Shugaba Tinubu ya Naɗa Farfesa Joash Ojo Amupitan a Matsayin Shugaban INEC
Published: 9th, October 2025 GMT
Majalisar magabata a Najeriya ta amince da nada Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) daga jihar Kogi a matsayin sabon shugaban hukumar zaben kasar INEC.
Cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce Shugaba Tinubu ne ya gabatar da sunan Farfesa Amupitan ga majalisar domin neman amincewarta.
Tinubu ya shaida wa majalisar cewa Farfesa Amupitan ne mutum na farko daga jihar Kogi da zai rike mukamin, kuma ba dan siyasa ba ne.
Nan take kuma duka mambobin majalisar suka amince da shi ba tare da sabani ba.
A yanzu shugaba Tinubu zai aika sunansa zuwa majalisar dattawan Nigeria domin amincewarta kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Farfesa Amupitan, mai shekara 58, malami ne a Jami’ar Jos da ke jihar Plateau.
A 2014 ne ya samu mukamin babban lauya na SAN.
Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Naɗi
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan Majalisar Kudu sun roƙi Tinubu ya yi wa Nnamdi Kanu Afuwa
’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.
Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, wajen yi wa Nnamdi Kanu afuwa wanda kotu ta same shi da laifin ta’addanci.
Alƙali James Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin, inda ya same shi da laifi a kan tuhumar da ake masa guda bakwai, sannan ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
Tuni aka tura Nnamdi Kanu zuwa gidan yari a Jihar Sakkwato inda yake zaman waƙafi.
Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke FuskantaA cikin sanarwa bayan taron gaggawa da suka gudanar a Abuja, ’yan majalisar sun ce duk da cewa suna girmama kotu da tsarin shari’a, lamarin ya rikiɗe zuwa matsalar ƙasa mai tasiri ga rayuwar jama’a, tattalin arziki da tsaro.
Da yake karanta sanarwar, Hon. Iduma Igariwey ya ce yin afuwa zai taimaka wajen rage tashin hankali da dawo da zaman lafiya a yankin.
Sun lissafa dalilai guda huɗu da suka sa suka yi wannan kira.
Dalilan da suke bayyana su ne ƙaruwa da rashin tsaro da tashin hankali da ke da alaƙa da tsare Kanu; Wahalar rayuwa da tattalin arziki da jama’a ke fuskanta da kuma buƙatar shugabanci mai tausayawa wajen shawo kan matsalolin ƙasa.