Leadership News Hausa:
2025-10-13@13:34:44 GMT

Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara

Published: 11th, October 2025 GMT

Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara

Ya kara da cewa, ana ci gaba da kokari don ganin an iske masu yin kiwon shanu a kasar nan, domin fadakar da su kan muhimmancin rungumar wannan tsari na zamani.

 

Sai dai, ya yi nuni da cewa; wasu al’adu na haifar da tarnaki a tsakanin wasu masu kiwon a kasar na rungumar wannan tsarin.

 

“Na ga wasu gidajen gona da ake yin irin wannan dabara ta zamani, sannan kuma ana bayar da kulawar da ta kamata; wanda hakan ya sanya ake iya samar da litar madarar shanu daga tsakanin lita 15 zuwa 30,” in ji Jatau.

 

“Akwai wasu Fulani Makiyaya ‘yan kalilan da suka rungumi wannan tsari, misali a Jihar Bauchi; inda wani makiyayi ya rungumi wannan tsari tare kuma da amfanarsa yadda ya kamata,” a cewarsa.

 

“A lokacin da muka gudanar da ayyukanmu, wasu daga cikin Fulani Makiyaya, sun zo sun saurari wannan batu na dabara ta zamani tare da shanunsu, mun kuma aiwatar da tsarin a kan shanun nasu, inda daga baya suka ga yadda madarar shanunsu ta kara habaka,” in ji shi.

 

Jatau ya kara da cewa, suna kan ci gaba da bai wa Fulani Makiyaya kwarin guiwa, kan rungumar wannnan tsari, sai dai, wasu na fuskantar kalubale na kula da shanunsu da aka dora su a kan tsarin.

 

“A wasu kasashen na Afirka za ka cewa, Makiyayin da suka rungumi wannan tsari, na da shanu uku ne kacal da daukacin iyakansa suka dogara a kansu, wanda hakan ke ba su dama a kullam na samar da litar madara daga tsanakin 15 zuwa 20, “ a cewarsa.

 

Ya kara da cewa, hakan ya sanya a kullum suke samar wa da kansu dimbin riba, wanda kuma hakan ya sa ba su dogaro da aikin gwamnati ba kwata-kwata.

 

Ya yi nuni da cewa, idan har a raba daya za ka sayar da litar madara daya kan Naira 1,000, a wata za ka iya samun kudin shiga da suka kai Naira miliyan 1.8 da shanu uku kacal.

 

Ya ci gaba da cewa, da wannan ribar kadai za ka iya ci gaba da ciyar da shanun da lula da lafiyarsu da biyan ma’aikatan da ke kula da su da kuma daukar sauran dawainiyar kula da iyalanka.

 

Ya bayyana cewa, duba da cewa; ana fuskantar matsalar wajen da dabbobi za su yi kiwo a kasar nan, amma idan Fulani Makiyaya suka rungumi wannan tsari, hakan zai rage yawan samu rikice-rikice a tsakanin manoma da Fulani Makiyya a kasar.

 

Kazalika, ya sanar da cewa; idan masu kiwon suka dauki wannan tsari za a samu cewa, alfanun da za su samu ya dara irin na kiwon gargajiya da ake yi a cikin kasar.

 

Jatau ya bayyana cewa, wannan tsarin abu ne da ke da tsawon tarihi a kasar nan, domin an faro shi ne tun a shekarar 1949; tun bayan da aka dauki nau’in na jinsin daga wata gona da ke garin Shika a birnin Zaria, aka kuma kai shi zuwa cibiyar gudanar da bincike kan lafiyar dabbobi ta Bom.

 

Sai dai, ya bayyana cewa; rashin ci gaba da bibiyar wannan tsare-tsaren daga bangaren gwamnati, hakan ya haifar da koma baya ga wannan tsair.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Noma Da Kiwo Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina October 3, 2025 Noma Da Kiwo Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo October 3, 2025 Noma Da Kiwo Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi September 27, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: rungumi wannan tsari Fulani Makiyaya

এছাড়াও পড়ুন:

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

Garin Girfa (cinnamon), Garin kaninfari Clove)

 

Yadda za a hada:

Za’a samu garin girfa kamar cokali 5 garin kaninfari cokali 7 za a hade waje daya, sai a rika diban rabin karamin cokali ana zubawa a ruwan shayi ana sha sau 2 a rana ayi kamar sati daya.

Za a samu waraka da yardar Allah.

 

Ciwon Sanyi

Abubuwan bukata:

Hulba, Bagaruwa, Man Habbatussauda

yadda za a hada:

A hada Bagaruwa da Hulba a tafasa su, sai idan ya dan huce sai a zauna a ciki, sannan kuma za a shafa man Habbatussauda a gaban, a sashi kamar yadda za’a yi matsi.

In sha Allah za a samu sauki.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Adon Gari Ko Kin San… Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al’adarsu? August 31, 2025 Ado Da Kwalliya Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa August 3, 2025 Adon Gari Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa July 27, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano
  • Rikicin kabilanci: Mutane 2 sun mutu, wasu 7 sun jikkata a Jigawa
  • Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
  • Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
  • Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
  • ’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno
  • Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida
  • Birnin Tarayya Zai Taimaka Da Tara Kudin Shiga Daga Fannin Da Bai Shafi Mai Ba — Dantsoho