Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)
Published: 10th, October 2025 GMT
Ga alkawarin, komai da Allah Ya yi wa wani, Allah Ya fada. Allah bai boye komai ba, sai abin da ya yi ga Annabi Muhammadu (S.A.W.), nan ko ba a fada ba, amma kowane annabi komai matsayinsa in ka duba sai ka ji sirrin da aka yi da shi. Yanzu game da wannan ma’aiki da annabawan da duk Allah ya tara su, ga abin da Allah Ya ce (ya ku) Annabawa, idan na ba ku littafanku da kyawawan dabi’u da hikima da ma’arifanku (ai, misali, an ba ka wukar yanka da takobin yanka da tagwayen masu ke nan).
Wani malami yake cewa in dai lamarin Manzon Allah (S.A.W.) ne wani baki ma bai iya fada, kamar za ka iya cewa komai Allah kan dauke shi yadda ya dauke shi, amma idan abin Manzon Allah ne Allah bai daukar shi da wasa.
Ayar ta yi gargadi a kan kar wani (a cikin Annabawa) ya juya baya ga wannan alkawarin da Manzon Allah ya zo da shi, ya ki tashi daga annabtarsa, ya ki bin Manzon Allah. To ka ga ashe Manzon Allah (S.A.W.) shi ne Annabin Annabawa, shi ne ma’aikin ma’aika, manzon Allah shi ne mafi girman duk wani mai girma na halittar Allah.
Manzon Allah (S.A.W.) shi ne mafi girman wani mutum da tarihi ya sani, shi wannan masanin falsafa da ya fadi wannan kusan ya karanta tarihin duniya tun daga farko har karshe, yana da tarihin duniya domin malami ne masanin falfasafa da ya yi bincike kwarai kuma ba shi da wani addini da zai hana shi karanta wannan. Ya nuna idan muna son mu karanta wani abu watakila muna tsoro saboda addini, shi ko ba shi da wannan (addini) ma, yake cewa “Manzon Allah (S.A.W.) shi ne mafi girman wani dan Adam da tarihi ya sani, shi ne wanda ya juya halitta ya kawo wa halitta canji, ya kawo mata canji cikin addini da yadda duk ake addini, a zo da addini ta kowane fanni sai Manzon Allah (S.A.W.).
Masanin falsafan ya ce Manzon Allah ya kawo canji a cikin addini, ya kawo canji cikin siyasa, da tsarin rayuwa, da tsarin kasa, da tsarin jama’a. Manzon Allah (S.A.W.) Annabi ne, ma’aiki ne daga Allah, Annabi ne, ma’ana malami ne wanda ya yi karatu a Hadarar Allah, ma’aiki ne, ma’ana ma’aiki ne ba kamar yadda muke dauka kamar wani dan sako ba, saboda galibi wasunmu abin da muka sani da an batun manzo sai a dauka dan aike ne kawai mai isar da sako ko ya karanta, amma ma’iki abu ne mai girma na daga annabawa, mutum ne da ya yi fikiri, ya yi tunani har ya samu saduwa a cikin hadarar Allah, har ya zama ma’aiki a hadarar Allah.
Yanzu duk abin da zai fada Hadarar Allah ce ta sa shi, siyasa ce da Hadarar Allah yake fada, Hadara ce ta sa shi ya fada, su sauran annabawa dukkansu Allah ya bar masu ladabin su isar da sakon wanda da ma su ma’aikan Allah ne, Annabi Isa ne ya dauke masa wannan ya ba shi izini, shi Annabi Isa ne zai fadi abin kai-tsaye daga Hadarar Allah, cewa Allah ne Ya ce ba wani ma’aiki ko wani abu ba, Annabi Isa ne kadai ke da wannan, amma sauran Annabawa dukanninsu za su ce ma’aikin Allah ne, kar ka za ci wani abu ne na wulakanci, a’a abu ne da ke da girma, saboda Manzon Allah ya yi fikiri, ya yi tunani ya yi halwar da duk wani mai takamar halwa zai yi, ya shiga inda duk wani dan tunani ke takamar ya shiga.
Annabi (SAW) ya shiga kogon hira ya yi adadin kwanaki, ya yi adadin watanni, duk malamai sun tafi ba sallah ya je ba, tahamusi ya rika yi, kamar yanzu mutum ya shiga kogo na dutse ka kulle kanka na tsawon kwanaki arba’in (40) ai ka cika namiji bare ka tafi daji-dajin ma ka hau dutse, dutsen ma ka shiga cikin kogo, Allah ya san me ye a cikin kogon nan. A zamani irin na wannan lokaci, har Allah ya ba Manzon Allah (SAW) abin da ya ba shi, dan haka mun gode wa Allah.
Duk annabawa fa ba wasa ba ne, kowane a cikinsu sai ya yi tunanin nan. Annabi Ibrahim ya yi tunanin nan, Allah Ya yaye masa malakutus samawati Wal’ ard. Annabi Musa (AS) wannan ciwon da ya yi shekaru arba’in (40) a cikin yawon neman Allah ya yi, amma duk da haka sai ka ga ya iya abin da Allah ya ba shi ga shi da wani a cikin jama’arsa ko zamaninsa zai yi wani tunani babba har ya iya gano wani abin da al’imma za ta ki yarda da wannan abu in ya yi wasa ma ta kashe shi. Amma Manzon Allah da tafakkurinsa zikirinsa da shiga cikin kogo da shafewarsa da haduwarsa da mudalakin hakika da Manzon Allah (S.A.W.) babu wani dan halitta da ya isa ya ce zai yi irin wannan har ya zo da abin da annabi ya zo da shi (S.A.W.), babu shi.
Shehi babbanmu, Ibn Arabi Hatimi duk abin da zai rubuta a cikin Futuhatil Makiyya da Khususil Hikam zai ce “ni fa magaji ne na manzon Allah, ban yi kusa ma da Manzon Allah (S.A.W.) ba, gado ne”, kuma da gaske yake yi. Shehu Ibrahim Inyass (R.A.) ya ce duk abin da ya fada, ya fada ne saboda shi Hadimin Manzon Allah ne, ya ce Manzon Allah ne ya ba ni, ya yi mani wata kyauta ta daban, bayan baiwar can, ya kuma ba ni abin da ma bai ba halitta ba, amma komai girman abin na Shehu Ibrahim ya ce Manzon Allah ne ya ba shi.
Duk irin wannan ilimi na Sayyidina Ali wanda ya bugi kirji ya ce ni ne digon nan na karkashi ba’un, amma duk wanna sunansa kofar ilimin Manzon Allah, amma gidan ilimi shi ne Manzon Allah (S.A.W.), saboda haka mu daina tsoro, malamai na musulunci su daina tsoro, ba wani wanda zai zo da wani karatu, ba wani wanda zai fito da wani abu wanda ya fi karfin na Annabi din nan (S.A.W.), a’a duk abin da zai zo da shi a cikin na Manzon Allah (S.A.W.) ne.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: a Hadarar Allah duk wani mai ya yi tunani da Allah Ya da Allah ya Da Allah Ya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
An sake tabbatar wa ma’aikatan Gwamnatin Tarayya FG da suka yi ritaya cewa za a biya su wani bangare na kudaden ariyas a cikin wannan watan, kamar yadda hukumomin da abin ya shafa suka yi alkawari.
Mataimakin Sakataren ƙungiyar masu karɓar fansho ta ƙasa, Alhaji Ahmed Gazali, ya bayar da wannan tabbaci yayin da ake tattaunawa da shi ta wayar tarho daga Abuja.
Alh. Ahmed Gazali, ya yi bayanin cewas daraktan dake kula da kudade na ofishin akanta janar na tarayya ya tabbatar da daukan matakin hakan na biyan kudaden.
Ya bayyana fatan ganin kudirin FG na gaggauta biyan kudade, domin dakatar da duk wata zanga zanga wanda hakan bai dace ba ga ma’aikatan da suka yi ritaya domin bata martaban kasan nan.
Hakan kuma masu karban fensho a Radion Tarayya na kasa FRCN da Gidan talabijin na kasa NTA dake Kaduna sun nuna damuwarsu game da zargin da ake yi cewa ana kokarin wulakanta shugabannin kungiyar ma’aikatan da suka yi ritaya karkashin jagorancin kwamaret Munkaila Ogunbote.
DAGA SULEIMAN KAURA