Najeriya ta tafka asarar tiriliyan 14.5 sakamakon rikicin Boko Haram – UNICEF
Published: 9th, October 2025 GMT
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya kiyasta cewa Najeriya ta yi asarar kimanin dala biliyan 10, kwatankwacin Naira tiriliyan 14.5 sakamakon rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas. Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Wafaa Saeed, ta bayyana hakan a Maiduguri ranar Laraba yayin ƙaddamar da wani shirin farfaɗo da rayuwar yara da rikici ya shafa ta hanyar ba su horo da tallafi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arewa maso Gabas Boko Haram
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan Najeriya miliyan 60 na fama da taɓin hankali – Likita
Wani Likitan ƙwaƙwalwa a Asibitin Neuropsychiatric Aro, a Abeokuta, Jihar Ogun, Dokta Emmanuel Abayomi ya ce kimanin mutane miliyan 60 ne ke fama da taɓin hankali a halin yanzu.
Ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma’a a Abeokuta a wajen wani taron ƙarawa juna sani da Ƙungiyar likitoci ta NAS ƙarƙashin Ƙungiyar masu ruwa da tsaki ta ƙasa ta shirya domin tunawa da ranar kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa ta duniya ta bana.
Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe ’Yan sanda sun ceto mutum 3 da aka sace a Kano da KadunaShirin da Ash Montana Deck tare da haɗin gwiwar Atlantis, Americana 1 da Longhorn Deck suka yi wanda ya ja hankalin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar.
Da yake bayani game da “Samar da kayan kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa a cikin yanayin agajin gaggawa,” Abayomi ya bayyana damuwa game da ƙaruwar matsalolin ciwon taɓin hankali a tsakanin ‘yan Najeriya.
Da yake ambaton Ƙididdigar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, masanin likitancin ya ce ɗaya daga cikin mutane takwas na fama da matsalar taɓin hankali.
Sai dai a Najeriya Abayomi ya ce adadin ya fi haka inda aka ƙiyasta kimanin ‘yan ƙasar miliyan 60 ne ke fama da matsalar taɓin hankali.
“A Najeriya, adadin ya haura, a gaskiya kimanin ’yan Najeriya miliyan 60, bisa ga ƙididdigar baya-bayan nan, suna fama da matsalar taɓin hankali.
Kuma idan aka dubi adadin ƙidayar ’yan ƙasar zuwa miliyan 200 ko miliyan 240, wannan na nuna ɗaya cikin mutum biyar ko ɗaya cikin mutane shida da ke da matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa.
“Don haka, yana da yawa kuma abin damuwa ne a Najeriya,” in ji shi.