Mohajirani: Iran na goyon bayan shawarar Falastinawa kan batun dakatar da bude wuta
Published: 10th, October 2025 GMT
Mai Magana da yawun gwamnatin Iran Fatemeh Mohajerani ta tabbatar da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar Palastinu a gwagwarmayar neman ‘yanci da mutunci.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Mohajerani ta ce Iran za ta goyi bayan duk wani mataki ko wani shiri da zai kai ga dakatar da kisan kiyashin da ake yi a Gaza, da janyewar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila, da shigar da kayayyakin jin kai, da sakin fursunonin Falasdinu, da kuma tabbatar da hakkinsu na yau da kullun.
Ta yi nuni da cewa goyon bayan Iran ga al’ummar Palasdinu “ba matsayi ne na siyasa kawai ba, a’a yana dogara ne akan imani da ‘yancin al’ummar Palasdinu da kuma tsayin daka wajen kin amincewa da zalunci da mamaya.” Ta nanata cewa tsayin dakan da al’ummar Palasdinu suke yi ya dace kuma yana wakiltar wani muhimmin bangare na tsarin maido da ‘yancin Falasdinu.
Mohajerani ta kara da cewa dakatar da laifuffukan da ake yi a Gaza “ba shi ne karshen lamarin ba, dole ne a bi kadun lamarin a gaban kotunan duniya domin hukunta wadanda suka yi umarni da aikata laifukan yaki, da kisan kare dangi, da cin zarafin bil’adama,” tana mai kira ga kasashen duniya da su dauki nauyin bin kadun wannan shari’a.
A baya ma dai ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da goyon bayan Tehran ga duk wani mataki ko wani shiri da ya hada da dakatar da yakin kisan kiyashi da ake yi wa Palastinawa, tare da bayyana bukatar dukkanin bangarorin da su yi taka tsantsan kan abin da ta bayyana a matsayin yaudara irin ta yahudawan sahyoniyawa da yadda suke keta yarjejeniyoyin kasa da kasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Khalil al-Hayya: Mun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin October 10, 2025 Ministan mai na Nijar ya gana da Jakadan Iran a Yamai October 10, 2025 Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Trump ya gabatar October 10, 2025 Guterres ya jaddada wajabcin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza October 10, 2025 Madagascar: An Yi Kiran Gudanar Da Yi Wa Shugaban Kasa Zanga-zanga October 9, 2025 Jagora: A Yi Amfani Da Hanyoyin Sadarwa Na Zamani Domin Koyar Da Muhimmancin Salla October 9, 2025 An Fara Aiki Da Zango Farko Na Tsagaita Wutar Yaki A Gaza October 9, 2025 Shugaban Kasar DRC Ya Kira Yi Takwaransa Na Rwanda Da Ya Daina Taimakon M23 October 9, 2025 Jagora: Dole Ne Ga Hukumomin Da’awa Da Malamai Su Kula Da Batun Tsayar Da Sallah A Tsakanin Al’umma October 9, 2025 Babban Kwamandan IRGC Ya Jaddada Batun Wurga Makiya Cikin Mummunar Nadama October 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: goyon bayan
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Bukaci HKI Ta Aiwatar Da Yarjeniya Da Gaza Kamar Yadda Take
Masu zanga-zanga a nan Iran a jiya jumma’a a manya-manyan garuruwan kasar bayan sallar Jumma’a sun bayyana goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu a Gaza, sannan sun bukaci HKI ta aiwatar da yarjeniyar da ta cimma da kungiyoyi masu gwagwarmaya. Har’ila yau sun bukaci a gaggauta shigo da abinci da magungunacikin zirin Gaza.
Tashar talabijin talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga zangar wadanda suka hada da mata da maza, malaman addini, daliban jami’o’i da sauransu suna tattaki daga dandalin inkilab zuwa dandalin azadi.
Har’ila yau sun rera wakoki na goyon bayan masu gwagwarmayar, dauke da hotunan shahidai da kuma shuwagabannin kawancen masu gwagwarmaya a yankin.
An gudanar da jerin gwanon a cikin manya manyan biranen kasar wadanda suka hada da Tabriz, Ahvaz, Shiraz, Bandar Abbas, Isfahan, da Gorgan.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka HKI Ta Kashe Mutane 19 A Gaza Duk Tare Da Tsagaita Wuta October 11, 2025 Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Shirin Zaman Lafiya Da Ya Hada Da Kawo Karshen Kisan Kiyashi A Gaza October 11, 2025 Faransa Da Jamus Da Kuma Birtaniya Sun Bayyana Aniyarsu Ta Ganin An Farfado Da Tattauna Da Iran October 11, 2025 Kungiyoyin Falasdinawa Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 11, 2025 Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya October 11, 2025 Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta October 11, 2025 Putin: Natanyahu Yana Son Warware Matsaloli Da Iran Cikin Lumana Ba Tare Da Yaki Ba October 10, 2025 Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha October 10, 2025 Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa October 10, 2025 Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka Rusa A Arewacin Yankin October 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci