Kungiyoyin Falasdinawa Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza
Published: 11th, October 2025 GMT
Bangarorin kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun fitar da sanarwar hadin gwiwa kan tsagaita bude wuta a Gaza
Kungiyar Hamas, Jihad Islami, da kuma Popular Front mai fafatukar ‘yantar da Falasdinu, sun fitar da sanarwar hadin gwiwa a jiya Juma’a, inda suka bayyana matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza, inda suka yi maraba da gwagwarmayar al’ummar Falastinu, musamman a Gaza wajen fuskantar laifukan yahudawan sahayoniyya.
Kungiyoyin Hamas da na sauran kungiyoyin Falasdinu sun yaba da jarumtar gwagwarmayar da ta janyo hasara ga makiya, suna masu jaddada cewa: “Muradin jama’a da ‘yan gwagwarmaya ya fi duk wani yunkuri na murkushe su.” Har ila yau, sun jinjinawa “bangarori masu goyon bayansu a Yemen, Lebanon, Iran, da Iraki saboda goyon bayan da suke ba wa Falasdinawa.”
Sun gode wa masu shiga tsakani na Masar, Qatar, da Turkiyya, da kuma duk wadanda suka ba da gudummawar goyon bayan shawarwarin, suna mai kira ga Amurka da masu shiga tsakani da su ci gaba da bin sharuddan yarjejeniyar da kuma hana kaucewa daga kansu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya October 11, 2025 Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta October 11, 2025 Putin: Natanyahu Yana Son Warware Matsaloli Da Iran Cikin Lumana Ba Tare Da Yaki Ba October 10, 2025 Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha October 10, 2025 Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa October 10, 2025 Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka Rusa A Arewacin Yankin October 10, 2025 Rahotanni : Isra’ila ta fara janye dawa wasu yankuna na Gaza October 10, 2025 Amurka ta kakaba wa wasu kamfanoni 50 takunkumi saboda sayen man Iran October 10, 2025 Isra’ila ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki October 10, 2025 Mohajirani: Iran na goyon bayan shawarar Falastinawa kan batun dakatar da bude wuta October 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
MDD ta yi gargadi game da hadarin yunwa a wasu sassa na duniya
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya guda biyu sun yi gargadi a jiya Laraba cewa, miliyoyin mutane a yankuna akalla 12 da ke fuskantar rikici a duniya, ciki har da Sudan da zirin Gaza, na fuskantar barazanar yunwa, tare da gabatar da bukatar gaggawa na samar da kudade don magance gibin tallafin abinci, sakamakon raguwar tallafin da kasashen duniya ke bayarwa.
A cikin wani rahoto na hadin gwiwa, Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) da Hukumar Abinci da Aikin Noma (FAO) sun sanya kasashen Haiti, Mali, Sudan ta Kudu, da Yemen cikin kasashen da ke fuskantar barazanar yunwa.
Rahoton ya kuma bayyana halin da ake ciki na yunwa a wasu kasashe shida wato Afganistan, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Myanmar, Najeriya, Somaliya, da Syria, a matsayin mai matukar tayar da hankali.
Kungiyoyin biyu sun yi gargadin cewa rashin samun kudade na agajin jin kai na nuni ne Babbar matsalar da za a iya matukar dai ba a dauki matakan gaggawa ba.
Hukumar samar da abinci ta duniya da FAO sun yi kira da a kara samar da n tallafi daga gwamnatoci da masu hannu da shuni, tare da lura cewa kudaden da aka samu har zuwa karshen watan Oktoba sun kai dala biliyan 10.5 ne daga cikin dala biliyan 29 da ake bukata domin taimakawa masu fama da matsaloli irin wadannan a duniya.
Rahoton ya yi nuni da cewa, Amurka wadda ita ce kasar da ta fi bayar da tallafi ga kungiyoyin biyu a bara, ta rage yawan taimakon da take ba wa kasashen waje karkashin jagorancin shugaba Donald Trump, sannan wasu manyan kasashe ma sun rage ayyukan ci gaba da taimakon jin kai, ko kuma sun bayyana aniyarsu ta rage yawan taimakon da suke bayarwa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka Na Shirye-Shiryen Aikewa Da Sojoji Guda 1000 A Iyakar Isra’ila Da Yankin Gaza November 12, 2025 Shugaban Iran Ya Aike Da Wasika Ta Musamman Zuwa Ga Yarima Mai Jiran Gado Na Saudiyya November 12, 2025 Gwamntin Nijeriya tace Za ta Kare Sojojinta Da Ke Bakin Aiki November 12, 2025 Iran Da Pakistan Sun yi Kira Da Yin Aiki Tare Don Tunkarar Makiyansu November 12, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Iran Da Rasha Sun Tattauna Kan Rikicin Yankin November 12, 2025 Gabon: An Daure Mata Da ‘Dan Tsohon Shugaban Kasa Bongo Shekaru 20 A Gidan Yari November 12, 2025 Tanzania: MDD Ta Yi Kira Da A Yi Bincike Akan Daruruwan Mutanen Da Aka Kashe Sanadiyyar Rikcin Zabe November 12, 2025 Iran Ta Zama Memba A Kungiyar Tattara Bayanai Na Ilimomi Da Kere-kere Ta Duniya ( ISKO) November 12, 2025 Iran: Ta’addanci barazana ce ga dukkan yankin November 12, 2025 Araghchi: Matsalar Yammacin duniya ita ce ci gaban kimiyyar Iran ba makaman nukiliya ba November 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci