Falasdinawa na murna da tsagaita wutar hare-haren Isra’ila a Gaza
Published: 9th, October 2025 GMT
Falasdinawan da ke Gaza da Isra’ila ta shafe sama da shekara biyu tana kai wa hare-hare sun nuna jin dadi da farin ciki bayan sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta da nufin kawo karshen yakin.
Yayinda labarin yarjejeniyar ya yadu a cikin yankin da aka kewaye, mazauna Khan Younis a kudancin Gaza sun fito tituna suna murna da fatan wannan zai zama farko zaman lafiya daga hare-haren Isra’ila.
“Alhamdulillah da wannan dakatar da fada, karshen zubar da jini da kashe-kashe… duk Gaza na cikin farin ciki,” in ji Abdul Majeed Abd Rabbo, mazaunin Gaza.
Yarjejeniyar tsagaita wutar, wadda Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da ita a daren Laraba, na nuni da mataki na farko na shirin kawo karshen yakin da ya dauki shekaru biyu.
Yarjejeniyar na bukatar sakin fursunonin Isra’ila da ke hannun Falasdinawa a Gaza a madadin sakin Falasdinawa da ke hannun Isra’ila, yayin da dakarun Isra’ila za su ja da baya zuwa “layin da aka amince da shi,” a cewar Trump.
“Wannan lokaci ne da ake dauka a matsayin na tarihi, wanda Falasdinawa suka dade suna jira,” in ji Khaled Shaat, wani mazaunin Gaza.
“Farin cikin da muka fara gani a tituna alama ce ta samun sauki daga kisan kiyashi da kashe-kashe.”
Gidan talabijin na Al Jazeera ya ce akwai alamun sauki ga jama’ar Gaza gaba daya. “Wannan lokaci ne na tarihi,” in ji shi.
Bayan fama da yunwa da Isra’ila ta jawo a yankin tsawon watanni, hankalin kowa ya koma kan lokacin da za a fara raba taimako, abinci da magunguna a matakin da aka gani a lokacin dakatar da fada na baya.
A daren Laraba dai, a karon farko Falasdinawa sun yi barci mai natsuwa da ba a saba da shi ba, yayin da hare-haren sama da suka zama ruwan dare suka ragu sosai.
Sai dai duk da haka, hukumar kare rayuka ta Gaza ta sanar da da Isra’ila ta kai musu wasu hare-hare bayan sanar da yarjejeniyar, ciki har da “jerin munanan hare-hare” a birnin Gaza.
Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce zai kira gwamnatinsa a ranar Alhamis don amincewa da mataki na farko na yarjejeniyar, yana mai cewa wannan rana ce mai girma ga Isra’ila.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Falasdinawa Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Soja ya kashe matarsa, ya hallaka kansa a Jihar Neja
Wani soja mai muƙamin Las Kofur ya ɗirka wa matarsa harbi har lahira sannan ya kashe kansa a Jihar Neja.
Las Kofur Akenleye Femi da ke aiki a Bataliya ta 221, ya yi wannan aika-aika ne a Barikin Sojoji na Wawa da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja.
Muƙaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soja ta 22 da ke Ilorin, Kyaftin Stephen Nwankwo, ne ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce abin ya faru ne a ranar 11 ga Oktoba, 2025.
Ya ce mutuwar sojan da matarsa ta haifar da tashin hankali a cikin sansanin soja, inda mazauna wurin suka shiga ɗimuwa da mamaki kan abin da zai iya jawo irin wannan lamari.
Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoni Zaɓen Kamaru: Tchiroma Bakary na da kwarin gwiwa a yayin da ake jiran sakamako“An gano gawar Last Kofur Femi da matarsa ne a cikin dakinsu da ke Block 15, Room 24 na Corporals and Below Quarters a Wawa Cantonment,” in ji Kyaftin Nwankwo.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa sojan yana kan aiki a cikin sansanin kafin ya nemi izinin zuwa gida domin wasu bukatun kansa, sai daga bisani aka gano gawarsu a gida.
Kyaftin Nwankwo ya ce an ajiye gawar mamatan domin ci gaba da bincike, kuma rundunar sojan na aiki tukuru don gano musabbabin lamarin.
Rundunar Soja ta Najeriya ta bayyana matuƙar baƙin cikinta kan wannan abin takaici, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalai, abokai da abokan aikin mamatan.
Kwamandan Rundunar, Birgediya Janar Ezra Barkins, ya sha alwashin gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru, tare da ɗaukar matakan da za su hana faruwar irin haka a nan gaba.