Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka Rusa A Arewacin Yankin
Published: 10th, October 2025 GMT
Falasdinawan da HKI ta kora daga gidajensu a birnin Gaza sun kama hanyar komawa gidajensu a birnin Gaza dake arewacin yankin
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran reuters na cewa ya zuwa tsakiyar rana a yau jumm’a sojojin HKI sun janye makamansu daga babban titi wanda ya taso daga arewacin zirin Gaza zuwa kudancin yankin , wanda kuma ake kira Titin Rasheed.
A wani bangare kuma gwamnatin HKI ta fara bayyana sunayen Falasdinawa wadanda suke tsare da su, saboda musayarsu da fursinoni yahudawa wadanda Hamas take tsare da su. Wanda yake yake da cikin shirin. Yahudawan sun bayyana sunayen falasdinawa 25 wadanda suke cikin wadanda za’a saka. Yahudawan sun bayyana cewa daga cikin sunayen babu Marwan Barguthe da kuma Ahmad Saadat, manya-manyan falasdinawa wadanda suka fi shekaru 40 yahudawan suna tsar da su.
Ana saran na da sa’o’ii 72 za’a saki fursinoni yahudawa 48 wadanda suke tsare a hannun kungiyar Hamas, tare da falasdinawa kimani 2000 da yahudawan zasu saka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Rahotanni : Isra’ila ta fara janye dawa wasu yankuna na Gaza October 10, 2025 Amurka ta kakaba wa wasu kamfanoni 50 takunkumi saboda sayen man Iran October 10, 2025 Isra’ila ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki October 10, 2025 Mohajirani: Iran na goyon bayan shawarar Falastinawa kan batun dakatar da bude wuta October 10, 2025 Khalil al-Hayya: Mun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin October 10, 2025 Ministan mai na Nijar ya gana da Jakadan Iran a Yamai October 10, 2025 Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Trump ya gabatar October 10, 2025 Guterres ya jaddada wajabcin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza October 10, 2025 Madagascar: An Yi Kiran Gudanar Da Yi Wa Shugaban Kasa Zanga-zanga October 9, 2025 Jagora: A Yi Amfani Da Hanyoyin Sadarwa Na Zamani Domin Koyar Da Muhimmancin Salla October 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11
’Yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutum 11 mazauna garin Isapa da ke kusa da Eruku a Ƙaramar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara.
Harin ya faru ne sa’o’i kadan bayan sakin wasu masu ibada da aka yi garkuwa da su suna tsaka da ibada a coci.
An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a KebbiA cocin CAC da ke Ekuru, ana gudanar da bikin godiya domin murnar ’yantar da mambobi 18 da aka yi garkuwa da su kusan wata guda da ya gabata, sai ’yan bindiga suka kutsa suka yi garkuwa da mutum 38 bayan sun harbe uku har lahira.
Sabon harin, wanda ya faru da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin Litinin, an ce ’yan bindiga kimanin 20 zuwa 30 ne suka kai shi.
Bayanai sun una cewa maharan su rika yin harbi ta ko’ina yayin da suke kutsa cikin garin, lamarin da ya sa mutane suka ranta a na kare.
Wata tsohuwa ta ji rauni sakamakon harbin kan mai uwa da wabi.
Wani jagoran al’umma da bai amince a bayyana sunansa ba, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce: “Mutane 11 aka yi garkuwa da su, bakwai daga cikin su ’yan gida ɗaya. Waɗanda aka sace sun haɗa da mace mai juna biyu, masu shayarwa biyu da kuma kananan yara.”
Shaidar y ace sunaye mutanen sun hada da Talatu Kabiru, 20, Magaji, 6, Kande, 5, Hadiza, 10, Mariam, 6, Saima, 5, Habibat (mahaifiya), Fatima Yusufu (mahaifiya), Sarah Sunday, 22 (mai juna biyu), Lami Fidelis, 23 (uwa mai shayarwa) da kuma Haja Na Allah, ita ma uwa mai shayarwa.
Shaidun gani da ido sun ce ’yan bindigar sun bi wasu sassa na garin, inda suka bar alamun ramukan harsashin harbe-harbe a bangon gidaje da ƙofofi.
An gano harsashin bindiga AK-47 da aka harba daga wurare da dama bayan ’yan bindigar sun ja da baya tare da mutanen da suka yi garkuwa da su.
Lamarin ya haifar da tsananin tashin hankali a yankin da makotan garuruwa, yayin da jami’an tsaro da ’yan sa-kai ke ƙara ƙoƙari wajen gano maharan da ceto waɗanda aka sace.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kwara, Adekimi Ojo, ya tabbatar da lamarin ga yana mai cewa: “Eh, lamarin ya faru, amma ba zan iya cewa komai da yawa ba yanzu ba. Ina gab da shiga Isapa daga Ilorin. Zan ba da rahoto idan na isa.”
A yanzu haka dai Najeriya na fuskantar ɗaya daga cikin mafi munin matsalolin tsaro a tarihin ta. Hakan dai ya haifar da rufe makarantu da dama, musamman a Arewacin ƙasar.