NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Nada Shugaban Hukumar Zabe
Published: 9th, October 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A tsarin mulkin Najeriya, an bai wa Shugaban Ƙasa ikon naɗa shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) tare da sauran mambobinta. Wannan iko yana daga cikin muhimman nauyukan da ke hannun shugaban ƙasa domin tabbatar da cewa ana gudanar da zaɓe cikin tsari, gaskiya da adalci.
Sai dai, kafin wanda shugaban ƙasa ya naɗa ya fara aiki, dole ne a nemi amincewar Majalisar Dattawa, domin tabbatar da cewa wanda aka zaɓa ya cancanci rike wannan muhimmiyar kujera. Wannan tsari yana taimakawa wajen tabbatar da cewa hukumar zaɓe ta kasance mai zaman kanta, ba ta karkata ga wani ɓangare na siyasa ba, kuma tana iya gudanar da aikinta cikin gaskiya da amana.
NAJERIYA A YAU: Tasirin Takardun Shaida Na Bogi Ga Rayuwar Al’umma DAGA LARABA: Yadda Aka Yi Almajiri Ya Zama Mabaraciwannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
2027: INEC Ta Nemi A Gaggauta Amincewa Da Ƙudirin Sake Fasalin Tsarin Zaɓe
“Muna kira ga majalisar kasa da ta yi la’akari da shirin gyaran tsarin kudurorin zabe cikin gaggawa. Amincewa da dokar cikin lokaci yana da muhimmanci ga shirinmu na gudanar da zabe a 2027.
“Rashin tabbas game da tsarin doka na zabe na iya kawo matsaloli masu yawa ga ayyukan hukumar INEC yayin da lokacin zabe ke karatowa,” in ji shi.
Shugaban INEC ya bayyana cewa hukumarsa ta aiwatar da shawarwarin da aka mika mata kai tsaye a rahoton EU na zaben 2023.
“An dauki mataki kan wasu bangarori na shawarwarin da ake bukatar hukumar ta aiwatar da su. Haka kuma, ana daukar mataki kan shawarwarin da suka shafi fannoni da dama wadanda ake bukatar hadin gwiwa tsakanin INEC da sauran hukumomi da masu ruwa da tsaki yayin da ake jiran kammala bitar sake fasalin shari’a da majalisar kasa ke yi,” in ji shi.
A nasa kalamun, Mista Barry Andrews ya yaba da muhimmancin Nijeriya a dimokuradiyyar duniya, yana bayyana aikin EU na 2023 a matsayin daya daga cikin manyan aikace-aikace ga dukkan kasashen duniya.
“Aikinmu shi ne taimakawa wajen samun ci gaban na aiwatar da shawarwarin daga zabukan shekarar 2023. Mun lura da manyan ci gaba a wasu fannoni da dama, ko da yake wasu kalubale suna nan yadda suke, musamman wadanda suka shafi shari’a da gudanarwa da tsarin gyara fasalin kundin tsarin mulki,” in ji shi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA