Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
Published: 11th, October 2025 GMT
“Abin takaici ne ace Nijeriya tana karancin Mlaman makaranta da suka kai 194,876 a makarantun gwamnati a fadin tarayyar Nijeriya. Halin da makarantunmu na Sakandare suke ciki shi ma lamarin bata canza zane ba. Rashin isassun Malamai shi ma lamarin abin damuwa ne domin kuwa sannu a hankali hakan zai iya shafi samar da ingantaccen ilimi a makarantunmu kamar yadda sakamakon hakan ba zai haifar da da mai ido ba cewar, Amba”.
Don haka ya ja kunnen Nijeriya cewa rashin isassun Malaman zai iya kawo cikas wajen kokarin da Nijeriya ta ke yi na cimma muradin ci gaba na 4 (SDG 4) da ya kunshi ingantaccen ilimi ba tare da wani bambanci ba, tsakanin gwamnatoci uku ba tare da wani bata lokaci ba a dauki mataki wanda ya dace.
Ya ci gaba da bayanin“Mu ma mun sa bakinmu wajen kira da babbar murya domin aikin koyarwa ya kasance abinda kowa yake sha’awar yi ne ga matasa masu tasowa. Dole ne gwamnati ta dauki yawan Malaman da suka kamata a dauka tare da yin la’akari da ingancinsu, domin a ci gaba da samar da ingantaccen ilimi a tsarin tafiyar da makarantunmu,”.
Duk alkawarin da aka yi na jin dadin Malaman makaranta ba a cika shi
Amba har ila yau nya nuna rashin jin sadinsa kan yadda aka kasa cika alkawuran jin dadin da aka yi wa Malaman makaranta’, duk kua da yake an yi alkawarin tun, a shekarar 2020. Yana iya tunawa zamanini mulkin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da wasu abubuwan da za su taimaka wadanda suka hada da tsarin albashi na musamman, da kuma irin lokacin da za su yi ritaya, da gidaje masu saukin kama haya a kauyuka amma suma ba a kai ga yinsu ba.
“Abin takaici ne cewar bayan lamarin shekarun da za’ayi ritaya daga aiki idan an kai an gabatar dasu, 65, abinda Jihohi 22 da Babban Birnin Tarayya Abuja, yawancin duk abubuwan da aka amince za ayi masu har yanzu ba a cika alkawarin ba. Muna kiran gwamnatin tarayya da Jihohi su cika dukkan aalkawuran za aka yi na game da jin dadin Malaman makarabta kamar yadda suke, saboda a samu damar dawo da irin martabar da aka san aikin koyarwa yana da ita kamar yadda ya ce,”.
Game da aiwatar da dolar mafi karancin albashi na kasa kamar yadda aka amince a shekarar 2024, Shugaban kungiyar Malamai ta kasa yace Jihohi goma basu cika ka’idar ba kamar yadda take ba, ta aiyatar da mafi karancin albashi, yayin da Jihohi hudu ma basu fara biya ba.
Kungiyar Malaman ta yi magana kan rashin ba shi bangaren ilimi kuaddaen da suka dace a bashi, inda suka ce Nijeriya ta ci gaba da kasancewa a baya kan yadda mizani na kasa da kasa wato shawarar da aka yanke na kason da aka amincewa bangaren ilimi, inda aka ce a rika ware ma shi bangaren kashi 4–6 na kudaden da suk shigo ma kasa a duk shekara GDP oko kuma 15–20 na gaba dayan kasafin kudin zuwa ga bangaren ilimi.
Amba ya ce ya zuwa wayan Maris na shekarar 2024, kamar Naira biliyan 54 da aka ware ma bangaren ilimin bai daya (UBE) har yanzu ba a samu amsar ko kwabo ba saboda rashin bada kaso da akace a rika badawa wato Jihohi da Babban Birnin Tarayya Abuja.
“Rashin yadda Jihohi suka ki biyan kason na sun a kudi kaman a kai ga basu tallafin na UBEC, hakan ya kara gurgunta rashin bunkasa ilimin na bai daya, da kuma taimakawa tsare= tsaren da za su jawo hankalin Malamai ya raja’a kan aikin koyarwa kamar yadda ya ce,”.
Hakanan ma kungiyar bata ji dadin da wani kokarin na gwamnatin Jihar Edo ban a ta mika wasu makarantun gwamnati ga Hukumomi da ba nata ba, da kuma kungoyoyi masu zaman kansu, abinda ta kalla a matsayin wasu matakai ne da za su kawo cikas wajen cimma burin samar da ilimi kyauta.
Kungiyar ta ce wadannan matakan suna kawo barazana wajen samar da adalci, musamman ma ga irin wadanda basu da halin ba ‘ya’yan nasu ilimi, kamar ‘yanmata, yara masu kulawa ta musamman, da kuma wadanda suke can kauyuka.
Ta yi kira da gwamnatin Jihar Edo ta daukai matakan da suka kamata kamar yadda tsarin mulki ya tanadar wajen samar da ilimi kamar yadda lamarin yake yadda doka ta tanadar.
Kungiyar ta yi magana ne kan muhimmancin kulawa jin dadin Malamai,inda ta yi tunatarwa da rahoton shekarar 2008 kan kungiyar ma’aikata ta duniya da kuma hukumar ILO/UNESCO, in da aka yi bayanai kan muhimmancin jin dadin Malamai ’ a matsayin irin abubuwan da suke jan mutane na sha’awar aikin koyarwa da kuma ci gaba da zaman kwararrun a makarantu.
Mr. Bobby Winful na Kwalejin gwamnatrin tarayya ta maza da je Abuja Abuja, ya dora alhakin rashin Malamai kan wadansu abubuwa, da suka hada da rashin kulawa dajin dadin Malamai, da kuma karancin Malaman d aka amince da su masu lasin na aikin koyarwa.
“Muna karancin Malamai ne saboda yadda ba a kulawa da hakkin Malamai bare jin dadinsu abin ba wani abin azo a gani bane. Sau da yawa wasu wuraren ba ma a biyan albashin. Abin mamaki ace wai wasu Malaman suna zuwa aiki har tsawon shekara uku ba tare da albashi ba. Hakan shi yasa ake samun raguwar Malamai masu takardar shedar da aka amince sun cancanta su koyar, saboda yawancin dalibai a Jami’a basu sha’wara karanta darasin ilimi, duk wannan ba domin komai ba saboda babu wasu abubuwan da za su ja hankali a sharuddana aikin nasu, ba wata maganar jin dadinsu da kuma ,aganar albashi kamar yadda ya yi karin bayani,”.
Shugabar makarantun Chalcedony, Dakta. Mary Chinwuba, ta bayyana babban dalilin da ya kawo karancin Malamai a Nijeriya saboda babu wasu abubuwan jan hankali daga cikin sharuddan aikinsu ba, don haka ta yi kiran da ayi gaggawar inganta sharuddan aikinsu da kuma jin dadinsu.
Gwamnati ta yi kira ga Malaman makaranta da su hada kansu
A na shi jawabin Minisatan ilim, Dakta. Maruf Olatunji Alausa, ya kara jaddada manufar gwamnati ta sanin cewa Malamiai sune babban tubali wajen gina kasa da ci gabantar.
Ya yi karin haske “Malamai sune ginshikin ci gaban al’umma hakanan kuma babbar hanyar bi zuwa wajen bunkasa al’umma da kuma kasa.Don haka idan an yiwa Malamai wani ihisani hakan baya nuna ta hakan ne aka san da su ba, manufa kuwa sun kasance tamkar zuba jari ne domin samun ingantaccen ilimi, karuwar da dalibi zai yi, da kuma yadda kasa za ta kasance cewar Dakta Alausa.
Dakta Alausa ya bayyana hanyoyi masu yawa domin inganta shi aikin koyarwar wadanda suka hada da, tsarin ilimin Malami na kasa, tsarin sa ido na hukumar al’amuran Malamai, ci gaban bunkasa kwarewar aikin Malamta na NTI, da kuma irin yadda hukumar ilimin bai daya take taimakawa shi bangaren na ilimi.
An karrama Gwamnoni hudu saboda inganta jin dadin Malaman makaranta’
An karrama gwamnoni hudu saboda yadda suke taimakawa harkar ilimi ya wuce duk irin tunanin da mutum zai yi, saboda bunkasa jin dadin Malamai da yadda lkamarin ilimi yake a Jihohin nasu.
An yi bikin karramar ne, a Eagle Skuare, Abuja, gwamnonin da aka karrama sun hada da Katsina, Adamawa, Kogi, da kuma Delta saboda tsare-tsaren da suka bullo da su wadanda za su karawa Malamai kwarin ne su rungumi aikin nasu da gaskiya, da kuma gyara hanyoyin da ake amfani da su wajen koyarwa ko kuma a takaice yanayin da yafi dacewa da koyarwa da koyo.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
Babbar Kotun Jihar Oyo da ke Ibadan, babban birnin jihar, a ranar Litinin ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutum biyar da ta samu da laifin kashe wani direban tasi.
Kotun dai ta sami mutanen ne da laifin kashe direban mai suna Akeem Shittu a lokacin mummunan rikici a shekarar 2024.
DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane? An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a KebbiYayin yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Oyeyemi Ajayi ya bayyana cewa Segun Taiwo (36), Kehinde Ademola (46), Yahaya Adeniyi (45), Chinonso Samson (41), da Opadotun Michael (32) sun yi tarayya wajen yin hadin baki da kuma kisan Shittu.
“Na yi la’akari da cewa kotu za ta iya tabbatar da hadin baki a cikin ayyukan da suka kai ga mutuwar Shittu,” in ji shi.
Saboda haka, ya yanke wa kowanne daga cikin su hukuncin shekaru 20 a kurkuku saboda makirci, sannan ya yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin kisan kai.
“A kan tuhuma ta biyu, kowanne daga cikin waɗanda ake tuhuma an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya,” in ji alkalin.
Tun da farko, Lauyar gwamnatin Jihar, K. K. Oloso, ta bayyana yadda ƙaramin hatsarin hanya ya rikide zuwa mummunan hari.
Ta ce a ranar 10 ga Afrilu, 2024, da misalin ƙarfe 8:30 na dare, a kan titin Elepe, Arulogun Road, yankin Ojoo na Ibadan, waɗanda ake tuhuma tare da wasu da har yanzu ba a kama ba sun kai wa Shittu hari bayan ya yi karo da babur mai ɗauke da fasinjoji biyu.
“An ce ɓangarorin sun tafi wata mashaya kusa domin sasanta lamarin. A can, ƙungiyar masu babur ta nemi N50,000 don yin magani, amma Shittu ya iya bayar da N8,000 kawai. An hana shi barin wurin, aka cire masa kaya, kuma duk da cewa ya yi ƙoƙarin tserewa na ɗan lokaci, daga baya aka kewaye shi aka yanka shi da adda har lahira.”
Masu bincike daga baya sun gano motar tasi dinsa da mayafinsa a gaban shagon matar ɗaya daga cikin waɗanda aka yanke wa hukuncin.
Lauyar gwamnatin ta jaddada cewa laifukan sun sabawa sashe na 316 kuma laifuka ne a ƙarƙashin sashe na 319 da na 324 na Dokar Laifuka ta Jihar Oyo ta 2000, wadda ta tanadi hukunci mai tsanani ga makirci da kisan kai.