yan asalin Arewacin Nijeriya suka faɗa tarkon wasu ‘yan sa-kai a Uromi, a Jihar Edo, inda suka...
    Birgediya-Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya kuɓuta bayan shafe kwana 56 a hannun ’yan bindiga. An sace Janar Tsiga, wanda Tsohon Shugaban Hukumar NYSC ne, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2025. Mutum ɗaya ya rasu, 3 sun jikkata a rikicin ’yan sara-suka a Filato...
    Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, da aka dakatar, ta bayyana cewa “ita ba mahaukaciya ba ce”, kuma “ba ta tsoron kowa” a yayin da take jawabi ga dimbin magoya bayanta a lokacin da ta dawo gida a Ihima, karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi a ranar Talata da yamma. Dawowarta ta...
    Babban Darakta Muryar Najeriya VON, Malam Jibrin Baba Ndace ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kara kaimi wajen addu’o’in samun nasara ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bisa tsarinta na sabunta fata.   Ya yi wannan kiran ne a cikin sakonsa na Sallah ga al’ummar Musulmi da aka rabawa manema labarai a...
    Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan.   Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na...
    Asbitin ‘Mount Sinai’ (Dotsen Sinaa’ a kasar Amurka ta salami wata likita daga aiki, bayan da aika da wani rubutu da hoto a shafukan yanar gizo tana, wanda Asbitin tana cewa ai Musanta hare-haren ranar 7th ga watan Octoba ne’. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta bayyana cewa Dr Leila Abbasi,diyar shekara 46...
    Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan lafiya, tare da kira garesu da su rungumi koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W) a cikin rayuwarsu ta yau da kullum. Ya bayyana hakan ne a sakon sa na Sallah ga al’ummar jihar. Malam Umar Namadi ya yi addu’a...
    Masarautar Kauru da ke jihar Kaduna ta jaddada kudirinta na tabbatar da tsaro, inda ta bukaci mazauna yankin da su kasance masu taka-tsan-tsan duk da ci gaban da gwamnati ta samu a baya-bayan nan wajen magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane da kuma munanan hare-hare. Mai martaba Sarkin Kauru, Alhaji Zakari Ya’u Usman...
    Miliyoyin Musulmi ne a faɗin duniya ke bikin Ƙaramar Sallah bayan kammala azumin Ramadana. Ku ci gaba da kasancewa da shafin Aminiya domin samun hotunan yadda aka gudanar da Sallar Idi a wasu sassan duniya da kuma nan gida Nijeriya. Musulmi a Filin Idi na Kubwa da ke birnin Abuja Wasu da suka fito sallar...
    A birnin Roma masu goyon bayan al-ummar Falasdinu sun gudanar da zanga-zanga ta goyon bayan Falasdinawa, sun kuma ya allawadai da kungiyar tarayyar Turai da kuma Amurka kan yadda suka kasance manay-manyan masu taimakawa HKI a kissan kiyashin da take aikatawa a Gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa daubban wadanda...
    Ofishin jakadancin Amurka da ke Damascus ya fitar da wata sanarwar gaggawa, inda ya yi kira ga daukacin Amurkawa da su gaggauta ficewa daga kasar Syria, sakamakon karuwar hare-haren da ake kai wa a lokacin bukukuwan sallar Idi, wanda ke kawo karshen azumin watan Ramadan mai alfarma. A cikin wata sanarwa da ta fitar ma’aikatar...
    Hukumar ’Yan Sandan Saudiyya, ta yi magana kan bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna wata mata tana mari wani ɗan sanda bayan ya hana ta wuce wata hanya da aka rufe. A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, ta ce tana bincike domin tattara dukkanin bayanai kafin...
    Aƙalla mutum 19 aka kama bayan wata arangama tsakanin mabiya ɗarikar shi’a da jami’an tsaro a Abuja. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a yankin Banex, da ke Wuse 2, inda mutane da dama sun jikkata, sannan mutum ɗaya ya rasu. An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara Yadda kisan ’yan Arewa...
    Manyan Matakai Biyar Da Manoma Da Masu Zuba Hannun Jari A Fannin Aikin Noma Ya Kamata Su Yi La’akari Da Su Kamar Yadda kwararrun Suka Bayar Da Shawara: 1- Irin Kwakwar Manja Na Malesiya Bukatar da ake da ita ta Irin Kwakwar Manjan Nijeriya a duk shekara, ya kai na tan miliyan 3, inda kuma...
    A ranar Juma’a kasuwar ta rufe a cikin makon makon inda masu zuba hannun jarin, suka yi asarar Naira biliyan 166.43. Duk a cikin makon, saye da sayawar da aka yi ta shiyar ta kai ta jimlar Naira biliyan 3.281 da kuma wata shiyar ta Naira biliyan 63.517, duk a cikin hada-hada guda  60,782 da...
    Har ila yau, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya aike wa hukumomin tsaro wasiƙa yana sanar da shirinsa na gudanar da bikin. Gwamnatin jihar da masarautar Kano har yanzu ba su ce komai ba kan wannan haramci ba. Wannan mataki na zuwa ne bayan da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya sanar da...
    Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Ghana, John Mahama, sun  tattauna batutuwa da dama domin  karfafa alakar da ke tsakanin kasashen yammacin Afirka. An gudanar da ganawar ne  a Abuja  bayan da Mahama ya kai wa Tinubu ziyarar ban girma domin yabawa da  halartar shugaban Najeriya a yayin bikin rantsar da shi a Accra, babban...
    Mai Bai Wa Gwamnan Sakkwato Shawara kan Harkokin Karkara, Malami Muhammad Galadanchi (Bajare), ya bai wa magoya bayan jam’iyyar APC a jihar, kyautar Naira miliyan 22 domin gudanar da shagalin Sallah Karamar. Yayin bayar da kyautar a ranar Alhamis, Bajare ya ce ya yi hakan ne domin nuna godiyarsa ga jagoran APC a jihar, Sanata...
    Sojojin Iran sun fitar da bayani a daidai lokacin da ake shirin  raya ranar Kudus ta duniya, suna masu bayyana cewa; Hanyar da za ta warware matsalar Falasdinu ita ce yin gwgawarmaya da kuma samun goyon baya daga al’ummun duniya. Bayanin ya kuma kara da cewa; A daidai lokacin da al’ummar Falasdinu suke fuskantar zalunci,ta’addanci,...
    Kasashen Iran, Lebanon, Iraki, da kuma Yemen sun kaddamar da wani atisayen hadin gwiwa na sojojin ruwa domin nuna goyan baya ga  Falasdinawa a zirin Gaza, wadanda ke ci gaba da fuskantar zalinci  na gwamnatin Isra’ila. An fara faretin hadin gwiwa a tekun Fasha, da yankin gabar tekun Makran, da kuma tekun Caspian da ke...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300...
    Kwamitin tallafawa marayu da masu karamin karfi na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah dake karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa ya tallafawa gidajen marayu da masu karamin karfi da kayan abinci na kusan naira miliyan 9. Shugaban kungiyar Sheikh Hassan Sabo Musa ya bayyana hakan yayin rabon kayan da aka gudanar a...
    Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru, ya ziyarci Cibiyar Horar da Sojoji da ke Zariya, inda ya yi alƙawarin samar da ƙarin kayan aiki da ci gaba da inganta horon kuratan sojoji domin su dace da buƙatun zamani. A lokacin ziyarar, Ministan ya bayyana gamsuwarsa da horon da kurata na kashi 88 ke samu, inda ya...
    Manjo-Janar Muhammad Inuwa Idris mai ritaya, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman na Jihar Kano, ya yi murabus. Wannan dai na zuwa ne bayan shafe watanni bakwai kacal da karɓar muƙamin. Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Kano, Mustapha Muhammad ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Larabar....
    Dakarun (RSF) sun sanya sabbin takunkumai kan isar da kayan agaji a yankunan da ke karkashin ikonsu, lamarin da ya kara ta’azzara matsalar ayyukan jin kai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito. Matsalolin dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar RSF ke kokarin kafa gwamnatin daga bangarenta a yammacin kasar...
    Sai dai, tabbas za a karya tsarin, ganin yadda ba a samun adalci a ciki. Mun san kasar Sin daya ce daga cikin kasashen da suka warware dabaibayin hana ci gaba da kasashen yamma suka daura musu, inda ta raya tattalin arzikinta, tare da taka muhimmiyar rawa a cikin tsarin duniya ta fuskar samar da...
    Wannan ya taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin basasa a Laberiya da Saliyo. Duk da haka, ƙungiyar ta fuskanci ƙalubale, musamman bayan juyin mulki a ƙasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar a cikin shekarun baya-bayan nan. Shin ECOWAS na iya ci gaba da aiwatar da ayyukanta kamar da? Sai dai har yanzu wasu na yi wa...
    Sai dai duk da yaba wa Amurka bisa irin taimakon da ta bayar a baya, Byanyima ta nuna damuwa kan yadda aka dakatar da tallafin kwatsam ba tare da shiri ba. Wannan na iya haddasa koma baya a ƙoƙarin da aka shafe shekaru ana yi na rage yawan masu kamuwa da cutar, musamman a yankunan...
    Dakarun sojin Yaman sun ce sun kara kai hare-hare na nuna kyama ga Isra’ila da Amurka a matsayin nuna goyan baya a kan zirin Gaza. Kakakin rundunar Yahya Saree ya ce a daren jiya litinin sojojin na Yaman sun kai hari filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion na Isra’ila da makami mai...
    Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ya yi gargadin cewa hana shigar da kayayyakin jin kai da Isra’ila ta yi a zirin Gaza ya jefa yankin cikin mawuyacin hali na rashin abinci. “Makonni uku kenan da hukumomin Isra’ila suka hana shigar da kayayyaki cikin Gaza. “Ba abinci, ba...
    Ebrahim Rasool, jakadan Afirka ta Kudu da gwamnatin Trump ta kora, ya samu tarba a wannan Lahadin daga daruruwan magoya bayansa da suke rera wakoki  domin karrama shi a filin jirgin sama na Cape Town. Jama’a sun kewaye Rasool da matarsa ​​Rosieda bayan isowarsu, yayin da ‘yan sanda suka yi musu rakiya har zuwa tashar...
    Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi...
    Wata mata mai suna Krystena Murray ’yar Amurka, wadda ta ɗauki ciki tare da haife jariri namiji ba tare da sanin cewa ba ɗanta ba ne, ta fara ɗaukar matakin shari’a a kan wani asibitin da ke taimaka wa mata samun ciki ta hanyar dashen ɗantayi (IBF). Matar tana zargin asibitin da yi mata dashen...
    Jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar gama-gari idan Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ki bin hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na dakatar da matakin da gwamnatinsa  na korar shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet.  Yair Lapid ya shaidawa dubban masu zanga-zanga a Tel...
    Kungiyar Taliban ta ce Amurka ta cire tallafin dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan Sirajuddin Haqqani, mataimakin shugaban kungiyar kuma ministan harkokin cikin gida. A cewar Abdul Mateen Qani, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gidan Taliban, an janye tukuicin da aka bayar a baya a karkashin shirin bayar...
    Kallo ya koma sama bayan da mata suka karbe ragamar kasuwancin kayan lambu a a tsakiyar birnin Gombe, inda a baya kasuwancin kayan ya kasance a hannun maza kadai na tsawon lokaci. Wannan sabon sauyi ya da ya taso a hankali ya faru ne a sakamakon matsalolin kudi da nauyin kula da kai da kuma...
    Zaunannen wakilin Sin dake ofishin MDD a Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa a kasa Switzerland Chen Xu ya yi jawabi a gun taron hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 58 kan batun kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, inda ya yi bayani game da tunanin Sin kan kare...
    Wata karya ta hadiyi safa 24 da sauran kayan sawa, inda suka makale masa a mukamuki – lamarin da ya haifar da yi masa tiyatar ceton rai a Jihar California a Amurka, kamar yadda cibiyar kula da dabbobi ta bayyana. Wata karya mai suna Luna, jinsin Bernese Mountain da ta shafe wata 7 tana fama...
    Fadar Shugaban Kasar Nijeriya, ta yi watsi da rahoton baya-bayan nan da kwamitin hulda da kasashen wajen Amurka ya fitar, wanda ya kafa hujja da amincewar majalisar dokokin kasar, na zargin kakaba wa wasu kiristoci takunkumi a kasar. Mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa, Daniel Bwala, ya bayyana rahoton a matsayin...