Jagora: Dole Ne Ga Hukumomin Da’awa Da Malamai Su Kula Da Batun Tsayar Da Sallah A Tsakanin Al’umma
Published: 9th, October 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Kira ga tsayar da sallah wani aiki ne na wajibi ga hukumomin da’awar addini da malamai
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa: Kira ga tsayar da sallah da koyar da ita, da bayyana ma’anonin da ke cikinta, da riko da ita, wani aiki ne na wajibi da ya rataya a wuyan hukumomin da’awar addini da malamai da ma’abuta addini.
A cikin sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike ga zaman taron cibiyar karfafa tsayar da sallah karo na 32 ya bayyana cewa: Taron karfafa tsayar da sallah yana daya daga cikin mafi fa’ida a tsakanin al’ummar kasa, kuma ranar da ake gudanar da ita tana daya daga cikin ranaku masu albarka a wannan shekara. Wannan ya samo asali ne daga kebantuwa da fifikon wannan wajibi na Musulunci mai ma’ana da muhimmanci.
Jagoran ya kara da cewa: Idan ana yin sallah da ladubban da suka dace, kamar tawali’u da mika wuya ga Allah, takan kwantar da zuciya, da karfafa niyya, da zurfafa imani, da rayar da fata. Kyakkyawar makomar mutum a duniya da lahira ta dogara da irin wannan zuciya, irin wannan wasiyya, da imani, da irin wannan fata. Don haka shawarar yin tsayar da sallah a cikin Alkur’ani da sauran nassosin addini ta fi kowace nasiha muhimmanci, don haka ake ganin cewa ita ce mafificiyar dukkan ayyuka a fagen addini.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Babban Kwamandan IRGC Ya Jaddada Batun Wurga Makiya Cikin Mummunar Nadama October 9, 2025 Hamas: An Cimma Yarjejeniyar Karshen Kan Dakatar Da Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Gaza October 9, 2025 Kungiyar Jihadul-Islami Ta JInjinawa Al’ummar Falasdinu Kan Juriyarsu A Lokacin Yaki October 9, 2025 Shugaban Kasar Ecuador Ya Tsallake Rijiya Da Baya Daga Kisan Gilla October 9, 2025 Venuzuwela Ta Kaddamar Da Atisayan Soji Don Mayar Da Martani Ga Barazanar Amuka October 9, 2025 Ronaldo Ya Zama Biloniya Na Farko Tsakanin Yan Kwallon Kafa A Duniya. October 9, 2025 Trump Ya ce An Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Yakin Gaza October 9, 2025 M D D Ta yi Kira Da A Kawo Karshen Yakin Gaza Da Aka Kwashe Shekaru 2 Ana Yi. October 9, 2025 Iran da Rasha Sun Tattauna Kan Yadda Za su Inganta Yin Aiki Tare A Bangaren Nukiliya. October 9, 2025 Natanyahu Ya Ce Makamai Masu Linzami Masu Keta Nahiyoyi Na Iran Barazana Ce Ga Amurka October 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: tsayar da sallah
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila Tana Ci Gaba Da Rushe Gidaje A Yankin Gaza
Da safiyar Yau Laraba ne sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila su ka kai hare-hare a yankuna daban-daban na zirin Gaza, tare da rushe gidaje da dama. Sojojin mamayar sun yi amfani da jiragen sama marasa matuki da kuma tankokin yaki domin rushe gidajen. A arewacin Gaza da gabashin Jabaliya sojojin na mamaya sun yi amfani da manyan bindigogi akan gidajen fararen hular. A unguwar “Tuffah” ma an ga yadda sojojin mamayar su ka aike da jiragen yaki marasa matuki.A can kudancin Gaza kuwa jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ne su ka kai hare-hare akan barin Bani-Suhaila a gabashin Khan-Yunus,a lokaci daya kuma manyan bingigoginsu su ka bude wuta akan iyaka.
Tun bayan da aka tsagaita wutar yaki a cikin watan Oktoba ne, Sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ilan suke ci gaba da kai hare-hare akan Gaza ba tare da kakkautawa ba. Daga tsagaita wutar zuwa yanzu adadin Falasdinawan da su ka yi shahada a sanadiyyar hare-haren na ‘yan sahayoniya sun haura 300.
Hukumar agaji a yankin na Gaza ta yi gargadi akan cincirindon ‘yan hijira da suke rayuwa a cikin hemomin da babu kayan da rayuwa take da bukatuwa da su domin ci gaba. Ruwan sama yana ci gaba da sauka a yankuna mabanbanta na Gaza da sanyi yake karuwa ba tare da samar da na’urorin dumama hemomin ba.
Kakakin kungiyar agaji a Gaza Mahmud Basal ya ce; Suna samun dubban koke daga Gaza cewa hemomin da mutane suke rayuwa a ciki ba su dace da rayuwa ba ko kadan.Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe November 26, 2025 Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta November 26, 2025 Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki November 26, 2025 Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin November 26, 2025 Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah November 26, 2025 UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin Lebanon November 26, 2025 Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Ga Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci