Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da wasu mutum 173 afuwa
Published: 10th, October 2025 GMT
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da afuwar Shugaban Kasa ga mutane 175.
Daga ciki har da wadanda aka yi wa afuwar bayan mutuwa ga marigayi Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa da ɗan gwagwarmayar kwato ’yancin kan Najeriya, Herbert Macaulay.
An dauki wannan mataki ne bayan amincewa da shawarwarin da Majalisar Tsofaffin Shugabannin Ƙasa ta bayar a taronta da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja.
A cewar sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin bayanai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma yi afuwa ga tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan da wasu mutum uku, Misis Anastasia Daniel Nwaobia, Lauya Hussaini Umar, da Ayinla Saadu Alanamu, bayan an tabbatar da cewa sun nuna nadamarsu da shirin komawa cikin al’umma.
Vatsa, wanda marubuci ne kuma tsohon jami’in soja da aka kashe a shekarar 1986 bayan tuhumarsa da cin amanar ƙasa, ya samu afuwa bayan mutuwa kusan shekaru arba’in bayan kasha shi.
Haka kuma, Herbert Macaulay, ɗaya daga cikin fitattun ’yan gwagwarmayar Najeriya da kuma wanda ya kafa jam’iyyar NCNC, ya samu afuwa kan hukuncin da hukumomin mulkin mallaka suka yanke masa a shekarar 1913.
Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya yi afuwa ga fursunoni 82, ya rage wa wasu 65 zaman gidan yari, sannan ya sauya hukuncin kisa na wasu mutum bakwai zuwa ɗaurin rai da rai.
Bugu da ƙari, Shugaban Ƙasa ya yi afuwa ga ’yan gwagwarmayar Ogoni tara da aka kashe, Ken Saro-Wiwa, Saturday Dobee, Nordu Eawo, Daniel Gbooko, Paul Levera, Felix Nuate, Baribor Bera, Barinem Kiobel, da John Kpuine, tare da ba wa wasu huɗu lambar yabo ta ƙasa bayan mutuwa: Cif Albert Badey, Cif Edward Kobani, Cif Samuel Orage, da Theophilus Orage.
Wannan mataki ya biyo bayan shawarwarin da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Hakkin Yin Afuwa (PACPM) ya bayar, ƙarƙashin jagorancin Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi (SAN).
Kwamitin ya duba bukatu 294, inda ya ba da shawarar yin afuwa ga fursunoni 82, afuwar kai tsaye ga mutum biyu, rage zaman gidan yari ga mutum 65, sauya hukuncin kisa ga mutum bakwai zuwa ɗaurin rai da rai, da kuma afuwa bayan mutuwa ga tsofaffin masu laifi 15.
Ka’idojin da kwamitin ya yi amfani da su sun haɗa da shekaru (60 zuwa sama), ciwon da ba ya warkewa, ƙuruciya (16 zuwa ƙasa), nuna kyakkyawan hali a gidan yari na tsawon lokaci, da nuna nadama, da sauransu.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ne ya ƙaddamar da kwamitin na PACPM a watan Janairu 2025 don inganta adalci, gyaran hali da kare haƙƙin ɗan adam a ƙasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Afuwa Farouk Lawan bayan mutuwa
এছাড়াও পড়ুন:
An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
Hukumar kula da makarantun firamare da sakandare ta Jihar Katsina ta sanar da sake buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarabawar zangon farko na shekarar karatu.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sani Danjuma Suleman, ya fitar a madadin Shugaban hukumar, ta ce makarantun firamare, sakandiren je-ka-ka-dawo da kuma makarantu masu zaman kansu za su buɗe daga yau Talata domin ci gaba da jarabawar zangon farko.
Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran makarantun kwana za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai lokacin da hali ya ba da dama.
Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun bayan ƙaruwar hare-haren sace ɗalibai da masu garkuwa da mutane suka sake farfaɗowa da su a wasu yankuna.
Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne da nufin daƙile matsalar tsaro da kuma sa ido a kan al’amura.
A ƙarshe, hukumar ta roƙi haɗin kan iyaye da masu kula da ɗalibai domin su ci gaba da ba wa shirin goyon baya tare da ƙarfafa ɗaliban su dage da karatu wajen rubuta jarabawar da suke yi.