Hukumar Bunkasa Ma’aikata Ta Jigawa Ta Shirya Taron Karawa Juna Sani
Published: 10th, October 2025 GMT
Hukumar Bunkasa Ma’aikata ta Jihar Jigawa ta shirya taron karawa juna sani na kwana daya ga jami’an kula da dakunan karatu a wani bangare na aikinta na daga darajar ma’aikata da ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu.
A jawabinsa na bude taron, Darakta Janar na MDI, Umar Farouk Wada, ya ce makasudin shirya taron shi ne don bunkasa kwarewa da sanin makamar aikin da ake da su ta yadda za a samar da ingantacciyar hidima kamar yadda Cibiyar ta tanadar.
Ya kuma bayyana cewa, za a ci gaba da gudanar da irin wannan horon ne domin a baya Cibiyar ta shirya bita ga nau’ukan ma’aikatu masu zaman kansu da na gwamnati.
Umar Farouk ya bayyana ɗakin karatu a matsayin wuri mai aminci don adanawa da kuma samun mahimman bayanai don amfanin da su gaba ɗaya.
Jim kadan bayan bude taron, an gabatar da jerin kasidu ga mahalarta taron daga ma’aikatan da ke cikin cibiyar.
USMAN MZ
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Karawa Juna Sani
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don Halartar Taron Tsaro Na Aqaba
ShareTweetSendShare MASU ALAKA