An Shawarci Iyaye Su Bari A Yiwa ‘Ya’yansu Alluran Rigakafi A Jigawa
Published: 9th, October 2025 GMT
An shawarci mata a karamar hukumar Kirikasamma da ke jihar jigawa da su kawo ‘ya’yansu domin yi musu rigakafin cutar shan inna, kyanda, da Gaida da sauran cututtuka masu ban tsoro.
Uwargidan Shugaban Karamar Hukumar, Hajiya Fatima Maji Marma ta ba da wannan shawarar a lokacin kaddamar da shirin rigakafin cutar kyanda da na rigakafi na yau da kullum a fadar Hakimin Marma.
Ta kuma jaddada aniyar karamar hukumar na bayar da tallafin da ake bukata domin samun nasarar gudanar da aikin rigakafin.
Hajiya Fatima ta kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa bullo da inshorar lafiya ga marasa galihu a matakin unguwanni a kananan hukumomin jihar 27.
A nasa jawabin manajan hukumar kula da lafiya matakin farko na karamar hukumar Kabiru Musa Jahun ya bayyana jin dadinsa da yawan fitowar mata masu shayarwa da suke kawo jariransu domin yi musu rigakafin.
Shima da yake nasa jawabin Hakimin kauyen Marma, Alhaji Haruna Adamu, ya bayyana jin dadinsa kan sadaukarwar Hajiya Fatima Marma.
USMAN MZ
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Iyaye Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza
The Gaza Humanitarian Ffoundatin (GHF) a Gaza ta bada sanarwan kawo karshen ayyukanta a Gaza makonni 6 bayan an fara abinda suke kira tsagaita wuta a Gaza.
Shafin yana gizo na labarai ‘ArabNews’ na kasar Saudiya ya nakalto shugaban hukumar John Acree yana fadar haka ya kuma kara da cewa hukumar ta cimma manufar kafata na rarraba abinci tsakanin Falasdinawa a Gaza wadanda suke mutuwa saboda yunwa bayanda HKI ta hana shigowar abinci Gaza na tsawon kwanaki kimani 90 ko watanni 3.
Gwamnatin kasar Amurka ta da HKI ne suka kafa hukumar bada agajin bayan sun kori dukkan kungiyoyin bada agaji a yankin. Sannan sun yi amfani da hukumar don kissin Falasdinawa wadanda suke takawa da kafa zuwa cibiyoyin bada abinci da suka kafa a wuraren da sai sun wuta ta gaban sojojin HKI wadanda suke bude masu wuta. Amma Falasdinawan basu da zabi ko yunwa ta kashe su a cikin gaza ko kuma su je su karbi abincin da mai yuwa ba zasu dawo ba har abada.
Amurka da HKI sun kashe daruruwan Falasdinawa a cikin wannan lokacin. Acree yace sun raba kunshi miliyon uku dauke da abinci miliyon 187 ga falasdinawa a lokacin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Tsirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Rushewar Yarjejeniyar Bude Wuta Idan Israila Ta ci Gaba Da Kai Hare-Hare November 24, 2025 Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta November 24, 2025 Wakilin MDD Ya Bukaci Goyon Bayan Iran Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yamen November 24, 2025 Yara 50 Da Aka Sace A Najeriya Sun Tsere Daga Hannun Barayin Daji November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci