’Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da kashe ma’aikaciyar Arise TV a Abuja
Published: 9th, October 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, sun kama mutum 12 da ake zargi da hannu a kisan ma’aikaciyar Arise TV, Somtochukwu Christella Maduagwu, a unguwar Katampe da ke Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa Somtochukwu, ta rasu bayan faɗowa daga bene mai hawa uku, yayin da ta ke ƙoƙarin tserewa daga hannun ’yan fashin, yayin da mai gadin gidan ya rasa ransa bayan harbin bindiga.
Wata majiyar ’yan sanda ta bayyana cewa rundunar Scorpion Squad ƙarƙashin jagorancin ACP Victor O. Godfrey ce ta kama waɗanda ake zargin.
Wasu daga cikin waɗanda aka kama sun amsa laifinsu, inda ɗaya daga cikinsu ya ce shi ne ya harbi mai gadin gidan, yayin da wani ya ce ya yi ƙoƙarin riƙe ’yar jaridar lokacin da za ta faɗo.
Sun kuma bayyana cewa sun sace wata mota ƙirar Honda CR-V mallakin ’yar jaridar, sannan kowa daga cikinsu ya samu Naira 200,000 daga kuɗin da suka sato.
’Yan sanda sun ƙwato bindigogi, harsasai, wuƙaƙe da wayoyi daga hannunsu.
An sake kama wasu daga cikinsu a ranar 8 ga watan Oktoba, lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa aikata wani fashin a Maitama.
Kakakin rundunar Abuja, Josephine Adeh, ta ƙi yin bayani kan lamarin, amma Lere Olayinka, mai taimaka wa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya tabbatar da kama waɗanda ake zargin a shafukansa na sada zumunta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda yan fashi yar jarida ARISE TV Babban Birnin Tarayya zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
Babbar Kotun Jihar Oyo da ke Ibadan, babban birnin jihar, a ranar Litinin ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutum biyar da ta samu da laifin kashe wani direban tasi.
Kotun dai ta sami mutanen ne da laifin kashe direban mai suna Akeem Shittu a lokacin mummunan rikici a shekarar 2024.
DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane? An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a KebbiYayin yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Oyeyemi Ajayi ya bayyana cewa Segun Taiwo (36), Kehinde Ademola (46), Yahaya Adeniyi (45), Chinonso Samson (41), da Opadotun Michael (32) sun yi tarayya wajen yin hadin baki da kuma kisan Shittu.
“Na yi la’akari da cewa kotu za ta iya tabbatar da hadin baki a cikin ayyukan da suka kai ga mutuwar Shittu,” in ji shi.
Saboda haka, ya yanke wa kowanne daga cikin su hukuncin shekaru 20 a kurkuku saboda makirci, sannan ya yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin kisan kai.
“A kan tuhuma ta biyu, kowanne daga cikin waɗanda ake tuhuma an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya,” in ji alkalin.
Tun da farko, Lauyar gwamnatin Jihar, K. K. Oloso, ta bayyana yadda ƙaramin hatsarin hanya ya rikide zuwa mummunan hari.
Ta ce a ranar 10 ga Afrilu, 2024, da misalin ƙarfe 8:30 na dare, a kan titin Elepe, Arulogun Road, yankin Ojoo na Ibadan, waɗanda ake tuhuma tare da wasu da har yanzu ba a kama ba sun kai wa Shittu hari bayan ya yi karo da babur mai ɗauke da fasinjoji biyu.
“An ce ɓangarorin sun tafi wata mashaya kusa domin sasanta lamarin. A can, ƙungiyar masu babur ta nemi N50,000 don yin magani, amma Shittu ya iya bayar da N8,000 kawai. An hana shi barin wurin, aka cire masa kaya, kuma duk da cewa ya yi ƙoƙarin tserewa na ɗan lokaci, daga baya aka kewaye shi aka yanka shi da adda har lahira.”
Masu bincike daga baya sun gano motar tasi dinsa da mayafinsa a gaban shagon matar ɗaya daga cikin waɗanda aka yanke wa hukuncin.
Lauyar gwamnatin ta jaddada cewa laifukan sun sabawa sashe na 316 kuma laifuka ne a ƙarƙashin sashe na 319 da na 324 na Dokar Laifuka ta Jihar Oyo ta 2000, wadda ta tanadi hukunci mai tsanani ga makirci da kisan kai.