Khalil al-Hayya: Mun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin
Published: 10th, October 2025 GMT
Shugaban kungiyar Hamas a Zirin Gaza kuma shugaban tawagar Falasdinawa Khalil al-Hayya ya sanar da cimma yarjejeniyar kawo karshen yaki da cin zarafin al’ummar Palasdinu, da fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin a zirin Gaza, gami da janye sojojin mamaya, shigar da kayan agaji, bude mashigar Rafah ta bangarori biyu, da musayar fursunoni.
Al-Hayya ya bayyana cewa kungiyar ta samu lamuni daga masu shiga tsakani da gwamnatin Amurka, yana mai jaddada cewa dukkan bangarorin sun jaddada cewa an kawo karshen yakin.
Ya bayyana cewa yarjejeniyar ta hada da sakin fursunoni 250 da ke zaman daurin rai-da-rai, fursunoni 1,700 daga zirin Gaza da Isra’ila ta kama bayan 7 ga watan Oktoba, da kuma sakin dukkan yara da mata.
A cikin jawabin nasa, Al-Hayya ya ce, duniya ta tsaya tsayin daka kan sadaukarwa, dagewa, da hakurin da al’ummar zirin Gaza suke yi. Ya yi nuni da cewa al’ummar yankin sun yi juyiriya da duniya ba ta taba ganin irinta ba, inda suka fuskanci zalunci, da mummunan kisan kiyashi na makiya.
Ya kara da cewa al’ummar Gaza sun tsaya tsayin daka kamar tsaunuka, kudurinsu bai gushe ba wajen tinkarar kisa, kauracewa gidajensu, yunwa, da asarar dangi da gidaje. Ya jinjina wa shahidan da suka yi sadaukarwa baki daya, musamman shugabanni Ismail Haniyeh, Saleh al-Arouri, Yahya Sinwar, da Mohammed Deif.
Al-Hayya ya bayyana godiyarsa da jinjina ga kasashe da dakarun da suka bayar da gudunmawa daga Yemen, Labanon, Iraki, zuwa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da kuma ‘yantattun mutane a fadin duniya da suka tsaya tsayin daka wajen nuna goyon baya ga Gaza, musamman wadanda suka halarci ayarin tallafi da ‘yanci ta kasa da ruwa, da duk wanda ya ba da gudummawa wajen bayyana kalmar gaskiya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministan mai na Nijar ya gana da Jakadan Iran a Yamai October 10, 2025 Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Trump ya gabatar October 10, 2025 Guterres ya jaddada wajabcin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza October 10, 2025 Madagascar: An Yi Kiran Gudanar Da Yi Wa Shugaban Kasa Zanga-zanga October 9, 2025 Jagora: A Yi Amfani Da Hanyoyin Sadarwa Na Zamani Domin Koyar Da Muhimmancin Salla October 9, 2025 An Fara Aiki Da Zango Farko Na Tsagaita Wutar Yaki A Gaza October 9, 2025 Shugaban Kasar DRC Ya Kira Yi Takwaransa Na Rwanda Da Ya Daina Taimakon M23 October 9, 2025 Jagora: Dole Ne Ga Hukumomin Da’awa Da Malamai Su Kula Da Batun Tsayar Da Sallah A Tsakanin Al’umma October 9, 2025 Babban Kwamandan IRGC Ya Jaddada Batun Wurga Makiya Cikin Mummunar Nadama October 9, 2025 Hamas: An Cimma Yarjejeniyar Karshen Kan Dakatar Da Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Gaza October 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yarjejeniyar tsagaita al Hayya ya Al Hayya ya
এছাড়াও পড়ুন:
UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin Lebanon
Wani mai magana da yawun rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (UNIFIL) ya tabbatar da cewa Isra’ila ta gina katanga kan iyakar da ta ratsa zuwa cikin yankin kasar Lebanon kusa da garin Yaroun, abin da tawagar ta bayyana a matsayin keta kudurin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701.
“Isra’ila ta shafe shekaru da dama tana gina katanga a gefen Layin da aka Shata da ya raba yankunan Falastinu da Isra’ila ta mamaye da Lebanon, amma a cikin wannan yanayi katangar Isra’ila ta ratsa layin da ya raba bangarorin biyu,” in ji mai magana da yawun UNIFIL. “Don haka muna nuna rashin amincewa da wannan mataki, Wannan, a bayyane ya keta kuduri mai lamba 1701 da kuma hurumin kasar Lebanon.” Inji shi.
Dakarun Masu Sanya ido kan zaman lafiya a kudancin kasar Lebanon UNIFIL sun yi nazarin wurin kuma kuma tabbatar da cewa katangar ta ketare Layin da aka shata.
A cewar UNIFIL, sun gano cewa katangar tana cikin kasar Lebanon kuma ta kai kimanin mita murabba’i 4,000 a cikin kasar Lebanon”. Mai magana da yawun rundunar ya kara da cewa, tawagar ta sanar da sojojin na Isra’ila a hukumance game da keta dokar da suka yi, inda suka mayar da martanin cewa za su dubi lamarin.
UNIFIL ta jaddada cewa za ta ci gaba da bin diddigin lamarin, da kuma ci gaba da Magana tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa don tabbatar da cewa an kiyaye doka da kuma yin aiki da kudiri mai lamba 1701.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru Mafaka Ta Wucin Gadi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci