Sauye-sauyen Tinubu ba su rage talauci a Najeriya ba — Bankin Duniya
Published: 9th, October 2025 GMT
Bankin Duniya ya ce har yanzu talauci na ci gaba da yaɗuwa a Najeriya duk da sauye-sauyen tattalin arziƙi da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar domin daidaita tattalin arziƙin ƙasar.
A wajen ƙaddamar da rahoton ci gaban da aka samu a Abuja, Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ya bayyana cewa aƙalla mutum miliyan 139 ne ke rayuwa cikin ƙangin talauci a shekarar 2025.
Ya ce duk da cewa tattalin arziƙin Najeriya ya ɗan bunƙasa, kuma gwamnati tana samun ƙarin kuɗaɗen shiga, yawancin jama’a har yanzu na fama da tsadar rayuwa da wahalhalu.
“Duk da waɗannan nasarorin, yawancin ‘yan Najeriya har yanzu suna cikin wahala. Ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu shi ne yadda za a sauya waɗannan nasarorin zuwa inganta rayuwar kowa,” in ji Verghis.
A gefe guda, bankin ya yaba wa Najeriya bisa ƙoƙarin da ta yi wajen daidaita farashin musayar kuɗaɗen waje da rage giɓin kasafin kuɗi.
Sai dai ya ce waɗannan nasarori ba su kawo sauƙi ga rayuwar jama’a ba.
Ya shawarci gwamnati ta rage hauhawar farashin kayan abinci, ta yi amfani da kuɗaɗen jama’a yadda ya kamata, kuma ta faɗaɗa shirin tallafa wa marasa ƙarfi.
Rahoton, ya yi hasashen cewa tattalin arziƙin Najeriya zai iya bunƙasa zuwa 4.4 cikin ɗari nan da shekarar 2027, ta hanyar bunƙasar noma, da masana’antun da ba su da alaƙa da harkar man fetur.
Amma ya yi gargaɗin cewa hauhawar farashin kaya da abinci na iya kawo wa waɗannan nasarori naƙaso.
Ci gaban ba ya shafar talakawa — MasanaMasanin tattalin arziƙi Farfesa Uche Uwaleke, ya bayyana rahoton a matsayin gargaɗi, inda ya ce ci gaban da ake gani bai inganta rayuwar jama’a ba.
Ya buƙaci gwamnati ta zuba jari a noma da masana’antu domin samar da ayyukan yi da rage talauci.
Wani masanin tattalin arziƙi daga Jami’ar Al-Hikmah, Dokta Omotayo Lawal, ya ce ci gaban tattalin arziƙin Najeriya “ba daidaita ba,” domin fa’idar sauye-sauyen ba ta kai ga talakawa ba.
Ya ɗora alhakin hakan kan hauhawar farashi da kuma rashin daidaita manufofi a tsakanin gwamnatoci daban-daban.
“Idan farashi yana hauhaws kuma samun mutane yana raguwa, to babu wata manufa da za a ce tana aiki yadda ya kamata,” in ji Lawal.
Ya jaddada cewa kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali wajen daidaita farashin kayayyaki da inganta samar da abinci.
Ƙungiyar Afenifere ta soki kalaman gwamnatin tarayyaƘungiyar Afenifere ta yankin Yarbawa ta soki iƙirarin gwamnatin Tinubu na cewa tattalin arziki ya samu tagomashi, inda ta kira hakan da “ƙarya a kafafen watsa labarai ”
Ƙungiyar ta ce cire tallafin mai da rage darajar Naira sun durƙusar da kasuwanci da jefa miliyoyin mutane cikin ƙangin talauci.
“Yayin da mutane ’yan kaɗan ke amfana, samun mutane ya ragu saboda hauhawar farashi da saukar darajar Naira,” in ji Afenifere a wata sanarwa.
Jama’a na ci gaba da shan wahalaJama’a da dama sun tofa albarkacin bakinsu, inda suka ce har yanzu sauƙin rayuwa bai samu ba duk da an ce tattalin arziƙi yana farfaɗowa.
Wani mazaunin Jihar Kano, Hamza Bunkure, ya ce: “Mutane har yanzu suna sha wahala wajen siyan abinci. Wutar lantarki ba ta daidaita, kuma man fetur ya yi tsada.”
Wani mai suna Ibrahim Rufai, ya ce farashin kayan abinci ya fara sauka saboda gwamnati ta sassauta dokar hana shigo da abinci daga waje, amma ya nuna damuwa cewa hakan zai iya cutar da manoma.
Ya buƙaci gwamnati ta sayi amfanin gona daga hannun manoma don ƙarfafa musu gwiwa.
Shi kuwa Babatunde Rahman ya buƙaci ake kwatanta gaskiya da amana a tsakanin gwamnati da jama’a domin samun ci gaba mai ɗorewa.
“Har sai an samu adalci, gaskiya, da hangen nesa a tsakanin shugabanni da jama’a, sannan za a samu daidaiton tattalin arziƙi,” in ji Rahman.
Masana sun jaddada cewa duk da cewa Najeriya ta samu ci gaba a fannin daidaita tattalin arziƙi, akwai sauran aiki domin tabbatar da cewa fa’idar ci gaban ta shafi kowa ba wasu tsirarun mutane kawai ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Bankin Duniya Hauhawar Farashi Kayan abinci Talakawa Tattalin Arziƙi tattalin arziƙin tattalin arziƙi Bankin Duniya gwamnati ta
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya
Na farko, hada kai don samar da yanayi mai kyau ga ci gaban mata. Na biyu, a karfafa abubuwan da za su habaka ingancin ayyukan mata cikin hadin kai. Kana na uku, a gina tsarin kare hakkin mata tare. Sai na hudu, a bude sabon babin hadin gwiwa tsakanin mata a duniya.
Za a gudanar da taron kolin mata na duniya a yau da gobe Talata a birnin Beijing. Kuma tuni shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, suka yi musafaha da shugabannin tawagogin kasashe, da kungiyoyin duniya da suka halarci taron, tare da daukar hotuna tare da su. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA