Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza
Published: 10th, October 2025 GMT
Cikin darussan da wannan rikici ya tabbatar mana, akwai rashin tasirin amfani da karfin tuwo wajen warware duk wani rikici. Tabbas karfin soji kadai ba zai iya magance takaddama ko tashin hankali ba, ballantana ya wanzar da tsaro da walwalar bil’adama.
Muna iya ganin hakan a zahiri, idan mun lura da yadda Isra’ila ta nuna a fili cewa hare-haren da ta kwashe shekaru biyu tana kaiwa sassan Gaza za su iya kawo karshen barazanar da ta ce kungiyar Hamas ke haifar mata, amma sai ga shi daga karshe sakamako ya nuna akasin haka.
A wannan gaba, ya wajaba a jinjinawa kasashe masu son zaman lafiya kamar Sin, da mafiya yawan kasashe masu tasowa, wadanda suka jima suna maraba baya ga cimma daidaito, da kawo karshen wannan tashin hankali da ya ki ci ya ki cinyewa, ciki har da sama da kasashe 150 membobin MDD da suka amince da Falasdinu a matsayin kasa.
Ko shakka babu, lokaci ya yi da za a kawo karshen tashe-tashen hankula, da samar da isasshen agajin jin kai ga masu bukata a Gaza, kana a komawa tattaunawar diflomasiyya ta kafa kasashe biyu masu cin gashin kai, a matakin karshe na ganin bayan wannan tashin hankali baki daya.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila Tana Ci Gaba Da Rushe Gidaje A Yankin Gaza
Da safiyar Yau Laraba ne sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila su ka kai hare-hare a yankuna daban-daban na zirin Gaza, tare da rushe gidaje da dama. Sojojin mamayar sun yi amfani da jiragen sama marasa matuki da kuma tankokin yaki domin rushe gidajen. A arewacin Gaza da gabashin Jabaliya sojojin na mamaya sun yi amfani da manyan bindigogi akan gidajen fararen hular. A unguwar “Tuffah” ma an ga yadda sojojin mamayar su ka aike da jiragen yaki marasa matuki.A can kudancin Gaza kuwa jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ne su ka kai hare-hare akan barin Bani-Suhaila a gabashin Khan-Yunus,a lokaci daya kuma manyan bingigoginsu su ka bude wuta akan iyaka.
Tun bayan da aka tsagaita wutar yaki a cikin watan Oktoba ne, Sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ilan suke ci gaba da kai hare-hare akan Gaza ba tare da kakkautawa ba. Daga tsagaita wutar zuwa yanzu adadin Falasdinawan da su ka yi shahada a sanadiyyar hare-haren na ‘yan sahayoniya sun haura 300.
Hukumar agaji a yankin na Gaza ta yi gargadi akan cincirindon ‘yan hijira da suke rayuwa a cikin hemomin da babu kayan da rayuwa take da bukatuwa da su domin ci gaba. Ruwan sama yana ci gaba da sauka a yankuna mabanbanta na Gaza da sanyi yake karuwa ba tare da samar da na’urorin dumama hemomin ba.
Kakakin kungiyar agaji a Gaza Mahmud Basal ya ce; Suna samun dubban koke daga Gaza cewa hemomin da mutane suke rayuwa a ciki ba su dace da rayuwa ba ko kadan.Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe November 26, 2025 Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta November 26, 2025 Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki November 26, 2025 Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin November 26, 2025 Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah November 26, 2025 UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin Lebanon November 26, 2025 Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Ga Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci