2025-11-27@21:51:59 GMT
إجمالي نتائج البحث: 292
«allurar rigakafin cutar»:
161-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku, kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Mrtada Muttahari, ko kuma cikin littafan Mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ////… Ma dalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Haddan dan Aliyu (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda wasu...
Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta wanke Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano da aka dakatar, Alhaji Naziru Yau, daga dukkanin zarge-zargen da aka masa. Wannan ya ba shi damar komawa bakin aikinsa da shugabancin Ƙaramar Hukumar Rano. An kama Faston da ake zargi da yi wa mambobin cocinsa 3 fyade ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su An dakatar da Yauyayin da ake bincike a kansa. Bayan sanar da dawo da shi kan kujerunsa, dubban magoya bayansa ne suka tarbe shi da murna a kan iyakar Rano da Bunkure. Daga nan ya wuce zuwa fadar Sarkin Rano, Muhammad Isa Umaru, wanda ya yi masa addu’a kafin ya sake komawa ofis...
Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta wanke Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano da aka dakatar, Alhaji Naziru Yau, daga dukkanin zarge-zargen da aka masa. Wannan ya ba shi damar komawa bakin aikinsa da shugabancin Ƙaramar Hukumar Rano. An kama Faston da ake zargi da yi wa mambobin cocinsa 3 fyade ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su An dakatar da Yauyayin da ake bincike a kansa. Bayan sanar da dawo da shi kan kujerunsa, dubban magoya bayansa ne suka tarbe shi da murna a kan iyakar Rano da Bunkure. Daga nan ya wuce zuwa fadar Sarkin Rano, Muhammad Isa Umaru, wanda ya yi masa addu’a kafin ya sake komawa ofis...
Hukumar Zakka ta Jihar Zamfara ta sanar da shirye-shiryen aurar da marayu 200 ’yan asalin jihar a wani yunƙuri na tallafa wa marasa galihu. Sakataren hukumar, Malam Habibu Balarabe ne ya bayyana hakan, inda ya ce an kammala dukkan shirye-shirye domin gudanar da bikin auren a ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2025, a harabar hukumar da ke Gusau. Ya ce an gudanar da cikakken bincike da tantancewa kafin zaɓar waɗanda za su ci gajiyar shirin, domin tabbatar da cewa auren ya kai ga mutanen da suka fi buƙatar taimako na haƙiƙa. Sakataren ya ƙara da cewa, hukumar za ta ba wa amaren kayayyakin tallafi da kayan amfani na gida domin taimaka musu su fara sabuwar rayuwarsu cikin sauƙi da kwanciyar...
Ministan wuraren tarihi da yawon bude ido da sana’o’in hannu na iran Sayyid Ridha Salihi Amiri ya bayyana cewa: A Halin yanzu Iran tana da wuararen tarihi 20 da ake yi gani, da kuwa wasu 28 da suke a karkashin hukumar dake kula da kayan tarihi ta MDD ( Unesco). Ministan na Iran wanda ya ziyarci wani wurin tarihi a garin Zanjan a yau Alhamis, ya yi Ishara da muhimmanci shigar da wuraren a karkashin hukumar dake kula da kayan tarihi ta duniya. Haka nan kuma ya bayyana cewa da akwai wasu wuraren na Iran da nan gaba za a yi rijistarsu a karkashin hukumar Unesco ta MDD. Idan kuwa aka yi hakan, to za ta zama ita ce ta...
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya ce kasarsa na binciken wani jirgin sama da ya kawo ‘yan gudun hijirar Falasdinawa 153 kasar ba tare da takardun shiga ba. “Wadannan mutane ne daga Gaza wadanda, ta wata hanya, suka tsinci kansu cikin jirgin sama da ya tashi daga Nairobi (babban birnin Kenya) kafin su iso nan,” in ji Ramaphosa ga manema labarai, yana mai cewa hukumomin leken asiri da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida na kasar suna binciken lamarin. A ranar Alhamis, Afirka ta Kudu ta ba Falasdinawan su 153 mafaka ta kwanaki 90, duk da cewa an hana su shiga saboda sun gaza amsa tambayoyin da aka musu kuma fasfo dinsu ba su da tambarin tashi, ko tikitan komawa...
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa, ya yi watsi da hukuncin da Jam’iyyar PDP ta yanke na korar Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, daga jam’iyyar. Aminiya ta ruwaito yadda PDP ta kori Wike, Sanata Samuel Anyanwu da tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, a yayin babban taron PDP da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo. Cif Olabode George ne, ya gabatar da ƙudirin korarsu, kuma Shugaban PDP na Jihar Bauchi, Samaila Burga, ya mara masa baya. Sai dai bayan sanarwar, Gwamna Fintiri ya fitar da wata sanarwa, wadda ya nesanta kansa daga matakin da jam’iyyar ta ɗauka. Ya ce ba ya goyon bayan korar da aka yi wa Wike, domin hakan zai ƙara haifar da rikici a cikin jam’iyyar....
Gwamnan Sule ya ce irin wannan jaridar da ke kan gaba ta zaɓo shi a matsayin gwarzon gwamna, abun farin ciki ne sannan ya yaba wa kamfanin bisa tabbatar da sahihancin labarai da daidaitasu wanda hakan yasa ta bambanta ta da takwarorinta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Nijeriya — Minista November 12, 2025 Manyan Labarai An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano November 12, 2025 Manyan Labarai Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro November 12, 2025
Hukumar Tsarawa da Raya Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) ta gudanar da horon cikin gida na farko ga ma’aikatanta, wanda ya mayar da hankali kan aiwatar da dokokin aikin gwamnati, kyawawan ɗabi’un aiki da kuma ingancin ayyuka. Wannan horo, wanda ya zama muhimmin mataki a shirin ƙarfafa ƙwarewar ma’aikata na hukumar, an shirya shi ne domin haɓaka inganci a ayyuka da ƙarfafa ƙwararru da tabbatar da bin ƙa’idojin aikin gwamnati yadda ya kamata. A jawabinta, Manajiyar Darakta ta KNUPDA, Arc. Hauwa Hassan Tudun-Wada, ta bayyana horon a matsayin muhimmiyar hanya ta gina al’adar ladabi da biyayya da nagarta a cikin ma’aikatan gwamnati. Ta yaba da jajircewa da himmar ma’aikata wajen halartar shirin, inda ta jaddada cewa fahimta da bin dokokin...
UNICEF ta yi gargadin cewa Isra’ila na hana shigar da muhimman kayan aikin da ake buƙata don allurar rigakafi a Gaza, wanda hakan ke kawo cikas ga ƙoƙarin isa ga yara a yankin da yaƙi ya daidaita. Hukumar ta ce kayayyakin, ciki har da sirinji da ake amfani da su don allurar rigakafi na yau da kullun da kwalaben madarar jarirai, har yanzu suna nan a wuraren bincike, duk da ci gaba da tsagaita wuta da kuma ƙaruwar buƙatun jin kai. UNICEF ta bayyana cewa a halin yanzu tana gudanar da Shirin allurar rigakafi ga yara ‘yan ƙasa da shekara uku, waɗanda da yawa daga cikinsu sun rasa allurar rigakafi na yau da kullun a cikin shekaru biyu da suka...
Shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran ya sanar da cewa za a harba tauraron dan adam guda uku zuwa sararin samaniya cikin watanni biyu masu zuwa. Hassan Salarieh, shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran, a yayin jawabi a wani taron fasahar sararin samaniya a Tehran, ya nuna muhimmancin ayyukan da suka shafi bayanai na tauraron dan adam , kuma ya bayyana cewa an shirya harba tauraron dan adam guda uku na: Zafar, Paya, da Kowsar a farkon hunturu. A cewar Pars Today, ya yi Ishara da hadin gwiwar da Iran ke yi da wasu kasashe a fannin sararin samaniya, yana mai ambaton ayyukan hadin gwiwar da China kan ayyukan hadin gwiwar bincike da kasashen mambobin ECO. Wannan ayyukan hadin gwiwar...
Kasar Sin ta yi nasarar harba sabon rukunin taurarin dan Adam da da’irarsu ke kusa da doron kasa, daga cibiyar harba kumbunan kasuwanci ta lardin Hainan dake kudancin kasar. An harba rukunin taurarin wanda shi ne irinsa na 13, da ya kunshi jerin taurarin dan Adam masu samar da sadarwar intanet ne da misalin karfe 10:41 na safiyar yau Litinin agogon Beijing. An kuma yi amfani da rokar Long March-12 wajen harbawa, inda tuni suka shiga da’irarsu. (Mai fassara: FMM) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Ci Gaba Da Bude Kofa Mai Zurfi A Sin November 10, 2025 Daga Birnin Sin Mataimakin Firaministan Kasar Sin Zai Ziyarci Kasashen Guinea Da Saliyo November...
Tsohon Shugaban Amurka Biden ya yi dirar mikiya kan shugaba Trump cewa; Ba wai kawai yana lalata Fadar White House ba ne har ma da dukkan al’ummar kasar Tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya yi dirar mikiya kan magajinsa Donald Trump, yana mai cewa: Shugaban na yanzu ba wai kawai ya kawo wani abin kunya ga Fadar White House ba ce, har ma ga dimokuradiyyar Amurka. CNN ta ambato Biden yana cewa: A lokacin wani taron Jam’iyyar Democrat a Nebraska a yammacin Juma’a a Omaha: “Biden na cewa, ya san Trump zai kawo wani abin kunya a kasar, amma bai sani ba shin dole ne ya amince cewa akwai wani abin kunya da ya riga ya faru.” Biden yana magana...
3. A Hangen Nesansa wajen jagorancin al’umma, ya mayar da hankali kan masana’antu, sabunta ababen more rayuwa da kuma gina Dan’adam; domin mayar da Jihar Nasarawa matsayin wata babbar cibiyar zuba jari a Nijeriya da horar da aikin injiniya tare da kyautata jin dadin al’ummar jihar; an zabi Injiniya Abdullahi A. Sule a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025. Injiniya Abdullahi Sule: Wanda Ya Fi Yin Fice Kan Harkokin Masana’antu A Duk Fadin Arewa 4. Shugabancinsa ya yi matukar kawo sauye-sauye a Jihar Ekiti, musamman ta hanyar gudanar da mulki na adalci, sabunta ayyukan more rayuwa, karfafa matasa da fadada aikin gona; sakamakon tawali’un da yake da shi da horon da ya samu wajen tafiyar harkokin kudi da gina jama’a tare...
Shugaban kasar Mali Assimi Goita ya yi wa al’ummar kasar jawabi akan karancin man fetur da ake fama da shi a kasar da kuma yadda masu ikirarin Jihari suke killace motocin dakon makamashi. An fara samun kamfar man fetur ne a kasar Mali wacce ba ta da iyaka ruwa, da masu ikirarin jihadi su ka tare kan iyaka da hana tankokin man fetur shiga cikin kasar. Goita ta bayyana cewa: “ A duk lokacin da za a dauko motocin dakon mai, mutane suna mutuwa, ana yin kwanton bauna akan hanya,ana kona motocin da mutane a cikinsu har su kone kurmus.” Goita ya bayyana haka ne a lokacin dake halartar bikin bude wurin hako ma’adanin “Lithium” a yankin Bougouni a kudancin...
Sanata Ali Ndume ya ce jahiltar halin da Najeriya ke ciki ne ya sa Shugaban Amurka Donald Trump ya yi iƙirarin cewa ana kisan Kiristoci a ƙasar. Ndume, wanda ke wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise ranar Talata. Ousmane Dembele zai buga wasan PSG da Bayern Munich ’Yan kwangila sun hana zaman majalisa kan rashin biyan haƙƙoƙinsu Sanatan ya ce maganganun Trump sun nuna rashin cikakken fahimtar yadda matsalar tsaro take da sarƙaƙiya a Najeriya. Ya ce matsalar rashin tsaro a ƙasar ta shafi al’umma baki ɗaya ba tare da la’akari bambancin addini ba, yana mai cewa “mutane daban-daban ne ke...
Da yake kaddamar da shirin, Darakta Janar na IRM, Alhaji Anas Muhammad, ya ce an kirkiro da shirin ne domin karfafa zaman lafiya da hadin kai ta hanyar tallafa wa Musulmai da Kiristoci ta bangaren samar da kiwon lafiya da bayar da tallafin kayan abinci da jari. Ya ce: “Kalubalen lafiya ba sa bambance addini ko kabila, don haka bama bambantawa wajen bayar da tallafin. in sha Allah zamu ci gaba da aiwatar da irin wannan shiri a fadin jihar Kaduna baki daya.” A nasa jawabin, Shugaban hukumar KADCHMA, Malam Abubakar Hassan, ya bayyana cewa wannan hadin gwiwa tana nuna muhimmancin dangantaka tsakanin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu wajen cimma dorewar tsarin inshorar lafiya ga kowa. ...
Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan jawabin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi inda yake zargin kashe kiristoci a Najeriyar. A martanin da ta mayar, ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ta ce lamarin ba haka ba ne. Sanarwar da kakakin ma’aikatar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, ta ce, “duk da cewa Najeriya na godiya da kulawar da kasashen duniya ke ba ta musamman kan batun hakkin dan’adam da hakkin addini, wannan batun na zargin kashe kiristoci a kasar ba haka ba ne. Duk yan Najeriya suna da yancin gudanar da addininsu yadda ya kamata, kuma suna gudanar da ibadarsu ba tare da tsangwama ba.” Inji sanarwar. Shi dai shugaban Amurka Donald Trump Ya ce kiristanci na fuskantar...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025 Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025 Manyan Labarai Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi October 31, 2025
A cewar Salahudeen, Ranar Yaƙi da Cutar Polio ta Duniya muhimmiyar dama ce ta faɗakar da jama’a kan barazanar da cutar shan-inna ke haifarwa ga rayuwar al’umma da tattalin arziki, tare da sake duba nasarori da kalubalen da ake fuskanta. Ya ce haɗin kai tsakanin gwamnatin jihar da kungiyoyin bunkasa lafiya — musamman Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) — ya taimaka matuƙa wajen cimma wannan gagarumar nasara. “Gwamna Dauda Lawal ya ayyana dokar ta-baci a bangaren lafiya, kuma hakan ya zame ginshiqin da ya taimaka wajen samun tallafi, goyon baya da isassun ma’aikata don tabbatar da an kai rigakafi ko’ina,” inji shi. Dekta Salahudeen ya kara da cewa WHO, UNICEF, Chigari, Sultan Foundation da Salina Foundation sun...
Gwamnatin Jihar Gombe ta ƙaddamar da taron sauraron ra’ayoyi jama’a kan shirye-shiryen tsara kasafin kuɗin shekarar 2026 a wani yunƙuri na jaddada ƙudirinta na gudanar da mulki cikin gaskiya da haɗin kai. Da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Gwamnan Jihar, Dakta Manassah Daniel Jatau, ya bayyana cewa wannan mataki na nuna jajircewar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya wajen tabbatar da cewa ra’ayoyin jama’a na taka muhimmiyar rawa a tsara kasafin kuɗi da aiwatar da shi. Za a rataye wanda ya kashe ɗan uwansa a Ekiti Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja Ya ce tattaunawar ta bai wa gwamnati damar haɗa kai da sarakunan gargajiya, mata, matasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki, domin bayar da...
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya rattaba hannu kan sabuwar dokar da ta ƙirƙiri ƙarin ƙananan hukumomi 29 a jihar. Wata takarda da Aminiya ta samu ta nuna cewa Mukaddashin Mataimakin Magatakarda na Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Musa Yerima, ya tura wannan ƙuduri zuwa Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulki, yana neman amincewar Majalisar Tarayya domin tabbatar da dokar a cikin gyaran kundin tsarin mulki da ake yi. Tinubu ya ƙirƙiri sabon harajin da zai iya ƙara N100 a kan kowacce litar man fetur Zargin Kisan Kiristoci: ’Yan majalisar Amurka sun yi amfani da bayanai marasa tushe — Gwamnati A halin yanzu, Jihar Bauchi na da ƙananan hukumomi 20 da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya amince da su. Da...
Kwamitin Haɗin Gwiwa na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai kan gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya, ya amince da buƙatar ƙirƙiro sabbin jihohi guda shida. Wannan mataki na cikin abin da aka cimma a ƙarshen taron kwana biyu da aka gudanar a Legas, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu. Matsalar kashe-kashe a Nijeriya ba ta da alaƙa da addini — Femi Kayode Boko Haram na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare — Zulum A cewar kwamitin, an tattauna kan buƙatu 69, ciki har da buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da kuma ƙananan hukumomi 278. Daga cikin buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da aka gabatar, kwamitin ya amince da ƙirƙirar jihohi...
Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa (NEC) ta amince da shirin Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu na sake fasalin da kuma zamanantar da cibiyoyin horar da jami’an tsaro a faɗin ƙasar. Wannan mataki ya biyo bayan taron majalisar na 152 da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda Ministan Tsare-tsaren Kasafi da Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya gabatar da jawabi kan dabarun cimma burin Shugaban Ƙasa na samar da tattalin arzikin da ya kai darajar dala tiriliyan guda. An kafa kwamitin da Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ke jagoranta don tsara cikakken tsari na gyaran da sabunta cibiyoyin horar da jami’an ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro cikin wata guda. Mambobin kwamitin sun haɗa da gwamnonin jihohin...
Kungiyar gwagwarmyar ta Hamas ta yi maraba da matakin da kotun kasa da kasa ta ICJ ta dauka na karyata ikirarin da HkI ta yi kan hukumar bada agaji ga falsdinawa yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya . Gwamnatin Sahyuniya ta yi ikirarin karya kan hukumar ta UNRWA inda kafafen yada labarai na kasashen turai suka yayata ba tare da wani bincike ba kan gaskiyar lamarin, inda kotun ta ICJ ta majalisar dinkin duniya ta mayar da martani kan ikirarin karya da isra’ila ta yi kuma ta kare hukumar UNRWA ta bayyana irin ayyukan jinkai da take yi da gudanarwa ga alummar falasdinu. Babban kotun duniya ta umarci isra’ila da ta bada dama a shiga da kayayyakin agaji zuwa...
Har ila yau, an kama wasu mutane biyu da ake zargi a kauyen Doka da ke Kachia, kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, yayin da ake zarginsu da safarar bindigogi kirar AK-47 guda uku ga ‘yan bindiga a cikin wata mota kirar Golf. Da yake mayar da martani kan wannan ci gaban, Gwamna Uba Sani ya yabawa hukumar DSS kan nasarar da ta samu, inda ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kawar da miyagun laifuka a fadin jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas October 23, 2025 Manyan Labarai Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki October 22, 2025...
Kasar Iran Ta Kai Hare-Hare A Wuraren Da Kawayen Isra’ila Ba Su San Da Su ba A Lokacin Yakin Kwanaki 12
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai hari kan wasu muhimman wuraren da hatta kawayen haramtacciyar kasar Isra’ila ba su sani ba Tauraron dan Adam na Noor 3 ana daukarsa a matsayin dabara, soja, tauraron dan adam da Iran ta kera wanda ya samu gagarumin ci gaba na bayanai da leken asiri ga sojojin Iran. Masanin tsaro da dabarun yaki Laftanar Janar Abdul Karim Khalaf ya tabbatar da cewa: Tauraron dan adam Noor 3 na Iran yana wakiltar ingantaccen na’ura akan tauraron dan adam na Noor 2, wanda aka kara masa kilo 7 na karin kayan aiki. Tauraron dan Adam na Noor 2 yana da nauyin kilogiram 25, yayin da tauraron Noor 3 ke daukar nauyin kilogiram 32. Abin lura shi...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta yi kira ga Maniyyata Aikin Hajjin 2026 da su biya kafin alkalami nan da ranar 14 ga watan Nuwamban 2025. Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Ibrahim Datti ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba 22 ga watan Oktoban 2025. Hukumar wacce ta ce kudin kama kujerar kar su gaza Naira Miliyan Biyu, ta ce Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON, na kokarin sama wa Maniyyata rangwame bisa kudin kujera da ta sanar a baya. Ta kara da cewa duk wanda bai biya ba kafin karshen wa’adin da ta bayar, ba zai sami kujerar Aikin Hajjin Bana ba. Har ila yau Hukumar ta ce Maniyyata za su...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan October 20, 2025 Daga Birnin Sin Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira October 20, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing October 20, 2025
An gudanar da zanga-zanga a sassa da dama na kasar Amurka, ciki har da manyan birane kamar New York, da Los Angeles, da Washington, da Chicago da sauransu, inda masu zanga-zangar suka rika sukar manufofin shugaba Trump na yaki da bakin haure ta hanyar amfani da karfin tuwo, da tura rundunonin jami’an tsaro zuwa wasu biranen kasar, da kara buga harajin kwastam da sauransu. Masu shirya zanga-zangar sun ce adadin mutanen da suka fito don zanga-zangar ta wannan karo ya zarce miliyoyi. A birnin New York, mutane fiye da dubu 100 sun halarci zanga-zangar a jiya Asabar, ciki har da jagoran jam’iyyar demokrat a majalisar dattijan kasar Chuck Schumer. Masu zanga-zangar kenan a birnin New York na adawa ne da...
Hukumar samar da abinci ta MDD ta bukaci a bude duk wasu hanyoyi domin shigar da abinci a Zirin Gaza, saboda yadda magance matsalar yunwa a Zirin zai dauki lokaci. Kakakin WFP Abeer Etefa ta shaidawa manema labarai a Geneva cewa, za a dauki lokaci kafin a rage yunwa. “Yanayi a Gaza yana da matukar wahala kuma har yanzu muna da nisa daga cimma wannan burin,” in ji ta. A cewar WFP, bukatar gaggawa ta ta’allaka ne ga “bude mashigar kan iyaka guda biyar” zuwa cikin yankin “domin a wadata Gaza da abinci da kuma samar da wuraren rarrabawa cikin gaggawa,”. Shirin WFP, “shi ne kara yawan taimakon da za a kai ga mutane miliyan 1.6 a cikin Gaza cikin...
Makami mai linzami na Iran kirar “Ghadr-H” ya aika da sako mai muni ga gwamnatin mamayar Isra’ila Wani masani kan harkokin tsaro da tsare-tsare Kanar Abdul Karim Khalaf ya bayyana cikakkun bayanai masu inganci da siffofi na musamman na makami mai linzamin na Iran “Ghadr H”, yana mai jaddada cewa; Makamin ya aike da sako mai karfi ga gwamnatin mamayar Isra’ila saboda karfin da take da shi na kutsawa cikin mafi tsauri na tsaron iska da kuma gujewa radar. Khalaf ya bayyana a cikin bayanansa cewa: “Ghadr” ya bambanta da sauran hasken wadda da ba a taba ganin irinsa ba a cikin yaki da kuma karfin da yake da shi na barna saboda fasahar da ke dauke da shin a...
An gudanar da bikin bayar da lambar yabo ta wasan kwallon kafa na Asiya da Futsal na shekarar 2025 a birnin Riyadh na kasar Saudiyya. A bangaren mata kuwa, Marzieh Jafari, shugabar kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Iran, ita ce babbar mai horar da mata, yayin da Salar Aghapour ta lashe kyautar ‘yar wasa mafi nuna kwazo a wasan Futsal a wannan shekara. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran: Kudurin Kwamitin Tsaro Kan Yarjeniyar JCPOA Ya Kawo Karshe A Yau...
Kwamandan Dakarun Sa Kai Na Iran Ya Bayyana Cewa: Iran A Yayin Yaki Da Isra’ila Ta Tarwatsa Wasu Muhimman Wurare 21
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da tarwatsa wasu muhimman wurare 21 na ‘yan sahayoniyya a lokacin yakin 12 Kwamandan Dakarun sa-kai na Basij Birgediya Janar Gholamridha Sulaimani ya bayyana cewa: Tunanin kawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin yakin kwanaki 12 da aka yi, wauta ce ta makiya yahudawan sahayoniyya, wadanda suka gaza a yunkurin da suka yi. Ya jaddada cewa: Iran ta lalata muhimman wurare 21 na ‘yan sahayoniyya da makamanta masu linzami a yakin karshe. Birgediya Janar Gholamreza Soleimani ya bayyana a wurin taron tunawa da shahidai a Isfahan cewa: Makiya sun yi tunanin cewa za su iya kawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran nan da kwanaki 10, kuma sun yi niyyar haifar da hargitsi da...
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta fara aiki kan dokar da za ta kafa wuraren tsaro (safe spaces) a makarantu domin karfafa ilimin yara mata a jihar. Shugaban Kwamitin Ilimi, Honarabul Mahmud Lawal, ya bayyana hakan a babban taro kan Ilimin Yara Mata da aka gudanar a Zariya, wanda Cibiyar Kula da Ilimin Yara Mata (CGE) ta shirya don tunawa da Ranar Yara Mata ta Duniya ta 2025. Ya ce dokar, mai taken “Dokar Wuraren Tsaro a Jihar Kaduna, 2025,” za ta kare ‘yan mata daga cin zarafi, hana wariya, da samar da tsarin horaswa da rahoto a makarantu. Daraktar CGE, Hajiya Habiba Mohammed, ta ce taron na da nufin kara karfafa ‘yan mata a matsayin shugabannin da za su...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta samu nasarar gano wasu motoci da aka sace tare da kama wasu da ake zargin ɓarayi ne masu aikata laifuka ciki har da ƙwace bindiga ƙirar gida. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a madadin Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Bello Yahaya, inda ya ce nasarorin sun biyo bayan sintiri da sahihan bayanan leƙen asiri da haɗin gwiwar al’umma. Miyetti Allah ta dakatar da shugabanninta a jihohi 3 An ceto mutane 3 da aka yi garkuwa da kama wasu a Bauchi A cewar sanarwar, a ranar 13 ga Oktoba, 2025, jami’an sashin Balanga sun gano wata mota ƙirar Toyota Jeep...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wasika daga daukacin malamai da daliban jami’ar nazarin aikin gona ta kasar Sin, inda ya taya dukkan malamai da dalibai da ma’aikatan jami’ar, da kuma wadanda suka kammala karatu a jami’ar murnar cika shekaru 120 da kafuwar jami’ar. Xi ya yi fatan jami’ar za ta ci gaba da tafiyar da harkokinta yadda ya kamata, da kudurce aniyar inganta aikin gona don amfanin kasa, da kuma zurfafa yin gyare-gyare kan hanyoyin koyarwa da ilmantarwa, da kara kokarin bincike, da kirkire-kirkire a fannin aikin gona, da kuma amfani da sakamakon binciken yadda ya kamata, ta yadda za a kai ga horar da karin kwararrun masana a fannin aikin gona, don ba da sabuwar gudummawa ga...
Hukumar Kula Da GIdajen Gyaran Hali A Zamfara Ta Neman Shigarda Fursunoni Tsarin Inshorar Lafiya Na NHIS
Kwanturola na hukumar gyaran Hali a Najeriya reshen jihar Zamfara, Murtala Muhammad Haruna, ya yi kira da a shigar da fursunoni cikin tsarin inshorar lafiya na kasa (NHIS) domin tabbatar da samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya. Ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga kwamishiniyar lafiya ta jihar Zamfara, Dakta Nafisa Muhammad Maradun, a ofishinta da ke Gusau. Haruna ya ce shirin ya yi dai-dai da hangen nesan babban kwamandan hukumar gyaran hali ta Najeriya da nufin inganta jin dadin fursunonin da ke gidajen yari. Kwantirolan ya kuma jaddada bukatar inganta asibitin hukumar da ke cibiyar tsaro ta matsakaita, Gusau, da samar da isassun kayan aikin likita da magunguna masu mahimmanci...
Hukumar kula da gidaje ta jihar Kano ta fara wani gagarumin aikin tsaftar muhalli kashi na biyu a birnin Kwankwasiyya, inda ta kara azama wajen gina tsaftataccen muhalli, lafiya da kuma dorewar muhalli a birane. Da yake jawabi yayin aikin, mukaddashin Manajan Daraktan Kamfanin, Engr. Isyaku Umar Kwa, ya bayyana cewa kashi na biyu ya mayar da hankali ne kan inganta harkar sharar gida, da inganta tsarin tattara shara, da kuma kawata wuraren jama’a a fadin birnin na Kwankwasiyya. A cewarsa, aikin na da nufin tabbatar da tsaftar tituna, wuraren shakatawa, da wuraren jama’a tare da inganta alkinta muhalli. Engr. Kwa ya bayyana cewa an tsara wannan shiri ne domin karfafawa mazauna garuruwan Kwankwasiyya da Bandirawo da...
Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya
An tallafawa ‘yan Kasuwa ƙanana, kuma an rage fitar da hayakin da ke gurɓata muhalli a faɗin nahiyar Afirka. Gwamna Uba Sani ya bayyana wannan nasara a matsayin babbar gagarumar bajinta da kuma abin alfahari ga Jihar Kaduna da NIjeriya baki ɗaya, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a fannin kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire domin bunƙasa tattalin arziki da bai wa matasa dama. “Wannan nasara ta sake tabbatar da ƙwarewar ƙirƙira da ƙarfin tunanin matasan Jihar Kaduna. Muna gina tattalin arzikin da ke dogaro da kirkira wanda ke daraja ra’ayi tare da haɓaka baiwa” in ji Gwamna Uba Sani. “Daga ajujuwa zuwa manyan matakan duniya, matasan Kaduna suna jagorantar makomar...
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da ’yan ta’adda ba waɗanda ke kashe mutane ba gaira ba dalili. Gwamnan, ya bayyana hakan ne a yau a wajen bikin yaye sabbin jami’an tsaron cikin gida (Community Watch Corps – CWC) guda 100, a karo na uku da aka gudanar a Katsina. Gwamna Buni ya ware N5.8bn don biyan haƙƙin tsoffin ma’aikata a Yobe Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan Radda, ya karyata rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai suka yada cewa gwamnatinsa tana tattaunawa da ’yan bindigar da ke ɓoye a dazuka. A cewarsa: “Babu wata tattaunawa ko sasanci da gwamnati ke yi da ’yan ta’adda....
Shugaban Kasar Columbia Ya Soki Donald Trump Akan Bai Wa Isra’ila Makamai Shugaban na kasar Columbia Gustavo Petro ya ce, Bugun kirjin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na bai wa “Isra’ila” makamai tare da cewa ta yi amfani da su da kyau, ba wani abu ne da ya cancanci a yi masa tafi, sunan shi tarayya a aikata laifi. Shugaba Gustavo Petro yana mayar da martani ne akan zancen da shugaban kasar Amurka ya yi a Majalisar “Knesset’ ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila ya ce; Isra’ilan ta yi amfani da makaman da ya ba ta da kyau. Shugaba Gustavo ya kara da cewa; wadannan makaman na Amurka sun kashe mutane 70,000 sannan kuma sun jikkata wasu 200,000....
Babbar Kotun Jihar Kano a ranar Talata ta bayar da umarnin aikewa da Ogugua Christopher zuwa gidan gayarn hali bisa zarginsa da hannu a sata da kuma safarar yara daga jihar Kano zuwa kudancin Najeriya. Ana dai zargin mutumin ne da mallakar wani gidan marayu a jihar Delta ba bisa ka’ida ba, sannan yana amfani da shi wajen ajiye yaran da ake zargin na sata ne a ciki. Majalisa ta gayyaci CBN da bankunan kasuwanci kan yawan cire wa kwastomomi kuɗaɗe DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Hukumar Hana Fatucin Mutane ta Kasa (NAPTIP) ce dai da gurfanar da Christopher tare da wasu abokar harkallarsa su biyu, Hauwa Abubakar da Nkechi Odlyne, wadanda su ba su...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya October 14, 2025 Daga Birnin Sin Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata October 14, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique October 14, 2025
Majalisar Wakilai ta gayyaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da bankunan kasuwanci domin amsa tambayoyi kan yadda suke cirar cajin kudade barkatai daga asusun masu ajiya. Majalisar ta gayyace su ne bayan kudurin da Honorabul Tolani Shagaya ya gabatar kan abin da ta kira ‘cirar cajin kudade barkatai babu bayani ba,’ da bankuna suke yi daga asusun masu ajiya, sabanin dokokin CBN. Honorabul Shagaya ya ce kodayake bankuna da gudanar da hidima ne da ake biya, amma yawancin ’yan Najeriya suna kuka kan yadda suke yawan ciyar kudade — kamar na tura sakon tses, kula da katin ajiya, kula da asusun ajiya, tura kudi, hrajin kan sarki da wasu da ba su san da ake fiye da sau daya. Ya ce...
A matsayin birnin dake karbar bakuncin taron, Dunhuang mazauni ne ga wurare 3 dake cikin jerin wuraren gargajiya na hukumar UNESCO da kuma wuraren kayayyakin gargajiya sama da 260, wanda kuma ke nuna hadaddun dabarun da aka dauka a shekarun baya-bayan nan da nufin kare al’adun gargajiya yayin da ake bunkasa birnin. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Barazanar Amurka Ta Kara Haraji Game Da Batun Ma’adanan Farin Karfe Ba Hanya Ce Mai Bullewa Ba October 13, 2025 Daga Birnin Sin Hada-Hadar Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso 4% Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana October 13, 2025 Daga Birnin Sin Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin...
An bayyana katin zabe a matsayin sheda da za a iya amfani da shi a muhimman wurare, kamar yadda ake amfani da fasfo da katin dan kasa a manyan kasashen duniya. Tsohon wakilin mazabar tarayya ta Birnin Kudu da Buji, Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yi wannan tsokaci new a wata tattaunawa da manema labarai a Dutse. Ya bayyana bukatar aiki tukuru a tsakanin masu ruwa da tsaki dan tabbatar da cewar dukkan wadanda su ka cancanta sun karbi katin zaben. Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yabawa gwamnatin Malam Umar Namadi bisa kafa kwamati na musamman a karkashin mai bada shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Lawan Garba Bullet, domin zaburar da kananan hukumomi su bada gudummawar da za ta taimaka...
Shugaban kasar Amurka ya yi barazana ga shugaban kasar Rasha na aike wa Ukraine makamai masu linzami kirar Tomahawk Shugaban Amurka Donald Trump ya ce: Zai gargadi takwaransa na Rasha Vladimir Putin cewa: Akwai yiwuwar Ukraine za ta iya samun makamai masu linzami kirar “Tomahawk” idan Rasha ba ta kawo karshen yakin Ukraine ba. Da aka tambaye shi a cikin jirgin Air Force One da ke kan hanyarsa ta zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila da Masar da yammacin ranar Lahadi ko shi da kansa zai tattauna da Putin kan batun, Trump ya ce, “Yana iya magana da shi. Yana cewa: Idan ba a warware wannan yakin ba, zai aika wa Ukraine da makamai masu linzami na Tomahawk.” Trump ya kara da...
Wata kungiya mai zaman kanta ta tantance mutane 60 wadanda za’a yiwa aikin ido kyauta a wasu kananan hukumomi 2 dake jihar Jigawa. Shugaban kungiyar mai zaman kanta, Alhaji Umar Saidu Yelleman Jambola ya bayyana cewar za’a gudanar da aikin ne kyauta ga mutane 60 a kananan hukumomin Malam madori da kaugama. A cewar sa wadanda za su ci moriyar aikin an zabi su ne daga dukkanin mazabu da ke kananan hukumomin. Sa’idu Yalleman ya kara da cewa yara da manya ne za su amfana da aikin idon kyauta wanda kungiyar ta dau nauyi. Da yake jawabi ga manema labarai, Dr Abubakar Adamu yace wadanda aka tantance kuma suke da yanar ido za’a kai su asibitin...
Wadanda suka amfana da horon, an ba su horon ne a fannoni daban-daban da suka hada da yin noma da takin gargajiya da kuma yin noman kayan lambu da sauransu. Kajin gidan gona da tare da kuma tallafa masu da kayan aikin noma. Bisa tsarin wannan haron, kowace mace daya da ta amfana da horon, an ba su tallafin Naira Naira 50,000. Kazalika, Adeleke ya danganta wannan tallafin kudin a matsayin mayar da hankalin gwamnatinsa na taimaka wa matan jihar. Gwamnan ya kuma jaddada muhimmcin tallafa wa mata, wanda ya sanar da cewa; hakan na da muhimanci domin inganta gobensu. Shi kuma shugaban gidauniyar, Dakta Deji Adeleke a nasa jawabin ya bayyana cewa, shirin wanda...
Uche Nnaji, Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, ya yi murabus daga mukaminsa. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Talata. Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Jerin ministocin da zargin takardun bogi ya tabaibaye su Nnaji na fuskantar zarge-zarge kan sahihancin takardun karatunsa, inda binciken da jaridar Premium Times ta gudanar ya gano cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ta ce ba ta ba shi takardar kammala digiri ba. A cewar jami’ar, tsohon Ministan bai kammala karatunsa a cikinta ba, kuma ba ta taɓa ba shi takardar shaidar kammala ta ba. A cewar jaridar, Simon U. Ortuanya, Shugaban Jami’ar UNN, ya...
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu
A cewarsa, gyaran yana taimakawa wajen samun bayanai daidai domin tsara ci gaba da kuma rarraba albarkatun ƙasa bisa adalci daga gwamnatin tarayya.“Wannan tsarin yana daidai da yadda ake yi a wasu jihohi, inda ake amfani da bayanan masarautu, yankuna da ƙauyuka wajen tsara ci gaba da rarraba kuɗaɗe,” in ji shi.Gwamnan ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen haɗa kan jama’a da tallafa wa ayyukan ci gaba, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da sabon tsarin cikin gaskiya.Ya yaba wa kwamitin bisa jajircewarsu da yadda suka gudanar da aikin cikin gaskiya da tsari.Tun da farko, shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya bayyana cewa sun karɓi buƙatu 196, wanda 17 don kafa sabbin masarautu, 166 don sabbin yankuna, da...
Kwamitin da Gwamnatin Jihar Bauchi ta kafa domin nazarin buƙatun ƙirƙirar sababbin masarautu da yankunan hakimai da dagattai, ya ba da shawarar ƙirƙirar masarautu 13, da hakimai 2 da dagattai 113 a fadin jihar. Wannan shawara na kunshe ne a cikin rahoton da shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya miƙa wa Gwamna Bala Mohammed a ofishinsa da ke Bauchi. Da yake miƙa rahoton, Akuyam ya bayyana cewa masarautu 13 da yankunan hakimai biyu da aka bayar da shawarar kafa su su ne suka cancanta daga cikin sama da buƙatu 100 da aka karɓa daga sassan jihar daban-daban. Kwamitin, an kaddamar da shi ne a ranar 4 ga Yuli 2025, da umarnin ya duba buƙatun al’ummomi, ya tantance dalilan tarihi, al’ada da...
Sojojin HKI sun bada sanarwan cewa zasu fara shirin aiwatar da shirin shugaban Trump na tsagaita buduewa juna wuta a Gaza. Da kuma batun musayar fursinoni gaba daya da kungiyar Hamas. Shafin yanar gizo na labarai Arab News na kasar Saudia ya bayyana cewa a jiya da yamma ne kungiyar Hamas ta bayyana cewa ta amince da tsagaita wuta tsakaninta da HKI wanda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya gabatar. Kungiyar ta bayyana cewa ta amince da wasu sassa na yarjeniyar amma sai an tattauna kan wasu. Wata majiyar sojojin yahudawan ta bayyana cewa shuwagabannin kasar sun basu umrnin dakatar da kai hare- hare kan falasdinawa a Gaza. Wannan sanarwan ta zo sa’o’ii kadan bayan da shugaban Amurka ya umurci...
Burgediya JanarEsma’il Qa’ani babban kwamnadan dakarun “Qudus'” IRGC a nan Iran ya bayyana cewa kungiyar Hamas ta boye ranar fara yakin tufanul Aksa har shugaban kungiyar Shahid Isma’il Haniyya da shahida Nasarallah duk basu san da lokaci fara yakin ba, sai suka ji an fara. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Qa’ani yana fadar haka, a jiya jumm’a a hirar da aka yi da shi a tashar talabijin ta cikin gida a nan Iran. Ya kumakara da cewa a lokacinda aka fara yakin shugaban kungiyar ta Hamas yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Iraki, yana dawowa ne ya ji labarin fara shi. Janar Qa’ani ya kara da cewa, amma duk da haka, shahida Nasarallah ya zauna...
Hukumar sararin samaniya ta kasar Iran ta bada sanarwan shirin cilla tauraron dan’adam a cibiyar cilla taurarin dan’adam na Chabahar tare da amfani da sandarerren makamashi. Kamfanin ndillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban hukumar Hassan Salarieh yana fadar haka a yau Asabar ya kuma kara da cewa, an kammala bangare na farko na cibiyar cilla taurarin yan’adam na Chabahar kuma hukumar ta fara shirin amfani da sandarerren makamashi don cillan taurarin yan’adam da suke gabanta, wadanda a shirye suke a cillasu. Salarieh y ace a halin yanzu akwai tauraron dan Adam mai suna Pars-2 da ke jiran cillawa, sannan hukumar zata ci gaba da aiki a bangare na 2 na cibiyar don kammala aikin cibiyar cilla tararin...
Shugaban cibiyar fasaha da kere-kere ta Pardis a nan Tehran ya bada sanarwan cewa, wakilai daga kasashe 65 ne suka bayyana anniyarsu ta halattan gasar fasahar kere-kere ta shekara ta 2025 a cibiyarsa. Kamfanin dilancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Mehdi Saffaari –Nio yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa gasar ta dai-dai kun mutane, wadanda zasu gwada korewarsu da kuma fasahar da suke da ita a gasar wacce za’a gudanar daga ranar 27-30 ga watan Octoba damukeciki a nan Tehran. A taron yan jaridun da ya kira don bada wannan sanarwan Mehdi Safaari-nio ya ce mafi yawan mahallata gasar matasa ne musamman daliban makarantu wadanda suke son gwada korewarsu da kumailminsu. Kuma a...
Shugaban kasar Madagaska Andry Rajoelina ya sanar da korar daukacin mambobin gwamnatinsa biyo bayan mummunar zanga-zangar da aka shafe kwanaki ana yi a kasar. A wani jawabi da ya yi na tsawon mintuna 17, ranar Litini, , Andry Rajoelina ya sanar da cewa ya ji kiran matasa tare da korar firaministansa da gwamnatinsa. Ya fara jawabinsane da jajanta wa wadanda suka rasa yan uwa da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata. Da yake jawabi ga matasan da suka fusata, ya bayyana cewa: “Na saurari muryoyinku, da bukatunku, Kuma ina ba da hakuri idan akwai mambobin gwamnati da ba su yi aikin da mutane suke tsammani […].” Shugaban ya bayyana a gidan talabijin na kasar cewa, “A bisa...
Ya bayyana cewa, bin wannan ƙa’idojin yana da matukar muhimmanci domin bai wa hukumar damar tattara sahihin jerin sunayen maniyyata da kuma tura dukkan kuɗaɗen zuwa ga hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) a kan lokaci. Ya shawarci maniyyatan da suka kammala biyan kudadensu da su miƙa takardunsu na tafiya cikin gaggawa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Xi Ya Yi Kira Ga Makarantun Horar Da ‘Yan Jam’iyya Da Su Kara Azamar Kyankyashe Hazikai Da Gabatar Da Shawarwari Ga JKS
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga makarantun horar da ‘yan jam’iyya da su taka rawar gani wajen kyankyashe hazikai, tare da gabatar da shawarwari ga JKS. Xi, wanda shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kiran ne cikin wani umarni da ya gabatar ga makarantun koyar da jagoranci na ‘ya’yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙungiyar Ma’aikata Masu Aikin Mai da Gas ta Najeriya (PENGASSAN), ta fara yajin aiki saboda korar wasu ma’aikata a Matatar Mai ta Dangote da ke Jihar Legas. Sakataren ƙungiyar, Lumumba Okugbawa, ya ce sun fara yajin aikin ne daga ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025. Jami’ar Bayero ta sallami ɗalibai 57 kan maguɗin jarrabawa ‘Yan fashi sun sace mutum 17 a mahadar tekun Akwa Ibom da Kuros Riba Da misalin ƙarfe 6 na safe, mambobin ƙungiyar da ke aiki a ɗakunan kula da na’urori suka daina aiki. Umarnin ya shafi mambobin da ke ofisoshi, kamfanoni, da hukumomin gwamnati a faɗin Najeriya, waɗanda za su daina aiki da misalin ƙarfe 12:01 na daren ranar Litinin, 29 ga watan Satumba. Okugbawa,...
Rahotanni da suke fitowa daga Jahar Zamfara a arewacin Nigeria sun ce, mutanen da sun karaci 100 ake fargabar mutuwarsu saboda ruftawar ramin hako ma’adanai. Shedun ganin ido sun fada wa kamfanin dillancin labarun “Reuters” cewa; ramin hako ma’adanan wanda yake a yankin Kaduri dake karamar hukumar Maru ya fada akan ma’aikatan dake ciki. Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, an kuma ci gaba da aikin ceto na fito da mutanen har zuwa jiya juma’a. Wani mazaunin yankin ya ce, an ceto da mutane 13 daga karkashin baraguzai, ana kuma jin cewa da akwai wasu mutane fiye da 100 da suke karkashin kasa. Wani shaidar ganin ido kuwa cewa ya yi, a tsakanin mutanen da sun kai 100 da...
Gwamnatin Jihar Kano ta miƙa ƙorafe-ƙorafen da aka yi a kan Malam Shu’aibu Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph, ga Kwamitin Shura na Jihar don ɗaukar matakin da ya dace. Sakataren Gwamnatin Jihar ne, ya tura ƙorafe-ƙorafen a ranar Juma’a, inda kwamitin ya fara zama domin sauraronsu. ’Yan Najeriya da tauraronsu ya haska a Ballon d’Or Yadda ’yan haya za su samu ragin N500,000 a shekara A cewar kwamitin, za a gayyaci masu ƙorafi da Malam Triump domin su gabatar da hujjoji. Masu ƙorafi za su fayyace abubuwan da suke tuhumar malamin, yayin da shi kuma za a ba shi damar kare kansa. Bayan haka kwamitin zai tattauna bisa ƙa’idojin shari’ar Musulunci. Sakataren kwamitin, Shehu Wada Sagagi, ya shaida...
A ranar Litinin aka gudanar da bikin bayar da kyautar Ballon d’Or a Birnin Paris, inda ake karrama fitattun ’yan ƙwallon duniya. A bana, Ousmane Dembele na Ƙasar Faransa da PSG ne, ya lashe kyautar maza, yayin da Aitana Bonmati ta Spaniya ta lashe ta mata karo na uku a jere. An gano yarinya da aka sayar ₦3.7m a Ondo Naɗin Olubadan: Tinubu da manyan jami’ai sun ziyarci Ibadan Abin farin ciki ga Najeriya shi ne, mai tsaron ragar Super Falcons, Chiamaka Nnadozie, ta zo ta huɗu a jerin mata, wanda shi ne matsayi mafi girma da wata ’yar Najeriya ta taɓa samu. Ga jerin ’yan Najeriya da suka taɓa shiga cikin jerin waɗanda suka fafata neman kyautar Ballon d’Or:...
Magajin garin Landan ya caccaki shugaban Amurka Trump, yana mai cewa shi mai nuna wariyar al’umma ce tare da kyamar musulmi Magajin garin Landan Sadiq Khan ya bayyana shugaban Amurka Donald Trump a matsayin “mai nuna wariyar al’umma kuma mai kyamar musulmi,” bayan da Trump ya zarge shi da neman aiwatar da shari’ar Musulunci a babban birnin Birtaniya. Khan ya shaida wa tashar Sky News cewa: “Yana ganin Trump a matsayin mai nuna wariyar al’umma, mai dabi’ar bunsuro, mai son zuciya, kuma mai kyamar musulmi.” Ya yi nuni da cewa, Landan ce ta farko a cikin alamomi da dama, kamar zuba hannun jari na kasashen waje, ya kuma jaddada cewa “yana matukar alfahari da cewa Landan ce birni mafi girma...
Ya ce zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya zai tabbata ne kawai idan aka tabbatar da adalci. Shugaban ya jaddada irin gyare-gyaren tattalin arziƙin Nijeriya, ciki har da cire tallafin man fetur da sauya dokokin musayar kuɗi. Ya ce matakan suna da tsauri, amma dole ne a ɗauke su domin samar da ci gaba mai ɗorewa. A kan tsaro, Tinubu ya ce yaƙin da ta’addanci ba wai da bindiga kaɗai ake cin nasara ba, sai da ra’ayoyi da ɗabi’u waɗanda ke haɗa al’umma. Ya kuma jaddada aniyar Nijeriya ga zaman lafiya, ci gaba, da kare haƙƙin ɗan Adam, inda ya yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta yi canje-canjen da za a iya gani, tare da gargaɗin cewa idan...
Za a fara samar da sabon maganin riga-kafin kare mutum daga kamuwa da cutar HIV, a ƙasashe masu ƙaramin karfi, a kan farashi mai rahusa daga shekarar 2027. Maganin allura mai suna lenacapavi wanda a ƙasashen da suka ci gaba ake sayarwa da dubban daloli a duk shekara, zai koma dala 40 kacal a kowace shekara. Wannan sabuwar hanyar riga-kafin za ta bai wa miliyoyin mutane damar ci gaba da rayuwa da kuma kauce wa haɗarin kamuwa da cutar HIV. Za a riƙa samar da maganin mai rahusa a Indiya, sannan kuma za a watsa shi a duniya ta hannun gamayyar wasu ƙungiyoyin kiwon lafiya a ƙasashe guda 120.
A ƙarshe, Shugaban ya ce matakan da gwamnati ta ɗauka kamar cire tallafin mai da sauya tsarin kuɗi, duk duk sanya shan wahala amma wajibi ne domin tabbatar da cigaba. Ya jaddada cewa Nijeriya za ta ci gaba da kare haƙƙin ɗan Adam, da haɗin kai da zaman lafiya, inda ya gargaɗi duniya da cewa babu wanda zai tsira sai idan duk mun tsira tare. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Akalla yara miliyan 4.8 ne ake shirin yi wa allurar rigakafin cutar kyanda da cutar shan inna a jihar Katsina a wani bangare na shirin allurar riga-kafi da aka shirya yi a wata mai zuwa. Shugabar ofishin kula da kananan yara ta UNICEF, Rahama Farah, ce ta sanar da hakan a wani taron tattaunawa da wayar da kan masu ruwa da tsaki a shafukan sada zumunta da aka gudanar a Katsina a wani bangare na shirye-shiryen rigakafin da ke tafe. Ya bayyana cewa za a yi allurar rigakafin cutar kyanda ga yara ‘yan tsakanin watanni 9 zuwa 14 yayin da za a yi allurar rigakafin cutar shan inna ga yara ‘yan kasa da shekaru biyar. Mista Farah...
A lokacin hatsarin karfen sauya hanyar ya karye gaba daya, wanda ya haifar da hatsarin. Hukumar ta kuma gano cewa duk da cewa direbobin jirgin ƙwararru ne, ba a ba su sabon horo ba. An kuma gano cewa wasu muhimman kayan aiki kamar na’urar CCTV, na’urar sadarwa da agogo sun samu matsala. NSIB ta shawarci NRC da ta gyara dukkanin kayan da suka lalace, ta sanya sabbin karafan sauya hanya, sannan ta riƙa horar da ma’aikata akai-akai don gujewa irin wannan matsala. A lokacin hatsarin, mutane 21 ne suka ji rauni daga cikin fasinjoji 618 da ke cikin jirgin, amma babu wanda ya rasu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta gabata, inda take zaune tare da mahaifinta, Mohammed Umar, da matarsa. CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100 Mahara sun kashe ɗan sanda sun ɗauke bindigarsa a Taraba Wani mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama a garin, Kabiru Abdulkadir, ya bayyana cewa sai bayan kwana biyar da ƙonewar ta faru ne al’amarin ya bayyana. “Don guje wa matsala, mahaifin yarinyar ya sayi wata...
Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta gabata, inda take zaune tare da mahaifinta, Mohammed Umar, da matarsa. CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100 Mahara sun kashe ɗan sanda sun ɗauke bindigarsa a Taraba Wani mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama a garin, Kabiru Abdulkadir, ya bayyana cewa sai bayan kwana biyar da ƙonewar ta faru ne al’amarin ya bayyana. “Don guje wa matsala, mahaifin yarinyar ya sayi wata...
Aƙalla mutum ne sun rasu, yayin da wasu 16 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a Ƙaramar Hukumar Karasuwa, a Jihar Yobe. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkareem ne, ya tabbatar da faruwar hatsarin ya faru a ranar Asabar da misalin ƙarfe 2:50 na rana a ƙauyen Zangon Kanwa. Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a Enugu Hatsarin ya rutsa da mota ƙirar Toyota Hiace wadda ke ɗauke da fasinjoji daga Jakusko zuwa kasuwar Jajimaji da kuma mota ƙirar Volvo daga garin Azare. Rahoto ya nuna cewa mota ƙirar bas ce ta ƙwace ta buga wani Keke Napep...
Wata mata mazauniyar garin Magama Gumau a Ƙaramar Hukumar Toro, Jihar Bauchi, ta shiga hannun ’yan sanda biyo bayan ƙona al’aurar ’yarta mai shekaru 10 kacal a duniya, kan zargin maita. Rahotanni sun nuna cewa matar ta yi amfani da cokali ta hanyar sanya shi a wuta ya yi zafi sannan ta umarci ’ya’yanta biyu suka riƙe yarinyar sannan ta ƙona ta. Janye Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya koma Ribas ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe Wannan ya jefa yarinyar cikin mawuyacin hali, inda ta ke fama wahalar yin fitsari da bayan gida. Bayan lamarin ya faru, maƙwabta sun kai ƙarar matar wajen ’yan sanda. An garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa...
Rundunar ƴansanda a Jihar Bauchi ta tabbatar da kama wata mata, wadda ake zargi da yi wa wata yarinya ‘yar shekara bakwai mummunan rauni ta hanyar ƙona mata al’aura da wuka mai zafi a garin Magama Gumau, ƙaramar hukumar Toro. Rahotanni sun ce matar ta zargi yarinyar da maita, lamarin da ya sa ta yi amfani da wuka da aka zafafata a wuta wajen ƙona jikinta. Ihun yarinyar ne ya jawo hankalin maƙwabta, inda suka yi gaggawar zuwa suka ceceta tare da sanar da ‘yansanda. Gwamnan Bauchi Ya Gargaɗi Magoya Bayan Wike A PDP An Cafke Mutum Hudu Bayan ‘Yan Fashi 20 Sun Afka Wasu Gidaje A Bauchi Wani mai fafutukar kare haƙƙin yara a yankin, Kabiru Mohammed Abdulkadir, ya...
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Yamen sun kaddamar da hare-hare guda 3 da gagarumar nasara a wasu mihimman wurare a HKI, da zimmar mayar da martani kan hare haren da Isra’ilan take kai mata, saboda ci gaba da nuna goyon bayan alummar falasdinu da take yi da ta kwashe shekaru biyu ta na yi musu kissan gilla, Acikin wani bayani da kakakin sojin kasar Yamen Yahya Saree ya fitar ya sanar cewa kasarsa ta kaddamar da hare hare a muhimman wuraren guda 3 a Yaffa da HKI ta mamaye , kuma ta yi amfani da makami na haypersoni balisstic missile da ta basu suna da falasdinu na 2. Haka zakila ta kai hari a yankin umm Rashrash wato...
HKI ta kai hare-hare kan wurare 5 a kudancin kasar Lebanon a jiya Alhamis. Tashar talabijin Al-mayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa kafin hare-haren yahudawan sun bada sanarwan cewa zasu kai hare-hare kan warare uku a gudancin kasar ta Lebanon a jiya Alhamis kuma sune Meis al-Jabal, Debbine, da kuma Kafar Tebnit. Mai aikawa tashar talabijin ta kasar Lebanon rahoto daga kudancin kasar ta bayyana, amma a lokacinda ta fara kai hare-hare jiragen yakin da ake sarrafawa daga nesa, suka fara shawagi a kan wadan nan wurare, suna ayyukan leken asiri. Sannan bayana wani lokacin makaman Drones suka ketasararin samaniya kasar Lebanon suka kai hare-hare har guda biyu a kan garin Meisal-Jabal, inda ya jiyamutum guda rauni. Yar rahoton...
Ƙasar Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan wani ƙudurin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ke neman a dakatar da yaki a Gaza nan take kuma ba tare da sharaɗi ba. Daftarin kudurin na majalisar ya kuma buƙaci Isra’ila ta cire duk wani takunkumi kan kai agaji ga yankin na Falasɗinawa. Wani ya sace munduwar Fir’auna a gidan tarihin Masar Kasar Albania ta nada mutum-mutumi a matsayin minista Kudurin, wanda ƙasashe 10 da aka zaɓa daga cikin mambobi 15 na majalisar suka tsara, ya kuma buƙaci a saki dukkan fursunonin aka yi garkuwa da su daga hannun Hamas da sauran kungiyoyi ba tare da sharadi ba, cikin mutunci da girmamawa. Kudurin dai ya samu goyon bayan ƙasashe 14, sai dai...
A ƙoƙarinta na ƙara wayar da kan jama’a game da harkokin lafiya a birane da karkara na Malam Madori, majalisar ƙaramar hukumar ta horar da mata da ‘yan mata 50 kan tsafta a lokutan al’ada domin kare kansu daga cututtukan mahaifa. Jami’in shirin, Malam Ali Haruna, ya ce an zaɓi mahalarta horon ne daga kowace gunduma ta yankin A cewarsa, manufar horon ita ce koyar da mahalarta yadda za su samar da kariya yayin al’ada da kansu domin rage kashe kuɗi da kuma kare kansu daga kamuwa da cututtukan mahaifa. Shi ma shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Shehu Sani Gwadayi, ya bayyana cewa tsafta na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar ɗan adam domin inganta rayuwa da ƙarfafa...
Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam ” Nahid 2″ Da Zai Samar Wa Yankunan Karkara Hanyar Sadarwa Ta “Internet”
Ministan sadarwa na Iran Sitar Hashimi ya bayyana cewa, an sami nasara a gwajin da aka yi na sabon tauraron dan’adam, mai suna “Nahid 2” wnada aikinsa shi ne samar da hanyoyin sanarwa na internet masu nagarta. Ministan sadarwar ya kuma ce dukkanin bangarorin tauraron dan’adam din sun yi aiki yadda ake so a yayin gwajin da hakan yake a matsayin wani ci gaba a fagen sadarwa a Iran. Har ila yau ministan Sadarwar Sitar Hashimi ya kuma ce; A tsakanin kauyuka 10,000 da ba su da hanyoyin sadarwa, yanzu an rage su da 2000, kuma ana ci gaba da aiki tukuru domin isa ga kauyunan da suke nesa,masu wahalar zuwa. Ministan sadarwar na Iran ya kuma kara da cewa;...
Jaragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa wato Drones sun fada kan wurare masu muhimmanci a kudancin kasar Falasdinu da aka mamaye, yan sa’o’in da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Janar Yahyah Saree yana fadar haka a dazo-dazon nan .Ya kumakara da cewa. hare-haren sun hada da Drons guda 4, 3 daga cikinsu sun fada kan tashar jiragen sama na Ramon da ke kusa da Ummu Rash-rash ko Ilat kamar yaddayahudawan suke kiransa. Sannan guda kumaya fada kan sansanin sojojin HKI na Negev duk a kudancin kasar. Ya ce an kai hare-haren ne don goyon bayan Falasdinawa wadanda HKI take kashewa tunkimani shekaru biyu da suka gabata. Sannan sanarwan...
Hukumar kare hakkin bil’adama ta “Human Right Watch” ta fitar da wani rahoto da a cikin ta bayyana cewa; kungiyar nan mai ikirarin jihadi a kasar Burkina Faso, ( Jama’at Nusratul-Islam wal Muslimin) da kuma kungiyar Daular Musulunci a cikin yankin Sahara, sun kashe fararen hula 50 daga watan Mayu zuwa yanzu. Rahoton ya ci gaba da yin bayanin cewa, a cikin Ogusta kungiyoyin na masu riya cewa suna yin jihadi sun kashe mutane 40 a cikin garuruwan Djibo da Youba. Rahoton ya kuma ce; a watan Yuli kuwa kungiyar IS ta kai wa fararen hula hari da suke kan hanyar kai kayan agaji zuwa garin Gorom-Gorom da aka killace da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 9. Kungiyar kare...
A cewar sanarwar, bisa wannan sanarwar, fadar ta shugaban ƙasa, ta yanke duk wata huɗɗa da Umunubo. Sanawar ta kuma jaadda cewa, ya zama wajbi ɗaukacin masana’antun da ke a ƙasar nan, su nesanta kansu, da yin dukka wata huɗɗa da Umunubo da sunanan gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu. Idan za a iya tunawa, Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa, fadar shugaban ƙasa, ba ta fitar da wata ƙwaƙwarar sanarwa, kan maƙasudin soke takardar ɗaukar aikin da aka yiwa Umunubo ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
ADC ta ce, “APC tana tsoron ƙaruwar shaharar ADC a faɗin ƙasar nan ne, kuma yana bayyana cewa shi ne kawai hanyar da za su iya bi wajen tarwatsa ƴan adawa a ƙasar nan. “An fara ne a Jihar Edo da gargaɗin shugabannin ADC kan ka da su ziyarci jihar, sannan Kogi ta biyo baya, tare da rufe tashar rediyo ta kashin kai a Jihar Neja, kafin ya ƙaru zuwa ga kai hare-haren da aka ɗauki nauyi kan taronmu na Kaduna, sannan kuma da hare-hare a kan ayarin motocin shugabannin ADC a Kebbi. “Haka kuma an kai hari a wurin taron ADC a Alimosho a Jihar Lagos, wannan yana nuna cewa APC ta ji kunya kuma ba ta girma ko...
Sojojin Yemen sun sanar da kai hare-hare kan wasu muhimman wurare a yankuna daban-daban na haramtacciyar kasar Isra’ila Dakarun Yemen sun sanar a yau cewa: Sun kai farmaki kan wasu wurare masu muhimmanci a yankin Jaffa da aka mamaye. Wannan farmakin na goyon bayan al’ummar Falastinu da ake zalunta ne, da kuma mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da kakaba yunwa da makiya yahudawan sahayoniyya suka aikata a kan ‘yan uwa a zirin Gaza, da kuma wani mataki na mayar da martani ga hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila ke kaiwa kasar Yemen. Rundunar sojin kasar ta Yemen ta kuma jaddada cewa; Rundunar sojin kasar ta kuma kai harin ne ta hanyar amfani da makamai masu...
Dakarun runduna ta 3 da rundunar haɗin gwiwa – Operation Enduring Peace (JTF OPEP) masu wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato sun kama wasu da ake zargin ɓarayin shanu ne a ƙauyen Kogul da ke Ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato. A cewar rundunar, kama waɗanda ake zargin ya biyo bayan ƙoƙarin da sojojin suka yi ne don daƙile barazanar satar shanu, “wanda ke haifar da rikici a yankin da Rundunar haɗin gwiwa ta ke.” 2027: Malamai sun gudanar da addu’o’in nasarar Tinubu-Barau a Kano An saki fursunonin siyasa 52 a Belarus Da yake yi a wa manema labarai bayan ikan nasarar da rundunar ta samu a Jos, a ranar Alhamis, kakakin rundunar, Manjo Samson Zhakom, ya ce a...
An Zabi Wuraren Ban Ruwa Hudu Na Kasar Sin Domin Shigar Da Su Jadawalin Wuraren Ban Ruwa Na Kasa Da Kasa
Rahotanni daga ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin, na cewa an kara wasu wurare hudu dake kasar Sin, cikin jerin muhimman wuraren ban ruwa na kasa da kasa ko WHIS. Wuraren sun hada da yankin ban ruwa na tafkin Chishan, da gonaki kan tuddai na kabilar Hani na Yuanyang, da madatsar ruwa ta Jianjiangyan, da tsohon mashigin ruwa na Mentougou dake kan kogin Yongding. An ce, za a shigar da wuraren cikin sabon jerin ne a hukumance yayin taro na 76, na kwamitin zartarwar hukumar kasa da kasa mai lura da wuraren ban ruwa da magudanansu ko ICID, taron dake gudana a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia. Da wannan kari, adadin wuraren dake kasar Sin da aka...
A cewarsa, kudaden fansa da ake yawan ji ana biya yawanci iyalan wadanda abin ya shafa ko al’ummarsu ne ke tarawa. Ya kuma bayyana cewa rahotanni sun nuna ’yan bindiga sun karɓi sama da Naira biliyan 2.5 a shekarar 2025 kadai, adadin da ya ce babu wata gwamnati da za ta iya ɗauka. Masanin tsaron ya ce matsalar tsaro a Najeriya ta fi ƙarfin dabarun soja kaɗai, inda ya danganta ta da cin hanci da rashawa wanda ya kira “babban mai ba da damar ayyukan ta’addanci.” Ya yi gargadin cewa ya zama dole a guji yin zarge-zargen da ba su da tushe kan shugabannin da ke kan karagar mulki, yana mai tunatar da cewa irin wadannan maganganu...
Sojojin HKI a yau Laraba sun tsananta hare-hare a cikin birnin Gaza, inda ta rusa hasumiyyar Birnin inda daruruwan falasdinawa suke rayuwa, saboda cimma manufarta na mamaye birnin gaba daya. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a safiyar yau laraba ce jiragen yakin HKI suka yi ruwan boma bomai kan Hasumiyar Tayba II wanda ke unguwar Rimal na birnin Gaza sun kuma dai-daita shi da kasa. Tun cikin kwanakin da suka gabata ne sojojin yahudawan suka fara rusa dogayen gine-gine a birnin Gaza, da nufin korar duk mutane birnin, hasumiyuar Tayba II na daga cikin dogayen gine-ginen da falasdinawa suke zama a cikinsa a gaza wanda HKI suka rusa.. Tun watan da ya gabata ne gwamnatin...
Kafar yada labaran Syria ta ce Isra’ila ta kaddamar da hare-hare ta sama a wasu sassa na tsakiya da kuma yammacin kasar. Rahotanni sun ce an kai hare haren ne a kusa da Homs da Palmyra da kuma birnin Latakia da ke gabar ruwa. Ana ganin Isra’ilan ta kai hare-haren kan sansanonin Soji ne. Ba a bayar da rahoto akan mutanen da hare haren ya shafa ba, haka ita ma Isra’ilan ba ta ce komai a kan harin ba. Isra’ila dai na kai hare-hare ta sama tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Bashar al- Assad a watan Disambar bara. ana ta bangaren gamnatin kasar siriya ta tir da kai harin tare da bayyana shi a matsayin keta dokokin kasa da...
Kamfanin Aero Engine Corporation na kasar Sin, ya fitar da sabon injin aiki a manyan na’urori mai aiki da iskar gas mai karfin gaske, wanda ke iya samar da karfin megawatt 110. Kamfanin ya fayyace sashen kirar injin mai suna Taihang 110, a yankin kira na kamfanin a Litinin din nan, kuma ana fatan fara shigar da injin kasuwa. Fitar da injin zuwa kasuwanni na nufin kasar Sin ta cimma nasarar gabatar da inji kirar gida mai matukar karfi, wanda manyan na’urori za su rika amfani da shi ta hanyar sarrafa iskar gas. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Tsagin Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya ƙi amincewa da korar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji a Jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Oginni Sunday ya raba wa ’yan jarida ranar Asabar. Musulman Kudancin Kaduna sun zargi manyan yankin da juya gaskiya Bikin naɗin Sarkin Ibadan yan hana Musulmi Sallar Juma’a — MURIC Oginni ya yi Allah wadai da korar ɗan majalisar, yana mai cewa babu wata hujja kuma ba su ba da izini ko wani iko na ɗaukar wannan hukunci ba. Sunday ya ce tuni an sallami shugaban jam’iyyar na Kano, Hashim Dungurawa tare da rukunin tsagin Kwankwasiyya daga jam’iyyarsu ta NNPP. A bayan nan ne...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Iran ta shiga cikin tsirarun kasashe wadanda suke da fasahar gina katafaren motocin jigilar ma’adinai ADAK 150AC. Tare da tsarawa da kuma gina shi a cikin gida 100%. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa duk tare da takunkuman tattalin arziki mafi muni wadanda kasashen yamma suka dorawa JMI kasar shiga cikin tsirarun kasashen duniya wadanda suke da fasahar gina irin wadannan motoci wadanda ake amfani da su a wuraren aikin tono ma’adinai. Labarin ya kara da cewa wannan ci gaban ba kawai ya nuna irin ci gaban fasahar kere-keren da kasar take da ba, sai dai kokari ne tabbar da cewa kasar ta wadatu daga saya ko kuma shigo da manya-manyan motoci da injuna daga kasashen...
Hukumar kwallon kafa ta Masar ta yi watsi da shawarar buga wasan sada zumunci da Zambia saboda masu horar da ‘yan wasan Zambia sun hada da ‘yan Isra’ila, kamar yadda kafafen yada labaran Masar suka rawaito a wannan Laraba. Wannan rashin amincewar ba a kai ga kai ga babban kocinta Avram Grant ba, wanda a baya ya taba horar da Ghana, ko mataimakinsa Eyal Lachman, sai dai a fagen siyasar da suke wakilta. Rahotanni sun bayyana cewa, an shirya wasan ne domin hutun kasa da kasa na watan Nuwamba, wanda zai gudana bayan kammala wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin Afirka, kuma wasan share fage ne gabanin gasar cin kofin nahiyar Afirka, da za a yi a Morocco daga...
Gwamnatin Kano ta sanar da cewa tana shirye-shiryen gudanar wa auren zawarawa da ’yan mata, wanda ya zarce na baya da ta yi. Babban Kwamanda Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne bayyana hakan a yayin ziyarar gaisuwa da ya kai wa Fadar Sarkin Rano a ranar Litinin. Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa Gwamnan Kebbi Sarautar Garkuwa Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya za ta karrama Sarkin Zazzau Sheikh Daurawa ya ce a wannan karon angwaye da amaren za su mori gwaggwaban tanadi na musamman daga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf. Ana iya tuna cewa, a watan Oktoban 2023 ne Gwamnatin Kano ta ɗaura auren mata 1,800 da angwayensu 1,800 wanda ta ɗauki watanni tana shiryawa. Tun bayan hawansa mulki...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
137- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka fara yakin gama gari tsakanin sojojin Imam Ali (a) da...
Sin Ta Sanar Da Rukuni Na Hudu Na Abubuwa Da Wuraren Tunawa Da Yakin Kin Jinin Mamayar Dakarun Japan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp