Farfesa Jeffrey Sachs na jami’ar Columbia, ya yaba wa nasarorin da Sin ta samu, inda ya ce, “shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, wani shiri ne mai ban mamaki kuma na musamman.”
Farfesa Sachs ya fadi hakan ne a kwanan nan, yayin da wakiliyar rukunin gidan rediyo da talibijin kasar Sin wato CMG ta zanta da shi.
Ya kuma bayyana cewa, kamar yadda shugaban kasar Xi Jinping ya fada a karon farko, yayin gabatar da wannan shawara, tushen ta ya samo asali ne daga hanyar kasuwanci ta hanyar siliki, hanyar dake da tarihin fiye da shekaru dubu biyu tsakanin yankin gabas da yamma. Ya ce, “Idan kina nazarin tattalin arziki kamar yadda nake yi, za ki yi imanin cewa, ainihin ciniki shi ne samun moriyar juna, da habaka al’adu, da samar da ingantattun kayayyaki, wanda ke amfanar mutane daga sassa daban-daban na duniya, to za ki amince
cewa ciniki shi ne tsarin gaskiya na samun riba ga kowa. Ina goyon bayan wannan ra’ayi na hadin kai, kuma na yi imanin cewa yana da fa’ida mai yawa. Shirin Sin na tabbatar da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ cikin hadin gwiwa, ya yi kokari sosai a fannin inganta hadin kai da kara zurfafa mu’ammala.” (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA

Daga
Birnin Sin Li Qiang Ya Halarci Bikin Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Koriya Ta Arewa
October 11,
2025 
Daga Birnin Sin Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza October 10, 2025

Daga Birnin Sin Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya October 10, 2025
উৎস: Leadership News Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa
A yau Jumma’a 10 ga watan Oktoba, an kaddamar da wani shiri na aikin hadin gwiwa mai lakabin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” na rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) na shekarar 2026 a birnin Beijing.
Shen Haixiong, babban darektan CMG, ya gabatar da jawabi a wajen taron, inda ya bayyana cewa, CMG ya samu damar zamowa kan gaba a fagen yada labarai na kasa da kasa bisa kayayyakin aiki da ma’aikata, kuma shi ne muhimmin dandali na tallata kayayyakin kasar Sin. Kamfanin a shirye yake ya dauki shirin a matsayin wata damar yin aiki kafada da kafada da abokan kawance daga kowane bangare na rayuwa, tare da rubuta sabon babi a fagen gina kasa mai kunshe da kayayyakin kamfanonin da suka kasance a kan gaba. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA

Daga
Birnin Sin Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka
October 10,
2025 
Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata October 10, 2025

Daga Birnin Sin Sin Ta Gabatar Da Shawarwari Shida Game Da Karfafa Tsarin Shari’a Da Inganta Shugabanci A Duniya October 10, 2025