Aminiya:
2025-11-27@20:58:07 GMT

Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina

Published: 11th, October 2025 GMT

Duk da Najeriya na cikin yanayin damina, wanda ake ganin a lokacin ta fi samar da wutar lantarki ga ’yan ƙasarta, amma jama’a a jihohin Kaduna da Kano na ci gaba da kokawa kan ƙarancin wutar.

A duk shekara jama’a na more wutar lantarki a Nijeriya a lokacin damina saboda tashoshin ruwa na samar da wutar lantarki suna aiki da cikakken ƙarfinsu.

Amma, wasu masana a ɓangaren wutar sun shaida wa wakilinmu cewa duk da matsalolin masu nasaba da lalata kayan aiki da kuma ƙin biyan kuɗin wuta da wasu masu amfani da ita ke yi, kamfanonin rarraba wutar (DisCos) suna yin iya bakin ƙoƙarinsu wajen cike giɓin.

Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa ana ƙoƙarin daidaita rarraba wuta tsakanin yankunan masana’antu da wuraren da aka sanya wa mita da ke biyan kuɗin wuta, da kuma sauran gidaje.

’Yan Najeriya miliyan 60 na fama da taɓin hankali — Likita Sojoji sun mutu yayin da Boko Haram ta kai hari sansanin soji a Borno

A Katsina, rashin daidaito a rarraba wuta ya kawo babban cikas ga kasuwanci inda dubban masu sana’o’i suka rasa ayyukansu, gidaje kuma ke yin kwanaki ba tare da wuta ba.

Masu shayi, gidajen masu burodi, masu walda da sauran ƙananan sana’o’ da ke dogaro da wuta su ne suka fi shan wahala.

Dakta Isma’il Balarabe ya ce, “Kasuwancinmu sun durƙushe, mun yi asarar dukiya saboda rashin wuta. Wani lokaci ma, ba mu samun wutar awa ɗaya a rana.”

Shi ma Dakta Muktar Alkasim ya ce, “A gaskiya babu wutar da za ta iya tafiyar da kowace irin kasuwanci a nan Katsina. Wurin da ake samu ma, sai dai lokaci-lokaci kuma ƙarfin ba ya isa a kunna kayan aiki.”

Haka ma wata ’yar kasuwa, Misis Ngozi Anosike, ta ce sana’arta ta tsaya. “Akwai lokutan da muke yin mako guda ko fiye babu wuta. Idan ma ta zo, kusan awa ɗaya ne, kuma ba ta da ƙarfi.”

Hajiya Hannatu ta ce, “Ba zan iya sayen nama ko kifi da yawa ba saboda idan na saka a firji, zai lalace. Idan ma an samu wuta, ƙarfin bai isa ya ɗauki firji ba.”

Kano: An fifita masu biyan kuɗi da yawa

A Kano kuwa, rahotanni sun nuna akwai babban bambanci a yanyanin rarraba wutar lantarki tsakanin yankunan kasuwanci da na gidaje. Wuraren kasuwanci sun fi samun wuta saboda suna biyan kuɗin wuta mai tsada, yayin da gidaje da dama ke shafe mafi yawan lokaci babu wutar.

Jama’a na ƙorafi kan cewa kamfanin KEDCO na fifita wuraren kasuwanci a yayin da al’ummomi da dama ke kwana cikin duhu.

Wani mazaunin unguwar Na’ibawa, Ahmad Aminu, ya ce, “A da idan damina ta yi, mukan samu wuta sosai saboda tashoshin ruwa suna aiki da cikakken ƙarfi. Amma bana abin ya canza. Sai sa misalin ƙarfe 11 na dare ake kawo wuta, a ɗauke ƙarfe 5 na asuba.”

Yusuf Idris daga unguwar Kuntau ya ce, “A baya muna biyan kusan N5,000 a wata. Amma watanni biyu da suka gabata an ƙara zuwa fiye da N17,000. Amma duk da haka ba mu samun wutar sosai.”

Ya ƙara da cewa mutane da dama sun daina amfani da wutar gwamnati, sun koma mai amfani hasken rana.

Amma duk da haka, kwastomomi da ke biyan kuɗaɗe masu yawa, musamman masana’antu, suna amfana da ƙarin wuta bisa sabon tsarin.

Sama’ila Sulaiman, mai sana’ar ƙanƙara a yankin Farm Centre, ya ce, “Yanzu muna samun wuta har ta awa 22 a rana saboda mu muna biyan kuɗaɗe masu yawa.”

Martanin KEDCO

Kakakin Kamfanin KEDCO, Sani Bala Sani, ya ce a zahiri akwai tsayayyiyar wuta a yankunan Kano da Katsina da Jigawa, sai dai iska da ruwan sama kan karya turakun wuta a wasu wurare.

Ya ce, “A wasu lokuta ana samun ɗan tsaiko saboda gyaran da Kamfanin Tura Wutar Lantarki ta Ƙasa (TCN) ke yi, haka nan yajin aikin ma’aikatan PENGASSAN ya shafi rarraba wutar.”

Ya bayyana cewa kamfanin yana zuba jari a sabbin kayan aiki da kuma samar da wuta daga hasken rana. “Mun fara amfani da Hasken Solar a Kano domin ƙara ƙarfinmu. Muna fatan kafin ƙarshen shekara mai zuwa mu samar da aƙalla megawatt 150 daga hasken rana.”

Kaduna: Al’umma na cikin duhu

Mazauna yankin Tudun Wada da ke Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu ta Jihar sun koka cewa tun watan Satumba aka rage ba su wuta.

Hadiza Adam, wadda ke sana’at sayar da ruwan leda ta ce, “Yawanci dai ciki dare ake kawo mana wuta, lokacin da kowa ke barci. Don haka ribar da nake samu kullum tana raguwa.”

Muhammad Ahmed ya ce, “Yanzu wutar sai da ƙarfe 1 na dare ake kawo ta su kuma ɗauke da safe. Mu ba masu gadi ba ne da za mu rika zama don jiran wuta. Amma duk wata sai sun kawo mana bill cewa suna bin mu dubban nairori.”

Unguwanni da dama a Kaduna—kamar Rigasa da Hayin Ɗan Mani da Zango da Sabon Gari da sauransu—sun kai watanni suna yin kwanaki babu wuta. Wasu sun koma yin rajista kai wayoyinsu wajen masu cajin ko amfani da injin janareta.
Badamasi Isa da ke yankin Hayin Ɗan Mani ya ce,

“Tun watan Fabrairu ba mu samun wuta da dare. Hakan ya rusa kasuwancin masu kayan sanyi da masu walda.”

Mustapha Baban Sultan daga yankin Millennium City ya ce, “Yanzu tsarin ya zama ‘iya kuɗinka iya shagalinka’. Masu arziki suna Band A, suna samun wuta sosai amma suna biyan kuɗaɗe masu yawa. Talakawa kuwa babu wuta amma ana cajin su.”

Wasu mazauna sun bayyana cewa saboda rashin wuta sai sun koma amfani da hasken rana wajen samun ruwan sha da gudanar da rayuwa.
Duk da haka, Kamfanin Wutar Lantarki na Kaduna ya alaƙanta matsalar da lalata layin wuta da iska mai ƙarfi ta yi a wannan daminar.

Dalilin ƙarancin wuta a Arewa

Rahoton Hukumar Rarraba Wuta ya nuna cewa daga cikin megawat 4,025 da ake samarwa a Nijeriya, yankin Arewa na samum kusan kashi ɗaya bisa huɗu ne kawai.

Masu ruwa da tsaki sun danganta hakan da matsalar rashin saka hannun jari a ɓangaren rarraba wutar da matsalar satar kayayyakin wuta da kuma rashin biyan kuɗin wuta daga jama’a.

Shugaban Ƙungiyar Kare Haƙƙodin Kwastomomi ta Nijeriya, Kunle Olubiyo, ya ce rushewar masana’antu a Arewa ta rage buƙatar wuta, sannan satar wuta da rashin kayan aiki na zamani su ma suna kawo cikas.

Ya ce, “A da masana’antu a Kano, Kaduna da Maiduguri suna jan wuta sosai. Amma yanzu sun lalace, sai Kano kawai ta rage. A Kanon ma akwai matsalar sata da kuma rashin isassun kayan aiki a layin rarrabawa.”

Ya ƙara da cewa, “Kamfanonin rarraba wuta kan fifita wuraren da za su iya dawo da kuɗaɗensu. Idan aka kai wuta wuraren ba a biyan kuɗi, sukan ki karɗar nauyin rabon. Wannan shi ne abin da ya fi dagula lamarin a Arewa, inda wasu wurare ke samun ƙarin wuta, wasu kuma ba su samu wutar ba,” in ji shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Lantarki matsalar biyan kuɗin wuta wutar lantarki rarraba wuta hasken rana

এছাড়াও পড়ুন:

Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai

Babbar Kotun Jihar Oyo da ke Ibadan, babban birnin jihar, a ranar Litinin ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutum biyar da ta samu da laifin kashe wani direban tasi.

Kotun dai ta sami mutanen ne da laifin kashe direban mai suna Akeem Shittu a lokacin mummunan rikici a shekarar 2024.

DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane? An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi

Yayin yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Oyeyemi Ajayi ya bayyana cewa Segun Taiwo (36), Kehinde Ademola (46), Yahaya Adeniyi (45), Chinonso Samson (41), da Opadotun Michael (32) sun yi tarayya wajen yin hadin baki da kuma kisan Shittu.

“Na yi la’akari da cewa kotu za ta iya tabbatar da hadin baki a cikin ayyukan da suka kai ga mutuwar Shittu,” in ji shi.

Saboda haka, ya yanke wa kowanne daga cikin su hukuncin shekaru 20 a kurkuku saboda makirci, sannan ya yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin kisan kai.

“A kan tuhuma ta biyu, kowanne daga cikin waɗanda ake tuhuma an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya,” in ji alkalin.

Tun da farko, Lauyar gwamnatin Jihar, K. K. Oloso, ta bayyana yadda ƙaramin hatsarin hanya ya rikide zuwa mummunan hari.

Ta ce a ranar 10 ga Afrilu, 2024, da misalin ƙarfe 8:30 na dare, a kan titin Elepe, Arulogun Road, yankin Ojoo na Ibadan, waɗanda ake tuhuma tare da wasu da har yanzu ba a kama ba sun kai wa Shittu hari bayan ya yi karo da babur mai ɗauke da fasinjoji biyu.

“An ce ɓangarorin sun tafi wata mashaya kusa domin sasanta lamarin. A can, ƙungiyar masu babur ta nemi N50,000 don yin magani, amma Shittu ya iya bayar da N8,000 kawai. An hana shi barin wurin, aka cire masa kaya, kuma duk da cewa ya yi ƙoƙarin tserewa na ɗan lokaci, daga baya aka kewaye shi aka yanka shi da adda har lahira.”

Masu bincike daga baya sun gano motar tasi dinsa da mayafinsa a gaban shagon matar ɗaya daga cikin waɗanda aka yanke wa hukuncin.

Lauyar gwamnatin ta jaddada cewa laifukan sun sabawa sashe na 316 kuma laifuka ne a ƙarƙashin sashe na 319 da na 324 na Dokar Laifuka ta Jihar Oyo ta 2000, wadda ta tanadi hukunci mai tsanani ga makirci da kisan kai.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi da 34 a Kaduna
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
  • Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina