Zamfara Ta Yi Gargadi Akan Yiwa Shirinta Na Bunkasa Ilimi Zagon Kasa
Published: 10th, October 2025 GMT
Gwamnatin jihar Zamfara ta yi gargadin cewa ba za ta lamunci duk wani aiki na sakaci ko zagon kasa da zai iya kawo cikas ga kokarin da take yi na gyara da inganta harkar ilimi.
Shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Zamfara (ZSUBEB), Farfesa Nasir Garba Anka ne ya yi wannan gargadin a wata ziyarar bazata a makarantar firamare ta UBE, Low Cost da ke Gusau, biyo bayan rahotannin sace-sace da kuma lalata kadarorin gwamnati.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ibrahim Maizare ya bayyana haka a wata sanarwa da ya ba rediyon Najeriya a Gusau.
Farfesa Nssiru Anka ya nuna matukar damuwa kan rashin kyawun kayan aiki, ya kuma bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
A wata ziyarar bazata da ya kai makarantar, Farfesa Nasir Garba Anka ya gano cewa an kwashe wasu kayayyaki da suka hada da kujeru, tebura, da tagogi, ko kuma an lalata su.
Ya kuma bayyana faruwar lamarin a matsayin babban sakaci, ya kuma sha alwashin ganin an gurfanar da duk wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya.
Nan take Farfesa Nasir Anka ya ba da umarnin a kama shugaban makarantar da jami’an tsaron makarantar domin yi masa tambayoyi don sanin yadda irin wannan barna ta faru a karkashin kulawarsu.
Farfesa Anka ya nanata kudirin hukumar na kare dukiyoyin jama’a da kuma samar da yanayi mai kyau na koyo a dukkan makarantun gaba da sakandare a fadin jihar Zamfara.
REL/AMINU DALHATU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Zamfara Ilimi
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya : Ana ci gaba da alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana jimaminsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, lamarin da ya ce ya kaɗu matuƙa da ya samu labarin.
Tinubu ya ce jagoran na ɗarikar Tijjaniya mutum ne mai daraja da ƙima, sannan ya bayyana shi a matsayin madubi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa.
Rasuwarsa za ta ba babban giɓi a Najeriya,” in ji shugaban.
Shi ma Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana rasuwar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi a matsayin rashi babba ga al’ummar Musulmi na Najeriya da ma Afirka baki ɗaya.
A wata sanarwa da Atiku ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ya bayyana marigayin da babban malami wanda ya koyar da addini da tarbiya.
Tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana jimaminsa tare a miƙa ta’aziyya ga iyalai da ƴanuwan da makusantan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi bisa rasuwar malamin.
Kwankwaso ya bayyana malamin a matsayin uba, kuma babban malami wanda koyarsa ta zama madubi ga ɗimbin al’umma.
Gwamnonin arewacin Najeriya sun nuna alhinin su bisa rasuwar jagoran ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya Shiekh Dahiru Usman Bauchi wanda ya rasu a yau alhamis.
Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya bayyana marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin mutumin da ya damu da harkokin addinin musulunci, mai son zaman lafiya, da samar da fahimta da juriya tsakanin musulmai da mabiya sauran addinai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ta yi tir da Australiya kan alakanta IRGC, da mai tallafawa ta’addanci November 27, 2025 Ramaphosa ya soki kalaman Trump na cewa ba zai gayyaci shi a taron G20 November 27, 2025 ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau November 27, 2025 Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan November 27, 2025 Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci November 27, 2025 Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya November 27, 2025 Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon Dake Takawa Makiya Birki November 27, 2025 Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa November 27, 2025 An Zabi Iran A Cikin Majalisar Zartarwa Ta Hukumar Yaki Da Makamai Masu Guba Ta Duniya CWC November 27, 2025 HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin November 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci