2025-11-20@19:14:45 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9166

«da Kwankwaso»:

    Ƙungiyar ɗalibai ’yan Jihar Kano ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni da ’yan Majalisar Tarayya da su kawo ƙarshen taƙaddamar Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU. Ƙungiyar ɗaliban ta ƙasa reshen Jihar Kano (NAKS) ta roƙi shugabannin da su gaggauta aiwatar da duk mai yiwuwa domin warware taƙaddamar da ke tsakanin gwamnati da ASUU. IAEA ta buƙaci Iran ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka An yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai Aminiyar ta ruwaito cewa, ɗaliban sun yi wannan kiran ne yayin wani taron manema labarai da shugabannin ƙungiyar a jami’o’in Bayero da kuma North West —Mudassir Adamu Musa da Asahabulkhair Labaran Usman —suka jagoranta. Ɗaliban sun bayyana cewa yajin aikin da ƙungiyar ASUU...
    Mahukunta a Jahar Kwara sun sanar da rufe makarantu a garuruwan Ifelodun,Ekiti, Irepodun, Isis, da Oke Ero, saboda matsalolin tsaro da ake fuskanta Kwamishinan ilimi na Jahar ta Kwara Lawal Olohungabebe ne ya sanar da daukar wannan matakin saboda abinda ya kira bayar da kariya ga rayuwar daliban da suke fuskantar barazanar masu dauke da makamai da suke karakaina a yankin. Gwamnatin ta Kwara ta dauki wannan matakin ne bayan wani lokaci kadan daga kustawa cikin wata majama’a da masu dauke da makamai su ka yi a Eruku dake karamar hukumar Ekiti. Mazauna yankin dai sun fada cikin frigici da razana haka nan kanan hukumomin da suke makwabtaka. An bayar da umarnin a rufe makarantun kwana na Irepodun saboda rahotanni...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, babban birnin Nijeriya, ta yanke wa fitaccen jagoran masu fafutukar kafa ƙasar Biafra Nnamdi Kanu, hukuncin ɗaurin rai-da-rai, bayan samunsa da aikata laifukan ta’addanci. Masu gabatar da ƙara sun buƙaci a yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin kisa, to amma Mai Shari’a James Omotosho, ya bayyana cewa a yanzu ba a amfani da hukuncin kisa, a maimakon haka ya yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai.
    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sami jagoran haramtacciyar ƙungiyar neman kafa kasar Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu, da laifukan ta’addanci da aka zarge shi da aikatawa. Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, Mai Shari’a James Omotosho, ya amince da batutuwa uku da aka gabatar a shari’ar, inda ya yanke hukunci a kan su daga bangaren masu gabatar da ƙara. Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas Alkalin ya ce barazanar tashin hankali da Kanu ya yi a cikin jawabansa ta haifar da tsoro da damuwa a zukatan jama’a a yankin Kudu maso Gabas. Justice Omotosho ya ƙara da cewa bisa...
    Gwamnatin Jihar Kwara ta bayar da umarnin rufe makarantu a ƙananan hukumomin jihar guda huɗu na saboda ƙaruwar hare-hare a jihar cikin sa’o’i 48 da suka gabata. Aƙalla mutane uku sun mutu a garin Bokungi da ke Ƙaramar Hukumar Edu a ranar Laraba. Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas Najeriya ta ɗora alhakin taɓarɓarewar harkokin tsaronta kan Amurka Lamarin ya faru kasa da sa’o’i 24 bayan mummunan harin da aka kai coci a Eruku, Ƙaramar Hukumar Ekiti ta jihar, inda aka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da mutum 30. Majiyoyin al’umma sun ce an fara yin garkuwa da mutane huɗu, ciki har da ɗan sa-kai, a cikin waɗannan hare-haren. Ɗaya daga cikin...
    Mutum uku da wani yaron babbar motar kaya sun rasa ransu bayan wayar wutar lantarki kashe su a lokacin wani bikin nadin sarauta a unguwar Idimu da ke Ƙaramar Hukumar Alimosho ta jihar Legas, bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Talata, 11 ga watan Nuwamba, kuma an gano cewa yaron motar, wanda ba a tantance sunansa ba tukuna, ya mutu nan take a wurin. Najeriya ta ɗora alhakin taɓarɓarewar harkokin tsaronta kan Amurka Babu addinin da ake yi wa kisan ƙare dangi a Binuwai — Gwamna Alia Rahotanni sun ce wani mazaunin unguwar da aka karrama da sarauta ne ya shirya taron cashiyar a titin Anjorin domin murnar nadin. Sai dai yayin da ake tsaka da bikin,...
    Mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jagoranci manyan jami’an Gwamnatin Nijeriya zuwa Amurka don tattaunawa game da zargin kisan ƙare dangi da ake yi wa Kiristoci. Lamarin ya samo asali ne bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya goyi bayan kafa ƙasashe biyu na Isra’ila da Gaza. A farkon watan nan, Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi barazanar daukar matakin soji a kan Nijeriya, kuma ya bukaci ‘yan majalisar dokokin kasar, ciki har da dan majalisa Riley Moore, su binciki lamarin. Ko da yake Nijeriya ta karyata ikirarin, amma Amurka ta ci gaba da jadadda zargin kisan Kiristoci. A ranar Talata, mawakiyar Amurka, Nicki Minaj a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ta...
    Gwamnatin Tarayya ta ɗora alhakin dawowar hare-haren ta’addanci, ciki har da sace dalibai mata a jihar Kebbi da kai hari a coci a jihar Kwara, kan kalaman da Amurka ta yi kwanan nan a kan Najeriya. Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya ce sakonnin da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa, inda ya zargi Najeriya da “kisan kiyasin Kiristoci” tare da barazanar tura sojojin kasarsa, sun kara wa wasu ƙungiyoyin ’yan ta’adda kaimin kai hare-hare. Babu addinin da ake yi wa kisan ƙare dangi a Binuwai — Gwamna Alia Yadda maganin sauro ya yi ajalin magidanci da iyalinsa a Kano “Kalaman da Amurka ta yi kwanan nan sun kara wa wasu ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya da ke son...
    Shugaban majalisar dokokin kasar Labanon Nabih Berri yayi kira da a gudanar da taron gaggawa na kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya  domin tattaunawa kan ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Israi’la ke yi kan kasar Labanon, wanda ya kashe mutane 14 , kuma ya jaddada game da muhimmancin shigar da kara a hukumance ga majalisar dinkin duniya. Wannan bukata ta zo ne adaidai lokacin da sojojin Isra’ila suke kai hare hare kan fararen hula dake jawo asarar rayuka, kuma yake jawo fargaba game da ci gaba da hara-haren israila na keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta mai lamba 1701, Isra’ila ta kai hare hare a lokuta daban daban a kudancin labanon kuma yayi sanadiyar mutuwar...
    An sanar da dan wasan Paris St Germain, Achraf Hakimi a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2025, mai tsaron baya da ya lashe kyautar karon farko bayan shekara 52. Dan wasan tawagar Masar Mohamed Salah shi ne na biyu mai taka leda a Liverpool da kuma Victor Osimhen na Super Eagles mai wasa a Galatasaray a mataki na uku. Mai tsaron bayan Morocco ya karbi kyautar sakamakon nasarorin da ya samu a 2025 tare da Paris St Geramin ciki har da lashe Champions League da Ligue 1 da Coupe de France da kuma UEFA Super Cup. Shi ne na farko daga Morocco da ya karbi kyautar tun bayan Mustapha Hadji a 1998, kuma...
    Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia, ya ce babu wani addini ko mabiyansa da ake yi wa kisan ƙare dangi a jiharsa ko a Najeriya baki ɗaya. Ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba a wani taron da Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Ƙasa (NHRC) ta shirya a Abuja kan kare haƙƙoƙin mutanen da aka tilasta musu barin gidajensu. Yadda maganin sauro ya yi ajalin magidanci da iyalinsa a Kano NAJERIYA A YAU: Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki Gwamna Alia, wanda tsohon Faston Katolika ne, ya ce: “A Binuwai, babu wani kisan kare addini, ƙabilanci, launin fata, ƙasa ko jiha. “Muna da wasu matsalolin tsaro, amma ba kisan addini...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu. Irin wadannan mata a wasu lokutan basa tsira da rayukansu, a wasu lokutan kuma ko sun tsira, sukan shiga halin ciwon damuwa wanda ke daidaita musu rayuwa, a wasu lokutan ma har sai sun ji kamar su dauki rayuwar su. NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Shirin Najeriya A Yau na...
    Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba. Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu. Ribadu ya jagoranci tawaga zuwa Amurka don ƙaryata zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana An tsara faea sauraren shari’ar a ranar Laraba, amma aka ɗage bayan lauyoyin waɗanda ake tuhuma sun nemi a ƙara musu lokaci. Lauyansu, B.I. Bakum, ya bayyana cewa har yanzu suna jiran takardun zargi da wajen DSS. Haka kuma, ya nemi a mayar da...
    Rahotanni daga Falasdinu na cewa Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 28 tare da raunata wasu 77 a zirin Gaza, wanda ke nuni da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a shiga tsakanin Amurka. Rahotanni daga kafafen yada labarai na cikin gida sun nuna cewa mata da yara 17 suna cikin wadanda Isra’ila ta yi wa kisan gilla. Sojojin Isra’ila sun kuma tabbatar da kai hari kan al-Mawasi a Khan Younis, kudancin Gaza. Isra’ila ta kai hare-hare uku daban-daban a birnin Gaza da ke arewacin yankin Falasdinawa da kuma kudancin Khan Younis, a cewar hukumar Falasdinawa. Hukumomin lafiya na Falasdinawa sun ce sojojin Isra’ila sun kai hare-hare 393, inda suka kashe akalla Falasdinawa 290 tare da raunata...
    Hukumar Kula da Harkokin Tarayyar Afirka ta AU ta yi Allah-wadai da duk wani nau’i na tsoma bakin kasashen waje a sha’anin kasashen Afirka da ke fuskantar matsalar tsaro, musamman ma game da rikicin da ake fama da shi a kasar Sudan. Da yake zantawa da manema labarai ranar Talatar da ta gabata a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, kwamishinan harkokin siyasa, da zaman lafiya da tsaro na kungiyar ta AU Bankole Adeoye, ya ce dole ne kungiyar ta AU ta jagoranci duk wata tattaunawa ta zaman lafiya a nahiyar, yana mai jaddada muhimmancin amfani da ka’idojin warware rikicin Afirka a bisa tafarkin Afirka. Adeoye ya kara da cewa, “Mu a matsayinmu na kungiyar Tarayyar Afirka, ba mu yarda...
    Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranci wata tawagar gwamnati zuwa Amurka domin mayar da martani kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya. Wannan zargi ya samo asali ne bayan mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya nuna goyon bayansa wajen kafa ƙasashe biyu tsakanin Isra’ila da Gaza. Wardley ya zama zakaran damben boksin na duniya Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana A farkon wannan watan ne Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ayyana Najeriya cikin jerin ƙasashen matsala ta musamman. Sannan Trump ya umarci wasu ’yan majalisar Amurka, ciki har da Ɗan Majalisa Riley Moore da su binciki lamarin. Duk da ƙoƙarin da Najeriya ta yi na bayyana...
    Tauraron ƙwallon ƙafar ƙungiyar PSG da ƙasar Morocco, Achraf Hakimi, ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana.  
    Tauraron ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal, ya bayyana cewa ya shirya jagorantar ƙungiyar wajen kafa sabon tarihi a filin wasa na Camp Nou, wanda za su koma buga wasa a ƙarshen makon nan yayin karɓar baƙuncin Atletico Bilbao. Tun kusan kwanaki 900 da suka gabata ne aka rufe filin wasa na Camp Nou sakamakon wasu manyan gyare-gyare da ake yi wa filin, lamarin da ya tilasta wa Barcelona komawa wasu filayen waje domin buga wasanninta. An kama miji da mata kan zargin mallakar buhuna 360 na Tabar Wiwi Osimhen ba zai halarci bikin karrama gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana ba Sai dai duk da cewa ba a kammala gyaran filin gaba ɗaya ba, an ba da damar komawa amfani...
    Rahotanni na cewa an kama wani mutum, Onun Ikoli, tare da matarsa, Itam Onun, bisa zargin mallakar buhuna 360 na tabar wiwi a Jihar Kuros Riba. Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ce ta cafke ma’auratan a ranar Talata a ƙaramar hukumar Yakurr a jihar ta Kuros Riba. Osimhen ba zai halarci bikin karrama gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana ba Tankin ruwa ya kashe mutum 4, wasu sun jikkata a Jigawa Kwamandan NDLEA na jihar, John Anteyi, yayin zantawarsa da Aminiya a Kalaba, ya ce ababen zargin sun yi iƙirarin cewa tabar wiwin wadda nauyinta ya kai tan 4.706, ta wani mutum ce da suke zaman haya a daya daga cikin dakunan gidansa. Ma’auratan sun shaida...
    Fitaccen ɗan wasan gaba na Najeriya da ke taka leda a ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya, Victor Osimhen, ba zai halarci bikin karrama gwarazan ‘yan wasan Afirka na 2025 ba. Osimhen, wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afirka a 2023, ya bayyana cewa ya koma Turkiyya ne domin duba lafiyarsa, bayan raunin da ya samu a wasan da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta doke Najeriya. Tankin ruwa ya kashe mutum 4, wasu sun jikkata a Jigawa An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari A yau Laraba ne Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) za ta sanar da sunayen gwarazan ‘yan wasan nahiyar na shekarar 2025, a yayin babban bikin da za a gudanar a Morocco. Za...
    Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza kusan sau 400 Babban Daraktan Ofishin Yada Labarai na Gwamnati a Zirin Gaza, Ismail al-Thawabta, ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta aikata laifuka 393 da aka rubuta tun lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a Zirin Gaza. Ya jaddada cewa wadannan laifukan sun shafi rayukan fararen hula kai tsaye, da nufin tsoratar da su da kuma fadada barna, ta haka ne ke kara ta’azzara yanayin jin kai da kuma barazana ga makomar kwanciyar hankali. Al-Thawabta ya kara da cewa, a cikin sanarwar da ya bayar ga Al Jazeera Net, cewa: Yanayin jin kai a Gaza yana kara muni tare da rugujewar tsarin lafiya da kuma rufe...
    An yanke wa abokan aikin ɗan tsohon shugaban kasar Gabon hukuncin ɗauri a gidan kurkuku Kotun Hukunta Laifuka ta Musamman da ke Gabon ta yanke hukuncin ɗauri a gidan kurkuku daga watanni 26 zuwa shekaru 15 ga tawagar abokan Nouruddine Bongo, ɗan tsohon shugaban ƙasa Ali Bongo, a shari’ar da aka fi sani da “Tawagar Matasa”, wacce ke da alaƙa da zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma satar dukiyar gwamnati. Bayan dogayen zaman shari’o’i da aka kammala a safiyar ranar 18 ga Nuwamba, 2025, kotun ta yanke wa Iyan Ghislain Ngolo, tsohon darektan ofishin Nouruddine Bongo, hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari, tare da dakatar da shekaru biyar, bisa tuhume-tuhumen da suka haɗa da satar dukiyar jama’a, cin...
    An shiga jimami a garin Zugai da ke Ƙaramar Hukumar Roni ta Jihar Jigawa, bayan da wani tankin ruwa ya faɗo tare yin sanadin rasuwar mutum da jikkata wasu. Daga cikin waɗanda suka rasu har da wata mace mai juna biyu. An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari Gwamna Abba ya gabatar da N1.36trn a matsayin kasafin 2026 Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya auku ne kwana uku bayan shugaban Ƙaramar Hukumar, ya raba ruwa ga masu sana’r sayar da ruwa, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin wasu mutane. Tankin ruwa, wanda ke amfani da hasken rana wajen samar da ruwa, ya fashe yayin da mutane da yawa suka taru a ƙasa domin...
    Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani shugaban ISWAP Hussaini Ismaila, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan samun sa da aikata laifukan ta’addanci. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan Ismaila, wanda ake kira Mai Tangaran, ya amsa tuhume-tuhume guda huɗu da Hukumar DSS ta gabatar a kansa. Gwamna Abba ya gabatar da N1.36trn a matsayin kasafin 2026 Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya DSS ta ce Ismaila ne, ya jagoranci kai wasu hare-haren ta’addanci a Kano a shekarar 2012. Hare-haren sun haɗa da harin Hedikwatar ’Yan Sanda ta Bompai, Barikin ’Yan Sandan Mopol a titin Kabuga, ofishin ’yan sanda na Farm Centre, ofishin ’yan...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin 2026 na kuɗi Naira tiriliyan 1.36 a Majalisar Dokokin jihar. Kasafin wanda aka yi laƙabi da “Kasafin Gine-gine, Ci Gaban Kowa da Ɗorewar Ci Gaba.” Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya Yayin jawabi da ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba, gwamnan ya ce an tsara kasafin ne don samar da sauye-sauye, kammala manyan ayyuka, inganta ilimi da harkar kiwon lafiya. Ya bayyana cewa za a kashe Naira biliyan 934.6 (kashi 68) a manyan ayyuka kamar hanyoyi, gine-gine da sauran muhimman ayyuka. Sauran Naira biliyan 433.4 (kashi 32), za su tafi...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin 2026 na kuɗi Naira tiriliyan 1.36 tiriliyan a Majalisar Dokokin jihar. Kasafin wanda aka yi laƙabi da “Kasafin Gine-gine, Ci Gaban Kowa da Ɗorewar Ci Gaba.” Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya Yayin jawabi da ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba, gwamnan ya ce an tsara kasafin ne don samar da sauye-sauye, kammala manyan ayyuka, inganta ilimi da harkar kiwon lafiya. Ya bayyana cewa za a kashe Naira biliyan 934.6 (kashi 68) a manyan ayyuka kamar hanyoyi, gine-gine da sauran muhimman ayyuka. Sauran Naira biliyan 433.4 (kashi 32), za su...
    Cibiyar Blue Sapphire ta kaddamar da wani shiri na musamman da aka kirkiro domin ƙarfafa gwiwar mata ’yan kasuwa a fannin dinkin kayan sawa da kuma harkokin kirkira a arewa maso yammacin Najeriya. Cibiyar na aiwatar da wannan shiri ne tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa Mata ta Arewa (ANWE) da Jami’ar Northwest Kano, tare da tallafin Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU). Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ Da take jawabi a wajen kaddamarwar a Kano ranar Talata, shugabar cibiyar, Maryam Lawan Gwadabe, ta ce an kirkiro shirin ne domin samar wa mata amintaccen muhallin da za su yi amfani da shi wajen...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da tafiyarsa zuwa Birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu, da Luanda na Angola, sakamakon sace ɗalibai a Jihar Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada a wata coci da ke yankin Eruku a Jihar Kwara. Tinubu, shirya barin Abuja a ranar Laraba domin halartar taron G20 karo na 20 da kuma Taron AU-EU karo na bakwai. Sanatan Enugu ya mutu a Birtaniya ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba. “Shugaban ƙasa ya umarci sojoji da ’yan sanda da su aike ƙarin jami’ai zuwa waɗannan yankuna domin a tabbatar...
    Majalisar Dattawa ta shiga cikin jimami a ranar Laraba bayan mutuwar Sanata Okey Ezea, mai wakiltar mazabar Enugu ta Arewa. Bayanai sun nuna marigayin ya rasu ne a kasar Burtaniya inda yake jinya. ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ Mai taɓin hankali ya kashe soja a Legas Ezea, wanda aka zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar LP, shi ne kaɗai Sanatan da ya ci zabe daga Enugu karkashin jam’iyyar a Majalisar Dattawa ta 10. Rasuwarsa ta sa ya zama sanata na biyu daga yankin Kudu maso Gabas da ya rasu cikin shekaru biyu, bayan mutuwar Sanata Ifeanyi Ubah daga Jihar Anambra, wanda shi ma ya rasu a Landan a watan Yuli 2024 yana da shekara 52. Da labarin...
    pirme ministocin kungiyar hadin guiwa ta kasashen shangai SCO sun kawo karshen taron kungiyar karo na 24 a birnin mosko inda suka fitar da bayanin hadin guiwa na yi watsi da duk wani mataki na kasashen turai dake nuna adawa da kasar iran, musamman kan abin da ya shafi shirin ta na nukiliya na zaman lafiya. Bayanin karshe na taron da mamabobin kungiyar suka fitar ya yi tir da adawa da kasashen yamma ke nunawa kasar iran  da ya shafi takunkumin karya tattalin arziki da ya sabama dokokin kasa da kasa , shuwagabannin sun yi gargadin cewa daukar irin wannan matakai zai cutar da majalisar dinkin duniya wajen cimma kudurin ci gaban alumma. Kasashen Amurka da sauran kawayenta sun maka...
    Majalisar Wakilai ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya sake kawo sabuwar dabarar da za ta kawo karshen kashe-kashe, da sace-sace da sauran ayyukan ‘yan bindiga a Jihar Zamfara da ma kasa baki daya.  Wannan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na kula da muradun jama’a da dan majalisa mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta jihar Zamfara, Hon. Kabiru Amadu, ya gabatar a zaman majalisar . A yayin gabatar da kudirin, Amadu ya bayyana cewa, idan aka yi la’akari da kalubalen tsaron da “yaki ci yaki cinyewa” a Jihar Zamfara da ma fadin kasar, za a iya cewa, “gwamnati ba ta yi abin da ya dace ba don kare rayuka da kadarorin ‘yan Nijeriya don ba su damar...
    Rahotanni sun nuna cewa hare-haren da Isra’ila ta kai a sansanin yan gudun hijira na Ainul Hilwa dake kusa da Sidon yayi sanadiyar shahadar falasdinawa 22 tare da jikkata wasu da dama, kana sun soki kasar Labanon game da rashin daukar matakin soji da na siyasa akai. Harin an kai shi ne kan sansanin yan gudun hijira mafi girma dake kasar Labanon  yanzu dai dubban gidaje ne suka shiga cikin fargaba saboda da hare haren da isra’ila ke kaiwa ba kakkautawa, Gwamnatin kasar labanon na fuskantar mummunar suka na rashin daukar matakan da suka dace da haka yasa isra’ila ke yawan kai hare-hare a kudancin kasar, yayain da jami’an gwamnatin ke cewa yanzu haka suna shirin mika wani korafi  ga...
    Wani mutum da ake zargin yana fama da matsalar tabin hankali ya kai hari tare da kashe wani soja a yankin Imota da ke Ikorodu a jihar Legas. Lamarin, wanda ya faru a fili da rana tsaka a ranar Lahadi, ya sa makwabtan wurin da dama guduwa don neman tsira. Gobara ta laƙume kasuwar Katako a Gombe Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar Alhamis Shaidu sun bayyana cewa wanda ya kai harin, wanda ba shi da makami sai sanda ta itace, ya kusanci sojan ya dinga dukan shi da sandar. Sojan da ya rasu, wanda aka ce yana aiki a karkashin Operation AWASE, rundunar haɗin gwiwa ta musamman da ke yaki da laifuka...
    Kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya, daga dala biliyan 600 da kasar ta zuba a baya. Yariman Saudiyyar ne Mohammed Ben Salman ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da Shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da ya kai fadar gwamnatin Amurka, bayan ganawar sirri da suka yi. A baya ne Trump ya bukaci Saudiyya da ta kara hannun jarinta a Amurka, sannan ya bukaci yariman ya tabbatar, inda shi kuma ya amsa da cewa, “tabbas.” Shugaban na Amurka ya ce Saudiyya za ta zama “babbar kawar kawance wacce ba daga NATO ba,” Ya kuma sanar da karfafa hadin gwiwar soja zuwa wani matsayi mafi...
    A wani lokaci yau Laraba ne aka shirya shugaban majalisar dokokin Togo zai gana da Shugaban Rasha Vladimir Putin a Moscow. Tattaunawa tsakanin shugabannin biyu, wadanda suka dade suna da kyakkyawar dangantaka, za ta mayar da hankali kan zaman lafiya da tsaron yankin, da kuma batutuwa daban-daban, tun daga da makamashi zuwa ciniki da noma. Wannan zata zama ganawarsu ta farko ta keke da keke tun shekarar 2019. Wannan ziyarar aiki, bisa gayyatar Vladimir Putin, wani bangare ne na “shawarwarin da Rasha ke ci gaba da gudanarwa a cikin ‘yan watannin nan da abokan huldarta na kasa da kasa,” a cewar wata sanarwa da aka fitar a Lomé. Kamfanin dillancin labarai na Rasha TASS ya ambato Togo a cikin kasashen...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Batun kubutar da ɗalibai mata da masu garkuwa da mutane suka sace na makarantar GGCSS Maga dake karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi na daya daga cikin abubuwan da alumma suka maida hankali a kai.   Iyayen wadannan yara, da sauran masu ruwa da tsaki na ganin ya kamata a yi dukkan mai yiwuwa don ganin an ceto wadannan yara ba tare da sun samu rauni ba. NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai. Domin sauke...
    A ranar Alhamis, 20 ga watan Nuwamban 2025, ake sa ran Majalisar Wakilan Amurka za ta gudanar da zama na musamman domin bincikar zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya. Kwamitin Majalisar Wakilan kan Afirka ya sanya ranar domin bitar fasalin da Shugaba Donald Trump ya yi kwanan nan na sanya Nijeriya a matsayin kasar da ake sa wa ido na musamman, CPC, kan zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi. Gwamnan Taraba ya dakatar da ficewa daga PDP saboda sace ɗalibai a Kebbi Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa, an gayyaci mambobin Kwamitin Harkokin Waje na majalisar, wanda aka shirya za a yi tattaunawar da...
    Dan wasan gaban Manchester United, Benjamin Sesko zai yi jinyar makonni huɗu, lamarin da zai hana shi buga wa ƙungiyar wasanni shida a jere. Šeško mai shekaru 22, ba zai samu damar taka leda ba a wasan da United za ta karɓi baƙuncin Everton a Old Trafford mako mai zuwa. Gwamnan Taraba ya dakatar da ficewa daga PDP saboda sace ɗalibai a Kebbi Mutane 7 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa Haka kuma ba zai haska ba a sauran wasannin da za su biyo baya da Crystal Palace, West Ham, Wolves, Bournemouth da kuma Aston Villa. Ana sa ran dan wasan na ƙasar Slovenia zai dawo cikin ƙungiya ne a lokacin da Manchester United za ta karɓi baƙuncin Newcastle...
    Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya sanar da dakatar da sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC a dalilin sace ɗalibai mata ’yan sakandire da aka yi a Jihar Kebbi. Gwamnan ya ce zai ci gaba da tattaunawa da kuma nazari kan lokacin da ya fi dacewa ya sauya sheƙar tare da magoya bayansa. Mutane 7 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi Aminiya ta ruwaito cewa, da sanyin safiyar Litinin, 17 ga watan Nuwambar 2025, mahara suka shiga a makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, inda bayanai ke nuni da cewa sun yi awon gaba da ɗalibai 25 tare da halaka mataimakin...
    Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Jihar Jigawa ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai ciki har da direban motar tare da jikkata wasu 11. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Shiisu Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a Dutse. Anthony Joshua zai yi dambe da tauraron YouTube Jake Paul a Disamba Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi Ya ce hatsarin ya afku ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin Lahadi, 16 ga Nuwamba 2025, a ƙauyen Jigawan Kurma da ke kan titin Kiyawa zuwa Azaren Jihar Bauchi. A cewar SP Shiisu, “Mota kirar Hummer ce da ta taso daga Kano zuwa Potiskum ɗauke...
    Fira ministan jamhuriyar Kalmykia mai kwarya-kwaryar cin gashin kai a tarayyar Rasha, Utshir Janibinov ya fada wa manema labaru a wurin taron gwamnonin gundumomin dake gabar ruwan “Caspian” cewa; Taron da aka yi wanda shi ne irinsa na farko yana da tasiri mai kyau wajen bunkasa alaka a tsakanin gundumomin gabar ruwan “Caspian”. Taron na gwamnonin gundumomin da suke a gabar ruwan “Caspian” an yi shi ne dai a garin Rasht a gundumar Gilan  dake nan Iran. Mataimakin Fira ministan jamhuriyar Kalmykia ta tarayyar Rasha, ya bayyana jin dadinsa na halartar wannan taron a nan Iran. A Yau Talata ne dai aka bude wannan taron wanda aka bai wa taken: ” Tekun Caspian A Matsayin Wata Gada Ta Bunkasa Alaka...
    A wani labari da kungiyar “ISWAP” mai alaka da “Isis” ta watsa, ta sanar da kashe wani babban jami’in sojan Najeriya a wani kwanton bauna da ta yi wa sojoji a kusa da kauyen Wajiroko dake Jahar Borno a ranar Juma’ar da ta gabata. Sanarwar kungiyar ta “Isis” ya kuma kunshi cewa, baya ga Birgediya  janar Uba da su ka kashe, sun kuma kashe wasu sojojin 4. Kamfanin dillancin labarun “Reuters” da ya tuntubi rundunar sojan kasar ta Najeriya domin samun Karin bayani akan abinda ya faru bai sami jawabi ba. Sai dai rundunar sojan ta Najeriya ta ce labarin da ake watsawa na kama babban jami’i mai mukamin janar, ba gaskiya ba ne, kuma bai kamata ‘yan kasa su...
    Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta bayyana matuƙar damuwa kan harin da aka kai Makarantar Sakandiren Mata da ke Maga a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi, wanda ya yi sanadin sace ɗalibai mata da dama tare da kashe jami’an makarantar. Shugaban ƙungiyar, kuma Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da rashin hankali, yana mai cewa ci gaba da kai hare-hare kan makarantun Arewa barazana ce ga zaman lafiya da makomar ilimi a yankin. Barau FC ta doke Enugu Rangers a Firimiyar Najeriya Anthony Joshua zai yi dambe da tauraron YouTube Jake Paul a Disamba A madadin sauran gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Kebbi, iyalan waɗanda aka sace da kuma waɗanda...
    Tsohon zakaran damben duniya a ajin masu nauyi, Anthony Joshua, zai fafata da tauraron YouTube, Jake Paul, a wani damben ƙwararru da za a yi a watan Disamba mai zuwa. Joshua, ɗan ƙasar Birtaniya mai shekaru 36, wanda ya lashe kambun duniya ajin masu nauyi sau biyu, zai kara da Paul a cibiyar Kaseya Center da ke Miami. ’Yan bindiga sun sako mutane 45 bayan sulhu a Katsina Barau FC ta doke Enugu Rangers a Firimiyar Najeriya Ana sa ran za a watsa damben kai tsaye a tashar Netflix a ranar 19 ga Disamba. Wadda za ta kasance fafatawa mai turmi takwas, kowanne na mintuna uku. Joshua, wanda ya yi fafatawa uku a baya da nauyin sama da kilogram 113,...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta doke Enugu Rangers da ci 2-0 a wasan mako na 13 na Firimiyar Najeriya da suka buga a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Jihar Kano. Umar Bala Mohammed ne ya fara zura ƙwallo ta farko a minti na 25, kafin Joseph Kemin ya ƙara ta biyu a minti na 72 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci. HOTUNA: Fada ya barke a Hedikwatar Jam’iyyar PDP ’Yan bindiga sun sako mutane 45 bayan sulhu a Katsina Wannan nasarar ce ta uku da Barau FC ta yi cikin wasanni 12 da ta buga a kakar bana, inda ta yi kunnen doki a wasanni huɗu, aka kuma doke ta a biyar. Yanzu...
    Ministan harkokin wajen Najeriya ya ce kasar ta soma tattaunawa da Amurka, bayan barazanar da Shugaba Trump ya yi na kai wa Najeriya harin soji kan kisan kiristoci da ya ce ana yi a kasar. A wata hira da kamfanin dillancin labarai na AFP, yayi da Yusuf Maitama Tuggar ya ce abin da suke tattaunawa a kai shi ne yadda za su hada kai wajen magance matsalolin tsaro don amfanin duniya. A farkon watan Nuwamban nan Trump ya ce ya bai wa ma’aikatar tsaron Amurka umurnin ta soma tsara yadda za ta kai hari Najeriyar. Sai dai ministan ya ce ba ya tunanin Amurka za ta yi hakan, ” muna ci gaba da tattaunawa, kuma ana samun ci gaba a...
    Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya amince da daftarin kuduri da kasar Amurka ta gabatar mata na kafa sansanin sojojin kasa da kasa a yankin Gaza. An amince da kudurin ne a jiya litinin inda aka amince da shirin na Donald Trump kan Gaza kuma ta bada umarnin kirkiro dakarun kasa da kasa na hadin guiwa da zai hada da mafiyawancin daga kasashen musulmi da zai kunshi  kasashen Masar, Indonesia, da kuma kasar Azarbaijan, Kungiyar Hamas ta yi watsi da wannan kuduri da zai kunshi dakarun kasada kasa domin baya wakiltar hakkokin falasdinawa kuma an yi shi ne domin kwabe dammarar dakarun gwagwarmayar neman yancin falasdinu. Haka zalika ta kara da cewa kudurin bai kunshi bukatun siyasa da taimakon...
    Rahotanni sun bayyana cewa Craig mokhiber tsohon babban jami’in hukumar kare hakkin dan adam na majalisar dinkin duniya ya sanar a hukumance yin Allah wadai da kuri’ar amincewa da kudurin Amurka da aka yi a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya na aikewa da dakarun kasashen waje zuwa yankin Gaza yace wannan baban abin kunya ne. Kalaman nasa ya nuna irin suka da kungiyoyin kasa da kasa suke yi ne kan mummunan tasirin da yakin yayi wa yankin gaza, da kuma kasa tsagaita wuta da yadda za’a shigar da kayayyakin agaji zuwa yankin Isra’ila ta toshe kafar shigar da magunguna da kayayyakin lafiya da kuma hana fitar da marasa lafiya sama da 16500 zuwa wajen don yi musu maganin, bayan...
    An ba wa hamata iska a Hedikwatar Jam’iyyar PDP da ke Abuja a tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna. Fadan ya barke ne bayan bangarorin sun halarci ofishin domin gudanar da tarukansu daban-daban a safiyar Talata. Idan ba a manta ba, bangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike, wadanda uwar jam’iyyar ta dakatar a yayin babban taronta na kasa da ya gudana  a karshen mako ya kira taron gaggawa a yau Talata a hedikwatar Jam’iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja.    
    “Cikin hukuncin Allah, sojojin Daularmu sun kama ‘Kwamandan Runduna’… bayan ya gudu daga harin kwantan-ɓauna… Bayan mun yi masa tambayoyi, Mujahidai suka kashe shi.” An kuma wallafa wani hoto a kafafen sada zumunta da ya nuna Janar Uba a ɗaure. Har yanzu rundunar sojin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa game da wannan lamari ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi November 18, 2025 Manyan Labarai Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai  November 17, 2025 Manyan Labarai Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC November 17, 2025
    Masu gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) a ranar Litinin din nan sun bukaci kotun da ta zartar da hukuncin daurin rai da rai kan Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman, wanda aka fi sani da Ali Kushayb, kwamandan rundunar Rapid Support Forces (RSF), saboda rawar da ya taka a ta’asar da aka aikata a lokacin harin da aka kai a yankin Darfur na kasar Sudan. An samu Kushayb da laifuka 27 da suka hada da laifukan yaki da cin zarafin bil adama da suka hada da kisan kai, azabtarwa, fyade, da dai sauran manyan laifuka. Shari’ar dai ita ce shari’ar farko da aka shigar a gaban kotun ICC dangane da yakin  Darfur. A farkon...
    Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da daftarin kudurin Amurka, don ba da izinin kafa Rundunar Tsaro ta Kasa da Kasa (ISF) a Zirin Gaza. Mambobi 13 daga cikin 15 na Majalisar sun amince da kudurin, inda Rasha da China suka kaurace wa kada kuri’ar. Kudurin yana da nufin tura sojojin kasashen waje na wucin gadi don kula da tsaro, tallafawa sake ginawa da kuma kiyaye tsari a yankin. Daftarin ya yi kira ga rundunar ta yi aiki na tsawon shekaru biyu, tare da yiwuwar kara sabunta wa’adin aikinta wanda ya danganta ne da ci gaban da ake samu a kasa. Kudurin ya kunshi abubuwa da yawa,  ciki har da kare iyakokin Gaza, kare fararen hula, kare hanyoyin...
    Gwamna Ahmed Idris na Jihar Kebbi ya ba da tabbacin cewa jami’an tsaro za su ƙwato ’yan matan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kwalejin ’Yan Mata ta GGCSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasu ta jihar cikin ƙoshin lafiya. Gwamnan ya bayar da tabbacin ne a yayin ganawarsa da iyayen ɗaliban kaɗan bayan harin ’yan bindigar a ranar Litinin. Aminiya ta ruwaito cewar da asubahin ranar ’yan bindiga suka kusta cikin harabar makarantar kwana ta ’yan mata ta GGCSS Maga, suka kwashe ɗalibai 25 daga ɗakin kwanansu zuwa cikin jeji. Maharan da suka riƙa harbi a iska kafin su shiga harabar makarantar sun bindige Matakin Shugaban Makarantar, Malam Hassan Yakubu Makuku, wanda ya yi ƙoƙarin...
    Kafofin yada labaran kasar Rasha sun rawaito a jiya Litinin cewa an dakile wani yunkurin kisan gilla kan sakataren majalisar tsaron kasar Rasha Sergei Shoigu a makabartar Troyekurov da ke birnin Moscow. Kafofin yada labaran kasar Rasha sun rawaito majiyoyi suna bayyana cewa wadanda suka aikata laifin sun yi yunkurin tayar da bam ne a lokacin ziyarar Shoigu a kaburburan ‘yan uwansa. Kazalika majiyoyin sun tabbatar da kame dukkan wadanda ake zargin tare da dakile shirin nasu, kamar yadda kafafen yada labaran Rasha suka rawaito. Shoigu ya taba rike mukamin ministan tsaron kasar Rasha daga shekara ta 2012 zuwa 2014 kafin shugaba Vladimir Putin ya nada shi sakataren kwamitin tsaron kasar ta Rasha, wanda ya zama babban mai bayar da...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana November 17, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing November 17, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO November 17, 2025
    Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka kan sabon harin da ’yan bindiga suka kai makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, wanda ya kai ga sace ɗalibai mata sama da 25 tare da halaka mai gadi da mataimakin shugaban makarantar. A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Amnesty ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici da kuma nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa ballantana kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga. CAF ta fitar da ’yan wasa uku da suka rage a takarar gwarzon Afirka na bana Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas Ƙungiyar ta ce bincikenta ya gano...
    A Damaturu, farashin mudun shinkafa ya ragu daga N5,000 zuwa N2,500, yayin da wake, masara da gero suma suka sauka fiye da rabin tsohon farashinsu. Masana tattalin arziki sun ce yawaitar shigo da hatsi kamar shinkafa da alkama ya taimaka wajen rage tsadar abinci da ake fama da ita a watannin baya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065% November 17, 2025 Labarai ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga  November 17, 2025 Labarai Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi November 17, 2025
    Hukumar ƙwallon ƙafar Afirka CAF, ta bayyana cewa bayan tankade da rairaya da ta yi, a yanzu ’yan wasa uku kacal ne suka rage a takarar gwarzon nahiyyar na bana. A wata sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana Achraf Hakimi da Mohamed Salah da Victor Osimhen, a matsayin sauran ukun da suka rage a takarar gwarzon dan ƙwallon ƙafar Afirka na bana. Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno Hakimi, kyaftin din Morocco, ya lashe kofuna daga ciki har da Champions League a PSG — na farko a tarihin ƙungiyar — da Ligue 1, da European Super Cup, da kuma kai wa zagayen ƙarshe...
    Gobara ta laƙume rayukan wasu yara biyu ’yan gida ɗaya a unguwar Rumuola da ke ƙaramar hukumar Obio/Akpor a Jihar Ribas. Bayanai sun ce ibtila’in ya auku ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Lahadi, lokacin da gobarar ta tashi a ɗaya daga cikin wasu ɗakunan haya da mahaifiyar yaran ta kulle ’ya’yanta huɗu ta tafi sayen kayan girki. Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno ’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe A cewar mazauna yankin, cikin yaran huɗun, biyun da suka riga suka kwanta barci sun ƙone su kurmus, yayin da sauran biyun da ke farke suka samu damar tserewa. Aminiya ta ruwaito cewa, mazauna yankin da sun ankara da gobarar...
      An samu wannan raguwar ne sakamakon sauye-sauyen da aka samu a shekarar da muke ciki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga  November 17, 2025 Labarai Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi November 17, 2025 Labarai MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi November 17, 2025
    Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun kashe wani babban kwamandan rundunar sojin Najeriya bayan wani harin kwantan ɓauna da aka kai wa tawagarsa a hanyar Damboa–Biu da ke Jihar Borno. Lamarin ya faru ne bayan da tawagar sojojin tare da dakarun haɗin gwiwa na Civilian Joint Task Force (CJTF) suka kai wani samame a yankin, inda suka gamu da harin ba-zata na ’yan ta’adda. ’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS Kwamandan, wanda daga baya aka bayyana sunansa a matsayin Brigade Commander M. Uba, shi ne ya jagoranci rundunar da ta kai ɗauki ga wasu sojoji da suka yi ɓatan hanya kafin su faɗa tarkon mayaƙan ISWAP. PRNigeria ta...
    Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya bayyana cewa: Iran tana da kyakkyawar alaƙa ta musamman da kuma al’adu da membobin ƙungiyar haɗin gwiwa ta Shanghai Mataimakin Shugaban Kasa na Farko na Iran ya ce, “Iran tana da alaƙar haɗin gwiwa na musamman da al’adu da dukkan ƙasashe membobin Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai (SCO), kuma abin farin ciki, ƙasar Iran ta shiga ƙungiyar SCO a hukumance cikin shekaru biyu da suka gabata.” Da yake jawabi a Filin Jirgin Sama na Mehr-abad kafin ya tashi zuwa Rasha don halartar taron kolin kungiyar Shaanghai ta SCO, Mataimakin Shugaban Kasa na Farko Mohammad Reza Aref ya ce, “Ƙungiyar SCO ƙungiya ce mai tasowa amma mai ƙarfi da cikakken iko. Jimillar yawan al’ummar ƙasashe...
    Jagoram juyin juya halin Musulunci da kan sa ya jagoranci yaki da harkokin al’umma a lokacin yakin wuce gona da iri na karshe kan Iran Kakakin Rundunar Tsaron kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), Brigadier Janar Ali Mohammad Na’ini, ya tabbatar da cewa: Maƙiya ‘yan sahayoniyya ba su da yanayin sabon yaƙi, kuma abin da ake gabatarwa a yau shine yaƙin tunani da yaƙin da aka saba gani. A wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr, Brigadier Janar Na’ini ya ba da labarin lokutan shaƙatawa da ba zato ba tsammani na barkewar yaƙin da kuma shahadar wasu manyan kwamandojin soja na ƙasar. Ya kuma lura da yadda aka sake gina sansanin umarni a cikin ɗan gajeren lokaci da kuma...
    Wata sanarwa da gwamnati ta fitar a Gaza ta yi gargadin cewa: Akwai wani bala’i da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin jin kai Ofishin Yada Labarai na Gwamnati a Zirin Gaza ya fitar da Sanarwar Manema Labarai Mai Lamba (1021) a yau, Litinin, inda ya yi magana kan sabbin ci gaba da manufofin gwamnati, tare da mai da hankali kan rikicin jin kai da Falasdinawa da aka kora suka fuskanta sakamakon mummunan harin sojojin mamayar Isra’ila. Sanarwar ta nuna cewa gwamnatin mamayar Isra’ila ta haifar da mummunan bala’in gidaje, inda sama da iyalai Falasdinawa 288,000 ke fuskantar mawuyacin hali saboda rashin kayan more rayuwa na yau da kullun. Gwamnatin mamayar Isra’ila ta kara ta’azzara bala’in da gangan...
    Babban sakataren Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta HIzbullahi ta kasar Lebanon  ya jaddada cewa: Gwamnatin Lebanon zata yi babban kuskure idan ta bi hanyar sassauci Babban Sakataren Kungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah Na’im Qassem ya bayyana cewa: Amincewa da yin shawarwari da gwamnatin mamayar Isra’ila da kuma amincewa da sharuddan da wakilin Amurka Tom Barrack ya gabatar ya zama sassauci, yana mai jaddada cewa: Gwamnati tana yin kuskure idan ta bi hanyar sassauci don kawo karshen zalunci kan kasar. Qassem ya jaddada cewa: Kasar Lebanon, tare da dukkan cibiyoyinta, ita ce ke da alhakin tsara shirye-shirye don tunkarar zaluncin, yana mai jaddada cewa tura sojojin nanayar Isra’ila a yankin kudu da kogin Litani, duk da ci gaba da zalunci kan kasar...
    Rushewar ramukan hako ma’adinai ta kashe ma’aikata 32 a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai 32 ne suka mutu a ranar Asabar sakamakon zaftarewar ƙasa a wani ma’adinan cobalt a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, yayin da ake ci gaba da neman waɗanda har yanzu ba a same su ba a yankin. Zaftarewar ƙasa ta faru ne a wurin Kalandu da ke cikin ma’adinan Mulundu kusa da Kolwezi, wani wuri da kamfanin Bajiklem ke gudanar da shi a hukumance. Ministan harkokin cikin gida na lardin, Rui Kawumba Mayondi, ya ce “masu hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba sun kai hari kan wurin duk da haramcin da aka sanya saboda ruwan sama mai ƙarfi da kuma haɗarin zaftarewar ƙasa,” ya...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama ƙunshi 66 na ganyen tabar wiwi a wani samame da ta kai a garin Deba, bayan samun wasu sahihin bayanan leƙen asiri. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ranar 16 ga Nuwamba, 2025, lokacin da aka hango wata mota mara lamba, ƙirar Toyota Corolla, da ake zargi tana ɗauke da kayan, a kan hanyar Kuri zuwa Deba. Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano Aminiya ta ruwaito cewa, bayan isar jami’an wurin da ake zargin akwai kayan laifin ne, sun lura da wasu...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama ƙunshi 66 na ganyen tabar wiwi a wani samame da ta kai a garin Deba, bayan samun wasu sahihin bayanan leƙen asiri. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ranar 16 ga Nuwamba, 2025, lokacin da aka hango wata mota mara lamba, ƙirar Toyota Corolla, da ake zargi tana ɗauke da kayan, a kan hanyar Kuri zuwa Deba. Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano Aminiya ta ruwaito cewa, bayan isar jami’an wurin da ake zargin akwai kayan laifin ne, sun lura da wasu...
      Ya kuma yi Allah wadai da kisan wani jigo na Jam’iyyar APC, Umar Moriki, da kuma sace-sacen jama’a da aka yi a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, inda aka sace iyalai baki daya, ciki har da mata da yara. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi November 17, 2025 Manyan Labarai Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai  November 17, 2025 Manyan Labarai Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC November 17, 2025
    Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce hauhawar farashin kayyayaki a ƙasar ya ragu zuwa kashi 16.05 cikin 100 a watan Oktoban 2025. Cikin rahoton wata wata da hukumar ke fitarwa, ta ce hauhawar farashin ya ragu ne da kashi 1.97 idan aka kwatanta da kashi 18.02 da aka samu a watan Satumba. ’Yan Majalisar Dokokin Taraba 16 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar. Aminiya ta ruwaito cewa, tun dai daga watan Yunin bana, hauhawar farashin kayayyaki ke ci gaba da sauka a ƙasar har kawo yanzu. Ana iya tuna cewa, tun watanni kadan da...
    An ɗaura auren Sanatan Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila, da Aisha Isah, wata jami’ar soji a Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, a wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar sali-alin a Rano. Ɗaurin auren wanda jama’a kaɗan ne suka halarta ya gudana ne da safiyar Litinin ɗin nan a fadar Sarkin Rano da ke Jihar Kano, lamarin da ya nuna cewa ba a yi wata sanarwa ta musamman ba kafin bikin. Masu ibadar Umarah 42 sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Makka ’Yan Majalisar Dokokin Taraba 16 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC Mai taimaka wa sanatan kan harkokin yaɗa labarai, Muttaqa Babire, ya tabbatar da auren a shafinsa na Facebook, inda ya wallafa hoton sanatan...
    Ma’aikatar raya al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta fitar da sanarwa a jiya Lahadi, wadda ke kira ga al’ummunta da su yi taka-tsantsan a kwanakin nan wajen zuwa yawon bude ido kasar Japan. Game da hakan, masani a kwalejin bincike ta Nomura Takahide Kiuchi, ya bayyana a jiyan cewa, raguwar yawan Sinawa masu zuwa yawon bude ido Japan, zai haifar da raguwar GDPn kasar ta Japan da kashi 0.36%, kana hasashen yawan asarar tattalin arziki da hakan zai haifar zai kai JYE tiriliyan 2.2, kwatankwachin kudin Sin yuan biliyan 101.6. Bayanai sun nuna cewa, kasar Sin ce babbar abokiyar ciniki mafi girma ta Japan, kasa ta biyu mafi girma wajen fitar da kayayyaki zuwa kasar, kana babban...
    Bonzena ya ƙara da cewa duk da cewa kafin yanzu APC ce ke da rashin rinjaye a majalisar, an ci gaba da aiki cikin zaman lafiya, amma yanzu yana farin cikin ganin cewa dukkan mambobin majalisar sun haɗe ƙarƙashin tsari daya da ya yi daidai da hangen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi November 17, 2025 Manyan Labarai Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka November 17, 2025 Manyan Labarai Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda November 17, 2025
    Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Taraba, Rt Hon. Kizito Bonzena, tare da ’yan majalisar 15 sun sauya sheka daga jam’iyyarsu ta PDP zuwa APC. A saifyar Litinin ne Rt Hon. Kizito Bonzena ya gabatar da takardarsa ta ficewa daga PDP tare da sauran mambobin zuwa APC. Ya bayyana cewa da sauyin shekar tasu, yanzu APC ce ke da daukacin kujeru 24 da ke Majalisar Dokokin Jihar Taraba. Hakan na zuwa ne jim kadan bayan Gwamnan Jihar Taraba, Kefas ya sanar da shirinsa na komawa APC daga PDP. Masu ibadar Umarah 42 sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Makka ’Yan ta’adda sun sace dalibai 25 a dakunan kwanansu a Kebbi Sauran mambobin majalisar da suka sauya sheka sun hada da...
    Wasu masu ibadar Umara 42 sun mutu bayan da motarsu ta yi taho-mu-gama da wata tankar mai a kusa da birnin Madina da ke kasar Saudiyya. Dukkan masu ibadar ’yan kasar Indiya ne, kuma hatsarin ya ritsa da su ne a kan hanyarsu ta zuwa Makka bayan kammala ziyara a birnin Madina. Ministan harkokin wajen Indiya Dakta S. Jaishankar ya bayyana cewa mutum daya daga cikin fasinjojin ya tsallake rijiya da baya a hatsarin da ya auku da tsakar daren Litinin. Hatsarin ya auku ne a bayan da motar safa mai daukar mutum 43 da masu ibadar suke ciki ta yi karo gaba-da-gaba da wata tankar mai. ’Yan ta’adda sun sace dalibai 25 a dakunan kwanansu a Kebbi NELFUND ya...
    Rahotanni sun bayyana cewa bangarorin falasdinawa sun yi watsi da kudurin da aka kaddamar ga kwamitin sulhu na majalsar dinkin duniya na shirin aikewa da sojojin ketare zuwa yankin Gaza sun yi kira ga kasar Aljeriya da sauran mambobin da ba na dindin ba a kwamitin sulhu da su kalubalance shi. Daftarin kudurin an tsara za’a kada kuri’a akan shi  a yau litinin na yiyuwar akewa da dakarun kasashen waje 20,000 domin kulawa da iyakokin Gaza, da kuma bada huro ga yan sandan falasdinu . A Sanarwar hadin guiwar dukkan bangarorin falasdinawan sun yi tir da wannan shiri, inda suka bayyana shi a matsayin wani sabon salo na kara mamaye yankin dama alummarsa,   domin bada halacci ga zaman dakarun kasashen...
    ’Yan ta’adda sun harbe Mataimakin Firinsifal har lahira, sa’annan suka yi garkuwa da dalibai 25 a Makarantar ’Yan Mata ta Gwamnati (GGCSS) da ke yankin Maga a Karamar Hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun bindige Malam Hassan Yakubu Makuku ne a yayin da yake kokarin kare daliban, a lokacin farmakin da aka kai makarantar da misalin karfe 5.20 na Asubahin ranar Litinin. Wani shaida ya ce, “Harin ya dimauta al’ummar garin Maga, yanzu muna cikin zullumi da alhini.” Ya kara da cewa, ’yan ta’addan sun harbe Malam Hassan ne a yayin da yake kokarin hana su tafiya da daliban.”
    Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya bayyana cewa ya raba jimillar kuɗi Naira biliyan 116 domin tallafa wa dalibai a faɗin ƙasar nan wajen biyan kuɗin makaranta da kuma kula da rayuwarsu ta yau da kullum. Shugaban NELFUND, Akintunde Sawyerr ya bayyana a Abuja cewa, daga cikin kuɗin, an tura Naira biliyan 65 aka tura kai tsaye zuwa makarantu 239 na tarayya — jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi — domin biyan kuɗin makarantar ɗaliban da aka amince da buƙatar lamuninsu. Sauran Naira biliyan 51 kuma an tura ne kai tsaye ga ɗaliban a matsayin tallafin kula da rayuwa na wata-wata. Ya ce: “Mun raba Naira biliyan 65 ga makarantu da kuma Naira biliyan 51 ga ɗaliban domin tallafin...
    Rundunar Ƴansandan birnin tarayya ta bayyana cewa babu wani rahoto ko bayanin da ta samu game da yunkurin kashe laftanar Ahmed Yerima, jami’in Sojin ruwa da ya yi taƙaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kan wani fili da ake jayayya kansa a Abuja kwanakin baya. Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar da sanarwar ne a ranar Litinin tana mai ƙaryata labarin da ya yaɗu a kafafen sada zumunta. Adeh ta ce babu wani lamari da ya faru ko aka rubuta a koda ɗaya daga cikin wata ƙaramar hukumar da ke cikin birnin, don haka ta buƙaci jama’a da su yi watsi da labarin saboda ba shi da tushe. Ta ƙara da cewa irin waɗannan labaran...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja November 16, 2025 Manyan Labarai Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su November 16, 2025 Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara November 16, 2025
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa za ta dauki mataki idan idan Kwamitin Gwamnonin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ya amince da wani sabon kuduri da bai dace da Iran ba. Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran Kazem Gharibabadi, ne ya bayyana hakan, a gefen taron kasa da kasa mai taken ‘’yancin kasa da kasa na fuskantar barazana a martanin ga kungiyar tarayyar Turai a sahun gaba (Faransa, Burtaniya, da Jamus) da suka gabatar da wani sabon kuduri kan Iran a taron Kwamitin Gwamnonin IAEA na mako mai zuwa. “Ina fatan Tarayyar Turai za ta yi aiki da hankali kuma ba za ta gabatar da kudurin a hukumance ba, amma idan ta yi, Iran za ta yi gyara na...
    A wani lokaci yau Litini ce kwamitin tsaro na MDD, zai kada kuri’a kan daftarin kudirin zaman lafiya na shugaban Amurka Donald Trump na Amurka kan Gaza. Kafin hakan Amurka ta sha matsin lamba ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya don amincewa da daftarin kudurin na Trump. Amurkar da wasu kawayenta na kasashen Larabawa sun yi kira ga Kwamitin Tsaron da ya “yi sauri” ya amince da daftarin kudurin wanda ya amince da shirin zaman lafiya na Donald Trump kan Gaza. Qatar, Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Indonesia, Pakistan, Jordan, da Turkiyya sun bayyana goyon bayansu ga daftarin kudurin na Amurka wanda ya tanadi kafa kwamiti da zai kula da gwamnatin rikon kwarya a Gaza da rundunar kasa da...
    ’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu ’yan bindiga biyar tare da ƙwace tarin makamai a hannunsu a yankin Zuru–Tadurga da ke Jihar Kebbi. Rundunar ’yan sanda ta musamman da ta kama su, ta bayyana cewa, ’yan bindiga suna cikin waɗanda suka kai hare-hare a kan al’ummomin Zuru a kwanakin baya. Ta ƙara da cewa dukkansu ’yan asalin kauyen Birnin Tudu ne da ke cikin ƙananan hukumomin Bukkuyum da Gummi a Jihar Zamfara. Kakakin ’yan sanda a jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya ce makaman da aka ƙwato daga hannun ’yan bindigar sun haɗa bindigogi AK-47 guda 7 a wata ƙaramar gida guda 1 da harbi-ruga guda uku. ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 64 a Zamfara Da amincewar...
    Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya ce kasarsa na binciken wani jirgin sama da ya kawo ‘yan gudun hijirar Falasdinawa 153 kasar ba tare da takardun shiga ba. “Wadannan mutane ne daga Gaza wadanda, ta wata hanya, suka tsinci kansu cikin jirgin sama da ya tashi daga Nairobi (babban birnin Kenya) kafin su iso nan,” in ji Ramaphosa ga manema labarai, yana mai cewa hukumomin leken asiri da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida na kasar suna binciken lamarin. A ranar Alhamis, Afirka ta Kudu ta ba Falasdinawan su 153 mafaka ta kwanaki 90, duk da cewa an hana su shiga saboda sun gaza amsa tambayoyin da aka musu kuma fasfo dinsu ba su da tambarin tashi, ko tikitan komawa...
    Sheikh Ahmad Gumi ya yi martani kan kiraye-kirayen da ake yi na kama shi, inda ya ce masu yin kiran na yi ne domin kawar da rawar da yake takawa wajen magance matsalar ’yan bindiga a Arewa. Gumi, ya ce duk ganawar da yake yi da ’yan bindiga yana yi ne domin samar da zaman lafiya, kuma hukumomin tsaro sun san da komai. Ɗan Najeriya ya kashe mahaifinsa, ya yanki ƙannensa da wuƙa a Amurka Tsaro: Na kan yi kuka duk lokacin da na ji an kashe wani — Akpabio Maganar ta sake fitowa fili ne bayan da ya sake jaddada cewa tattaunawa hanya ce da za ta iya kawo ƙarshen tashin hankali a karkara. A cikin dogon saƙon da ya...
    Babban lauya kuma mai kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana (SAN), ya bai wa ƴan Nijeriya shawara da su kai Gwamnatin Tarayya ƙara don neman a mayar musu da kuɗin fansar da suka biya yayin da aka yi garkuwa da ƴan uwansu. Ya ce gwamnatin ta kasa sauke babban nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata na kare rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa. Falana ya yi wannan jawabi ne a lokacin buɗe sabuwar shekarar Shari’a ta Tsangayar Shari’a ta Jami’ar Yakubu Gowon da ke Abuja. Ya ce yawaitar garkuwa da mutane a sassan ƙasar nan ya nuna gazawar gwamnati wajen tabbatar da kariya kamar yadda kundin tsarin mulki da Yarjejeniyar Afrika kan Haƙƙin Dan Adam suka tanada. Ya kuma...
    Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95 An ba da labari cewa, yawan fasinjojin da aka yi jigilarsu ta jirgin kasa daga watan Janairu zuwa Oktoba na wannan shekara a kasar Sin ya kai biliyan 3.95, wanda ya karu da 6.4% idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata. Bayanai masu alaka da hakan sun nuna cewa, a farkon watannin goma na wannan shekara, adadin fasinjoji da jiragen kasa na Sin suka yi jigilarsu ya kai matsayi mafi girma a tarihi a wannan lokaci, kuma a ranar 1 ga Oktoba kawai, yawan fasinjojin ya kai fiye da miliyan 23.13, wanda ya kai matsayi mafi girma a tarihi a...
    Babban jirgin ruwan yaki mai dakon sojojin kasa da sauran kayan yaki da ake amfani da su a kan-tudu samfurin 076 irinsa na farko a kasar Sin mai suna Sichuan, ya koma tashar jiragen ruwa da ke birnin Shanghai da misalin karfe 5 na yamma a yau Lahadi, bayan kammala gwajinsa na farko a teku. Gwajin jirgin na kwanaki uku ya kunshi gwada ayyukan na’urar da ke sarrafa tafiyar jirgin da na’urorin lantarkinsa da sauran kayayyakin aiki, inda aka samu sakamakon da ake sa ran samu. Kasancewarsa sabon jirgin ruwan yaki na zamani na rundunar sojojin ruwa ta ‘yantar da jama’ar kasar Sin, jirgin ya kunshi sabbin fasahohin majaujawar mayen karfe mai aiki da lantarki, da fasahohin rike jiragen sama...
    Wani matashi mai shekaru 27, Chukwuebuka Eweni, ya shiga hannun ’yan sanda a birnin New Orleans na ƙasar Amurka, kan zargin kashe mahaifinsa har lahira tare da jikkata ’yan uwansa mata guda biyu a gidansu da ke unguwar Pebble. Mahaifin matashin malami ne a fannin kimiyyar kwamfuta a Jami’ar Southern ta New Orleans. Tsaro: Na kan yi kuka duk lokacin da na ji an kashe wani — Akpabio Gwamnatin Gombe ta bai wa alƙalai da Khadi-Khadi kyautar sabbin motoci 16 Iyayen matashin waɗanda asalin ’yan Najeriya ne, sun bayyana lamarin a matsayin abin mamaki da ban tsoro. Sun shaida cewar Chukwuebuka na fama rashin lafiyar ƙwaƙwalwa amma bai taɓa aikata wani mummunan abu ba. Rahotanni sun nuna cewa ɗaya daga...
    Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce gwamnati ce ke da alhakin samar da tsaro da haɗin kai a Jihar Filato da kuma Najeriya baki ɗaya. Ya ce babu wata ƙasa da za ta shigo don kawo zaman lafiya na dindindin a Najeriya, face ’yan ƙasa sun haɗa kai. ’Yan Bindiga A Kano: Sanusi II ya ziyarci Faruruwa, ya buƙaci a tsaurara tsaro Ba da yawuna PDP ta kori Wike ba — Muftwang Akpabio, ya yi wannan magana ne a filin Polo na Jos a ranar Asabar yayin taron tarbar sabbin mambobin da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a Jihar Filato. Ya kira jama’a da su goyi bayan ƙoƙarin samar da zaman lafiya tare da yin aiki don ƙarshen...
    Gwamnatin kasar ta DRC da kuma kungiyar ‘yan tawaye ta M23 sun rattaba hannu akan wasu takardu da su ka kunshi yadda za a kai ga samun zaman lafiya mai dorewa a gabashin kasar. A jiya Asabar ne dai bangarorin biyu su ka rattaba hannu akan  takardun a birnin Doha na kasar Qatar domin kawo karshe fadace-fadacen da ake yi a gabashin kasar da ya ci rayukan dubban mutane da kuma tilastawa wasu yin hijira a cikin shekara daya kacal. Karamin ministan harkokin wajen kasar Katar Muhammad Bin Abdulaziz Al-Khulaifi ya ce, rattaba hannu da bangarorin biyu su ka yi share fage ne zuwa ga zaman lafiya. Haka nan kuma ya ce; Shi zaman lafiya ba a iya tilasta shi...
    Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya buƙaci al’umma su ƙara kula da tsaro tare da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro, yayin da ’yan bindiga suka fara kai hare-hare a ƙauyukan da ke iyaka da Jihar Katsina. Sarkin, ya yi wannan kira ne yayin ziyarar jaje da ya kai wa al’ummar Faruruwa da ke Ƙaramar Hukumar Shanono a Jihar Kano. Gwamnatin Gombe ta bai wa alƙalai da Khadi-Khadi kyautar sabbin motoci 16 Ba da yawuna PDP ta kori Wike ba — Muftwang A baya-bayan nan ’yan bindiga sun kai hari yankunan, inda suka sace shanu tare da yin garkuwa da mutane. Sarki Sanusi, ya ce yawan hare-haren da ake fuskanta a yankin ya nuna cewa ana...
    Gwamnatin Jihar Gombe ta raba sabbin motoci ƙirar SUV guda 16 ga Alƙalai na Babbar Kotu da Khadi-Khadi na Kotun Shari’a domin taimaka musu wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata a fadin jihar. Motocin sun haɗa da motoci biyu ƙirar Toyota SUV samfurin 2025 da aka bai wa babban alƙal8 da Grand Khadi. Na kusa komawa APC – Gwamnan Taraba Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa Motocin guda 14 ƙirar GAC SUV samfurin 2025 da aka raba wa sauran alƙalai da khadi-khadi. Da yake miƙa motocin, Mataimakin Gwamna Mannasah Daniel Jatau, ya ce gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na ƙoƙari wajen samar da kayan aiki na zamani domin inganta ayyukan gwamnati, musamman a ɓangaren...
    Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ce zai fice daga jam’iyyar PDP tare da sauya sheƙa zuwa APC a hukumance a ranar Laraba, 19 ga watan Nuwamba. Ya bayyana haka ne yayin da yake duba aikin gyaran Filin Wasanni na Jolly Nyame da ke Jalingo a ƙarshen mako. Ba da yawuna PDP ta kori Wike ba — Muftwang Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa Yayin da yake magana da ’yan jarida, Gwamna Kefas, ya ce ya yanke shawarar ficewa daga PDP ne saboda nemo hanyar da zai amfanar da al’ummar Taraba. Ya ce: “Zan sauya sheƙa a hukumance daga PDP zuwa APC a ranar 19 ga watan Nuwamba. Wannan sauyi zai amfanar da al’ummar Taraba.”...
    “A shekaru goma da suka gabata, ayyukan ta`addanci da tashe-tashen hankula daga masu tsattsauran ra`ayi ya haifar da mummunan koma bayan tattalin arziki da na zamantakewar alummomin dake shiyyar, halin da daliban irin wadannan makarantu suke ciki yana bukatar kulawar gaggawa daga kungiyar ta ECOWAS, abin takaici irin wadannan makarantun allo suna daukar dalibai masu yawan gaske kuma akasari kananan yara daga shiyyar, to amma kuma ba a bai wa makarantun da daliban kulawar da ta kamata, wannan ta sanya kungiyoyin `yan ta`adda ke samun kofar kusantar su domin kwadaita musu shiga cikin kungiyoyin.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai APOSUN Ta Jaddada Aniyarta Na Daƙile Hada-hadar Haramtattun Kuɗaɗe November 16, 2025 Labarai NNPP Tana Da Ƙwarin Gwiwar Riƙe Kano...
    Gwamntin daliban ta kasar Afghnistan ta sanar da sauya akalar harkokin kasuwancinta ta hanyar iran da tsakiyar asiya, domin rage dogaro da kasar Pakistan a lokacin da zaman tankiya ya kara Kamari tsakanin makwabtan guda biyu da ya kai ga rufe iyakokinsu. A wani yunkuri na kewaye kasar Pakistan  da kuma kaucewa matsalolin da ake samu a iyakarta da Pakistan, kasar Afghanistan ta kara yawan lokacin aikewa da kayayyakinta zuwa tashar jigin ruwa ta chabahar ta kasar iran. Kakakin ma’aikatar kasuwanci ta kasar Afghanistan Abdus salam Jawad Akhundaze Ya ce a tsawon watanni 6 kasuwancinsu da iran ya kai dala biliyan 1.6. fiye da dala biliyan 1 na kayayyakin da take fitarwa ta hanyar Pakistan . Share 0 0 votes...
    Ya ci gaba da cewa, “an kama masu laifuka da dama ta hanyar bayanai da muke bai wa jami’an tsaro wanda hakan ya taimaka sosai wajen magance aikata laifuka a POS”, domin a cewarsa “sun sanya tsauraran matakai yadda ko da an tura kudi kafin a zo karɓa mambobinmu suna ganewa idan an tura kudin ta hanyar da ya dace, idan ba su gamsu ba sai a sanar da jami’an tsaro a zo a kama mutum, an kama wasu a Abuja, an kama wasu a Maiduguri da wasu sassa na kasar nan”.   Ya bayyana kungiyar a matsayin mai farin jini, inda ya ce dukkan jami’an Nijeriya sun santa kuma sun yi marhaban da ita ta hanyar kai musu ziyara...
    Gwamna Caleb Muftwang na Jihar Filato, ya ce ba da yawunsa jam’iyyarsu ta PDP ta kori Ministan Abuja, Nyesom Wike ba. Yayin da yake nisanta kansa daga matakin da PDP ta ɗauka na korar Wike daga jam’iyyar, ya yi gargaɗin cewa hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba. Fintiri ya yi watsi da korar Wike daga PDP Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa A jiya Asabar ce jam’iyyar ta kori ministan, wanda ya daɗe yana rigima da shugabancin jam’iyyar, da sakatarenta na ƙasa Samuel Anyanwu, da tsohon Gwamnan Ekiti Ayo Fayose yayin babban taronta na ƙasa tana mai zargin su da yi mata zagon ƙasa. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa...
      Amfani da jami’an tsaro: Abu na farko dai dole ne kungiyoyi su yi aiki tare da yansanda, NSCDC, da jami’an tsaro na sirri wajen tsara tsare-tsaren tsaro a ranar da za su buga wasa, domin kuwa Bahaushe na cewa, “tun za a, ake shiri ba sai an dawo ba”, hakazalika yana da mahimmanci a tura isassun masu aikin kwantar da tarzoma (ba yansanda kawai ba) don sa ido kan magoya baya, lura da wuraren shiga/fita, da kuma taimakawa wajen rage turmutsitsi yayin wasa.   Amfani da CCTV: Yawancin filayen wasa na gasar NPFL ba su da isasshen tsarin kyamarar CCTV, a cikin filayensu cewar bincike, samar da kyamarori masu sa ido na iya rage tashin hankali a cikin...
    Da yake magana da manema labarai, Ahmed ya ce ficewar ba za ta raunana jam’iyyar ba, amma dai, ya yi fatan alheri ga ‘yan jam’iyyar da suka fice.   Ahmed ya ƙara da cewa, NNPP tana da ƙwarin gwiwar riƙe Kano da kuma lasheh kujera a Jigawa, Kaduna, da sauran jihohi. Ya kuma yi ikirarin cewa, an ƙwace nasarar da jam’iyyar ta samu ne a Taraba a zaben da ya gabata wanda ke nuna yiwuwar samun nasara a shekarar 2027. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Nazari Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna? November 16, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7 November 15, 2025 Manyan Labarai Sanusi...