ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar October 9, 2025 Daga Birnin Sin An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin October 9, 2025 Daga Birnin Sin Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.

26 October 9, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai

Babbar Kotun Jihar Oyo da ke Ibadan, babban birnin jihar, a ranar Litinin ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutum biyar da ta samu da laifin kashe wani direban tasi.

Kotun dai ta sami mutanen ne da laifin kashe direban mai suna Akeem Shittu a lokacin mummunan rikici a shekarar 2024.

DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane? An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi

Yayin yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Oyeyemi Ajayi ya bayyana cewa Segun Taiwo (36), Kehinde Ademola (46), Yahaya Adeniyi (45), Chinonso Samson (41), da Opadotun Michael (32) sun yi tarayya wajen yin hadin baki da kuma kisan Shittu.

“Na yi la’akari da cewa kotu za ta iya tabbatar da hadin baki a cikin ayyukan da suka kai ga mutuwar Shittu,” in ji shi.

Saboda haka, ya yanke wa kowanne daga cikin su hukuncin shekaru 20 a kurkuku saboda makirci, sannan ya yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin kisan kai.

“A kan tuhuma ta biyu, kowanne daga cikin waɗanda ake tuhuma an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya,” in ji alkalin.

Tun da farko, Lauyar gwamnatin Jihar, K. K. Oloso, ta bayyana yadda ƙaramin hatsarin hanya ya rikide zuwa mummunan hari.

Ta ce a ranar 10 ga Afrilu, 2024, da misalin ƙarfe 8:30 na dare, a kan titin Elepe, Arulogun Road, yankin Ojoo na Ibadan, waɗanda ake tuhuma tare da wasu da har yanzu ba a kama ba sun kai wa Shittu hari bayan ya yi karo da babur mai ɗauke da fasinjoji biyu.

“An ce ɓangarorin sun tafi wata mashaya kusa domin sasanta lamarin. A can, ƙungiyar masu babur ta nemi N50,000 don yin magani, amma Shittu ya iya bayar da N8,000 kawai. An hana shi barin wurin, aka cire masa kaya, kuma duk da cewa ya yi ƙoƙarin tserewa na ɗan lokaci, daga baya aka kewaye shi aka yanka shi da adda har lahira.”

Masu bincike daga baya sun gano motar tasi dinsa da mayafinsa a gaban shagon matar ɗaya daga cikin waɗanda aka yanke wa hukuncin.

Lauyar gwamnatin ta jaddada cewa laifukan sun sabawa sashe na 316 kuma laifuka ne a ƙarƙashin sashe na 319 da na 324 na Dokar Laifuka ta Jihar Oyo ta 2000, wadda ta tanadi hukunci mai tsanani ga makirci da kisan kai.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya
  • An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki
  • Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta
  • Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • ’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Wa Yara Miliyan 1.5 Rigakafin Cutar Shan Inna
  • An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia
  • Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru  Isa Chiroma Mafaka Ta Wucin Gagi