Aminiya:
2025-11-27@20:48:55 GMT

Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi

Published: 11th, October 2025 GMT

Aƙalla mutane biyu ne suka mutu a rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a unguwar Dambo, wani kauye da ke da tazarar ’yan kilomita daga Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.

Wani mazaunin yankin mai suna Ɗanladi Usman ya ce rikicin ya fara ne bayan an kashe wani mutum mai suna Sule yayin da yake aiki a gonarsa.

“Kashe Sule ya tayar da hankulan al’umma, inda manoma suka ɗauki fansa suka kashe wani makiyayi da har yanzu ba a gano sunansa ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa makiyayan sun sha faɗa da manoma a kwanakin baya bayan sun aike musu da sako cewa su hanzarta girbe amfanin gonakinsu domin za su riƙa wucewa da shanunsu ta gonakin nan ba da daɗewa ba.

An yi jana’izar sojojin da ’yan bindiga suka kashe a Kebbi  Rashin wutar lantarki ya rusa harkoki a Kaduna, Kano da Katsina

“A lokacin da wasu manoma suka je gonakinsu domin yin aiki, sai makiyaya suka kai musu hari, daga nan ne aka shiga tashin hankali,” in ji shi.

Wani mazaunin yankin, Abubakar Aliyu, ya roƙi gwamnati da ta kawo ƙarshen wannan rikici na dogon lokaci tsakanin manoma da makiyaya.

“Wannan matsala ba sabuwa ba ce, kuma sarakunan gargajiya sun san da ita. Muna fatan a samu adalci ga waɗanda abin ya shafa, kuma gwamnati ta kawo ƙarshen wannan rikici,” in ji shi.

Rundunar ’yan sanda a jihar ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba domin jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ba a iya samun sa a waya ba lokacin da ake haɗa wannan rahoto.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 11, ciki har da wat mai juna biyu da ƙananan yara Jihar Kwara.

Maharan sun kai farmaki tare da sace mutanen ne a yankin Eruku da ke Ƙaramar Hukumar Ekiti da ke jihar.

Ƙarin bayani na tafe…

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka
  • Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi
  • DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
  • An ceto ’yan mata 24 d aka yi garkuwa da su a makaranta a Kebbi
  • Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
  • An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi
  • Abin da ya sa nake haxa harkar fim da harkar karatu-Nabila
  • ’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara