Leadership News Hausa:
2025-11-27@20:04:00 GMT

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

Published: 9th, October 2025 GMT

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

 

Bugu da kari, an samu sabon yanayin sayayya yayin hutun, inda bangarorin da suka shafi kayayyaki masu kare muhalli da na fasahohin zamani da kayayyakin kwalliya masu sigogi na zamani da na gargajiya na Sin, suka kara samun tagomashi. Alkaluma sun nuna cewa, sayayyar abincin da aka samar ba tare da sinadarai na zamani ba ta karu da kaso 27.

9 kan mizanin shekara-shekara, sayayyar na’urorin amfanin gida ta karu da kaso 14.3, yayin da ta riguna masu sigogin zamani da na gargajiya na Sin, ta karu da kaso 14.1. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26 October 9, 2025 Daga Birnin Sin Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko October 8, 2025 Daga Birnin Sin Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan October 8, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta bayyana sabbin nasarorin da ta samu wajen yaƙi da laifuka a jihar, ta hanyar holen mutum 34 da ta kama da aikata laifuka daban-daban.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Rabi’u Muhammad, ya ce wannan ci gaba ya samu ne saboda sabbin dabarun aiki da kuma bayanan sirri da aka samu daga al’umma da hukumomin tsaro.

Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000

A Anguwar Barnawa da wasu wurare a Kaduna, rundunar Operation Fushin Kada ta kama mutane 13 da ake zargi da aikata fashi da makami da satar wayoyi a otel-otel da gidaje.

An ruwaito sun taɓa kashe ɗan sanda a shekarar 2024, kuma suna samun bayanai daga dilolin miyagun ƙwayoyi a wuraren shaƙatawa. A

An ƙwato bindiga ƙirar gida, gatari da adduna 13, mota, kwamfuta huɗu, wayoyi 13 da talabijin huɗu.

Haka kuma, a Nunbu Bashayi da ke Sanga, an kama mutane bakwai da ake zargi da garkuwa da mutane tare da neman kuɗin fansa.

Dukkanimsu sun amsa laifinsu kuma ana neman ragowar waɗanda suke tsere.

A wani samame daban, ’yan sanda sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da aikata fashi, fyaɗe da damfara.

Sun saba kai hari gidajen mutane, ɗaukar kuɗaɗen mutane, aikata fyaɗe sannan su riƙa ɗaukar bidiyo tsoratar da mutane.

A Zariya kuwa, an kama wasu mutane tara da suka haɗa da maza da mata waɗanda ake zargi da yi wa direban Adaidaita sahu fashi ta hanyar zuba masa magani a abin sha.

Rundunar ta kuma kama wani likitan bogi mai suna Adamu Abubakar Muhammed wanda ya yi wa mutane tiyata ba tare da shaidar karatun likitanci ba.

Ya yi amfani da takardun bogi wajen yin aiki na tsawon wata guda kafin a gano shi.

Kwamishinan, ya ce duk waɗanda aka kama suna hannun rundunar, kuma za a gurfanar da su kotu bayan kammala bincike.

Ya gode wa jami’an tsaro da al’umma kan haɗin kai, inda ya yi da a ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin inganta tsaro a jihar da ƙasa baki ɗaya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon  Dake Takawa Makiya Birki
  • An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
  • DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
  • Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba
  • Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru  Isa Chiroma Mafaka Ta Wucin Gagi
  • China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makaamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan
  • NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta