Aminiya:
2025-11-27@21:17:20 GMT

Sojoji sun mutu yayin da Boko Haram ta kai hari sansanin soji a Borno

Published: 10th, October 2025 GMT

Ana fargabar sojoji da dama sun rasu yayin da mayaƙan Boko Haram suka kai hari sansanin soji da ke Ngamdu, a Ƙaramar Hukumar Kaga a Jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa mayaƙan sun kai wa sojojin hari a sansanin da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe Kwastam ta kama buhunan lalatacciyar fulawa 10,000 ana ƙoƙarin shigo da ita Najeriya

Biyo bayan harin, sojoji sun rufe hanyar Ngamdu har zuwa ƙarfe 11:20 na safe, wanda hakan ya sa matafiya suka maƙale na tsawon lokaci.

“Na tashi daga Damaturu da sassafe ina fatan isa Maiduguri kamar ƙarfe 9 na safe, amma da na isa Ngamdu sai muka tarar da hanya a rufe,” in ji wani matafiyi.

“Jami’an tsaro sun ce mu yi haƙuri saboda an samu matsala a hanya. Daga baya mazauna yankin suka ce Boko Haram ne suka kai wa sojoji hari tare da kashe wasu daga cikinsu.”

Wani mazaunin yankin ya ce mayaƙan sun kai wa sojojin hari ba tare da tsammani ba.

“Harin ya ɗauki lokaci mai tsawo kafin ’yan ta’addan su tafi, amma sun kashe sojoji kuma sun ji wa wasu rauni,” in ji shi.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da faruwar harin, amma ta ce ba a rasa rayuka da yawa kamar yadda aka yaɗa ba.

“‘Yan ta’addan sun yi ƙoƙarin yi wa sojojin kwanton ɓauna, amma sojojinmu jarumai sun yi tsayin daka.

“Wasu daga cikinsu sun ji rauni an kuma kai su asibiti, amma an kashe ’yan ta’adda da dama,” in ji majiyar.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar sojojin Najeriya ba ta fitar da sanarwa kan harin ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Boko Haram hari

এছাড়াও পড়ুন:

Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS

Hukumar tsaro ta DSS ta zargi dan jarida kuma mai shiga tsakani da ’yan ta’addar da suka sace fasinjojin jrigin kasan Kaduna-Abuja a shekarar 2022, Tukur Mamu, da karbar Naira miliyan 50 daga kudin fansar fasinjojin.

Ana zargin Tukur Mamu da karbar kudin ne daga jagoran ’yan bindigar da ake kira da “Shugaba”.

Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000 Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi

Mamu na fuskantar tuhumar laifukan ta’addanci, ciki har da karɓar kuɗin fansa daga iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su a harin jirgin Kaduna na ranar 28 ga Maris, 2022, hulɗa da kuɗaɗen ’yan ta’adda, hana aikin kwamitin babban hafsan tsaron kasa da aka kafa domin tattaunawa da masu garkuwa da mutanen, musayar saƙonnin murya da mai magana da yawun Boko Haram, da sauransu.

A ci gaba da shari’ar a ranar Talata, shaida na hukumae ta DSS na shida ya shaida wa kotu cewa ƙungiyar ta’addan ta nemi Mamu ya koya musu yadda ake buɗe shafin yanar gizo domin gudanar da ayyukansu.

Tun da farko, DSS ta bayyana cewa Mamu ya ba da shawara ga ƙungiyar ’yan ta’addan da su tattauna kai tsaye da iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su, ba tare da shiga kwamitin babban hafsan tsaron da gwamnatin tarayya ta kafa ba.

Shaidar ya yi wannan bayani ne yayin fassara saƙonnin murya na Mamu a lokacin da ake yi masa tambayoyi a ƙasar Masar kafin a dawo da shi Najeriya.

A halin yanzu, Mamu ya shigar da Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) kara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa kiran shi da dan ta’adda.

Ya ce ya shigar da ƙarar ce kan kiran nasa da dan ta’adda da ministan ya yi, alhali ana tsaka da shari’ar tuhumar laifukan ta’addanci kuma har yanzu ba a kai ga yanke hukunci ba.

Alƙali ya dage shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Fabrairun 2026, domin amincewa da jawaban ƙarshe na ɓangarorin da abin ya shafa bisa tanadin Sashe na 49 na Dokar da kuma Sashe na 36 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji
  • NAJERIYA A YAU: Amafani Da Karfin Soji Ko Tattaunawa Ne Zai Kawo Matsalar Tsaro A Najeriya?
  • Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
  • Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka
  • Larijani Iran Tana Maraba Da Tattaunawa Ta Gaskiya Amma Ba Tsararren Sakamako Ba
  • Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau
  • Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS
  • Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000
  • ’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano