Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahoton Bankin Duniya kan yawan talakawa a Najeriya
Published: 9th, October 2025 GMT
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi fatali da sabon rahoton tattalin arziki da Bankin Duniya ya fitar, wanda ya kiyasta cewa mutane miliyan 139 na rayuwa cikin talauci.
Fadar ta bayyana adadin a matsayin wanda ya saba da zahiri kuma ya kauce wa hakikanin halin tattalin arzikin ƙasar.
SSANU da NASU za su yi wa gwamnati zanga-zanga kan rashin cika musu alƙawari 2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — KaluMai ba Shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya bayyana a shafinsa na X a ranar Laraba cewa dole ne a rahoton bai duba yanayin tsarin auna talauci na duniya ba.
“Duk da cewa Najeriya na daraja haɗin alakarta da Bankin Duniya kuma tana godiya da gudummawar da yake bayarwa wajen nazarin manufofi, adadin da aka ambata dole ne a duba shi cikin daidaitaccen yanayi. Bai dace da gaskiya ba,” in ji Dare.
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa adadin miliyan 139 ya samo asali ne daga layin talauci na duniya na dala $2.15 a kowace rana ga mutum ɗaya, wanda aka kafa a shekarar 2017 bisa tsarin da ake kira karfin iya sayen kayayyaki (PPP), kuma ba za a ɗauke shi a matsayin adadin da ke nuna yawan talakawan Najeriya kai tsaye ba.
Gwamnatin ta ce idan aka fassara wannan adadi zuwa naira bisa farashin musayar kuɗi na yanzu, dala $2.15 a rana na nufin kusan naira 100,000 a wata, wanda ya fi sabon mafi ƙarancin albashi na Najeriya na naira 70,000.
Rahoton ya ƙara da cewa tsarin PPP na amfani da bayanan tarihi na amfani da kaya (inda ƙididdigar ƙarshe a Najeriya ta kasance a shekarar 2018/2019), kuma sau da yawa yakan yi watsi da tattalin arzikin kasar na bayan fage da na dogaro da kai da ke tallafawa miliyoyin gidaje a ƙasar.
Gwamnati ta ce wannan adadi na bankin ƙididdigar duniya ce ta ƙiyasi, ba wai hakikanin yanayin rayuwa a shekarar 2025 ba.
Fadar Shugaban Ƙasa ta kuma bayyana cewa gwamnatin yanzu ta faɗaɗa shirye-shiryen jin ƙai da tallafi da dama don rage tasirin gyare-gyaren da aka yi kwanan nan, tare da shimfiɗa tubalin bunƙasa kasa mai ɗorewa a nan gaba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Bankin Duniya Fadar Shugaban Ƙasa ta
এছাড়াও পড়ুন:
Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya- Shugaba Tinubu
Daga Bello Wakili
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi cikin alhini da jimami.
Fitaccen malamin da ke Bauchi ya rasu ne a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2026, yana da shekaru 101.
Shugaban Ƙasan ya yi jimamin rasuwar jagoran Darikar Tijjaniyya, yana bayyana shi a matsayin ginshiƙin ɗabi’a wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da wa’azi.
Shugaba Tinubu ya ce rashinsa babban rashi ne ba ga iyalansa da dimbin mabiyansa kaɗai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.
Shugaban Ƙasa ya tuna da albarka da goyon bayan da ya samu daga marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a lokacin yakin zaɓen 2023.
“Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba, mai cike da natsuwa da hikima. A matsayinaa na mai wa’azi kuma masani kan tafsirin Alƙur’ani Mai Girma, yana da’awar zaman lafiya da tsoron Allah. Rasuwarsa ta bar babban gibi,” in ji Shugaban Ƙasa.
Shugaba Tinubu ya yi ta’aziyya ga mabiyan Shehun a ci da wajen ƙasa bisa wannan babban rashi.
Haka kuma ya ja hankalinsu da su girmama sunansa ta hanyar bin koyarwarsa ta zaman lafiya, ƙarfafa dangantakarsu da Allah, da kuma kasancewa masu taushin zuciya ga jama’a.