Cibiyar Kula Da harkokin Kasuwanci ta Kasa Ta Koka Kan Shirin Kafa Wata Cibiya Mai Aiki Irin Nata
Published: 10th, October 2025 GMT
Cibiyar Kula da Harkokin kasuwanci ta kasa ta bayyana kafa Cibiyar Gudanar da taron Kasuwanci na Najeriya a wani bangare na ganin ba a samarda cibiyoyi da ke da aiki iri ɗaya ba.
Babban magatakardar Cibiyar Mista Victor Olannye, ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da takardar a yayin taron jin ra’ayin jama’a na kwamitin majalisar wakilai kan harkokin kasuwanci a Abuja.
Mista Victor Olannye ya ce kudurin dokar da ke neman kafa sabuwar cibiyar ya ci karo da ayyukan Cibiyar Gudanarwa ta kasa da tuni Majalisar Tarayya ta 9 ta amince da ita wadda Shugaban kasar na wancan lokacin ya amince da shi.
Ya yi nuni da cewa, babban makasudin kafa Cibiyar Kula da Hadarin Kasuwancin Najeriya ta Chartered ita ce sarrafa tare da inganta ayyukan kula da hadarin kuma tuni dokar ta 2022 ta magance wannan lamarin.
A cewarsa, bayan nazarin daftarin da aka yi a tsanake, ya zama dole a jawo hankalin kwamitin kan wasu batutuwan da suka shafi dokokin da aka tsara, don kaucewa kwafin ayyuka da nauyin da aka riga aka kafa a karkashin wata doka da ta kasance da wannan majalisar.
“Dokar ta bada cikakken iko da kuma inganta al’adar kula da haɗari a kasuwanci a Najeriya, ciki har da takaddun shaida, ka’idoji, da kuma ci gaban sana’a,” in ji shi.
Don haka ya bukaci kwamitin da ya yi la’akari da watsi da kudirin, yana mai cewa ba shi damar ci gaba “zai saba wa dokokin da ake da su (Doka ta 39 ta 2022), ta haifar da rikice-rikice na shari’a da na hukumomi, da gurgunta ka’idar kaucewa kwafi da sake yin watsi da dokoki.
COV: TSIBIRI
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Cibiya
এছাড়াও পড়ুন:
Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza
Ministan wajen na Sin, ya kuma jaddada muhimmancin goyon bayan manufar kafa kasashe biyu masu cin gashin kai. Ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da sassan kasa da kasa, ciki har da Switzerland, ta yadda za a kai ga cimma nasarar aiwatar da sahihan matakan wanzar da zaman lafiya da daidaito a Gabas ta Tsakiya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA