Aminiya:
2025-10-13@13:34:44 GMT

’Yan bindiga sun kashe sojoji 3 a Kebbi 

Published: 11th, October 2025 GMT

’Yan bindiga sun kashe sojojin Nigeriya guda uku a wani kwanton ɓauna da suka yi masu a lokacin da suke ƙoƙarin hana yin garkuwa da wasu mutane a ƙauyukan ƙananan hukumomin Sakaba da Danko-Wasagu a Jihar Kebbi.

Sojojin da aka kashe an yi masu sutura a babban barikin sojoji da ke garin Zuru, hedikwatar ƙaramar hukumar Zuru.

Mai Martaba Sarkin Zuru Alhaji Sanusi Mika’ilu Sami, ya halarci janazar domin tausayawa da jinjina wa marigayin kan sadaukarwar da suka yi a wurin kare mutanen ƙasa.

Majiyar da ta shaida wa Aminiya ta ce sojojin sun kai ɗauki ne a lokacin da suka samu labarin ’yan ta’addan sun kai farmaki tare da ƙoƙarin yin garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.

Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina ’Yan Najeriya miliyan 60 na fama da taɓin hankali — Likita

Sai dai ana jiran bayani daga rundunar soja ta kasa kan wadannan jami’ai nata da aka kashe a fagen daga a yakin jihar Kebbi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22

Sojojin Nijeriya sun kashe wani kwamandan ƙungiyar ƴan ta’adda IPOB/ESN da ake nema ruwa a jallo, mai suna ‘Alhaji’, tare da wasu mutane 26 a jerin hare-haren da suka kai a sassan ƙasar tsakanin 8 zuwa 11 ga Oktoba, 2025. Rundunar Sojin ta ce an kuma ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su, tare da kwace makamai, da harsasai, da kuɗaɗe.

A kudu maso gabas, Sojojin Operation UDO KA sun kai farmaki a Izzi, jihar Ebonyi, inda suka kashe ‘Alhaji’ bayan ya yi yunƙurin kwace bindiga daga hannun wani Soja lokacin kama shi. Haka kuma, a jihar Imo, an rusa wata maboyar IPOB/ESN da ake amfani da shi wajen horar da mambobi.

Sojoji Sun Cafke Babban Kwamandan IPOB Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

A Arewa maso gabas, Sojojin Operation Haɗin Kai sun kashe ‘yan ta’adda tara a Magumeri da Gajiram a jihar Borno, inda suka ceto fararen hula biyu tare da ƙwato fiye da Naira ₦4.3 miliyan. A wasu hare-haren sama a jihar Sokoto, an hallaka shugabannin ‘yan ta’adda da dama, yayin da aka kama masu safarar miyagun ƙwayoyi daga Legas zuwa Zamfara.

A Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Kudu, Sojojin Operation Whirl Stroke da Operation DELTA SAFE sun kama masu garkuwa da mutane, sun kashe ‘yan ƙungiyar asiri biyu, kuma sun ƙwato makamai da babura. Rundunar Sojin ta ce gaba ɗaya an kashe ‘yan ta’adda 26, an kama mutum 22, kuma an ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tsaro A Ba Mu Makamai Don Kare Kanmu – Jama’ar Sakkwato October 11, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 9, Sun Ƙwato Naira Miliyan 5 A Borno October 11, 2025 Tsaro Sojoji Sun Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Lalata Kayayyakin Gwamnati A Binuwe October 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 9, sun kwato kudin fansa a Borno
  • Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22
  • Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro
  • ’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno
  • Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno
  • ‘Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Wata Ba’amurkiya Da Ta Ziyarci Saurayinta A Jihar Delta
  • Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi
  • ’Yan bindiga sun kashe Civilian JTF 8 a Zamfara
  • Sojoji sun mutu yayin da Boko Haram ta kai hari sansanin soji a Borno