Guguwar Ritaya Na Barazana Ga Ayyukan Hukumar Kwastam Yayin Da Jami’ai 825 Za Su Yi Ritaya
Published: 10th, October 2025 GMT
Wannan lamari ya haifar da tambaya kan yiwuwar dorewar shirin sauye-sauye da na zamani da ake gudanarwa a karkashin jagorancin Babban Kwanturola Janar, Adewale Adeniyi.
Adewale Adeniyi, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kara wa wa’adin mulki na shekara guda, shima zai yi ritaya daga hukumar a watan Agusta, 2026.
A halin yanzu, za a dauki babban mataki kafin a cike gibin ma’aikata da ake bukata a hukumar kwastam, musamman idan aka yi la’akari da cewa jami’ai 825 za su bar aiki ba tare da sabon daukar ma’aikata ba.
Binciken da leadership Hausa ta gudanar ya gano cewa ritayar ta shafi kowane mataki a hukumar daga manyan shugabanni, zuwa matsakaita, har da kananan jami’ai.
Daga cikin jami’ai 825 da za su yi ritaya saboda shekaru 60 da suka kai ko kuma shekaru 35 na aiki:
5 suna da mukamin mataimakan kwanturola na kasa wato (DCG) sai wasu kananan mataimaka Kwanturola na kasa (ACG) su 13 sai kuma Kwanturololi ( CAC) guda 53 da mataimakanau (DC) guda 51 kananan mataimaka Kwanturola ( AC) guda 46.
Sauran sune ; masu mukaman (CSC) guda 61 sai ( SC) Guda 226 da ( DSC) su 285 sai (ASC I) 64 da (ASC II) su 10 (IC), su 8 (CA I) guda 1 sai (CA II) su 2 Jami’an mataimaka Kwanturola Janar ( DCG) guda biyar da ritayar ta shafa su ne: Mista C.K. Niagwan da K.I. Adeola da kuma Mista S. Chiroma; Mr. G.M. Omale; da Mista A. Nnadi.
Kananan Jami’an mataimaka Kwanturola Janar (ACG) guda goma sha uku (13) da abin ya shafa su ne: K.C. Egwuh, M.S. Yusuf, da Z.M. Gaji da N.P. Umoh da O.A. Adebakin da kuma T. Bomodi da B.O. Olomu, O.P. Olaniyan, I.K. Oladeji, K. Mohammed, O.A. Adebakin, da B. Mohammed, da C.C. Dim.
Daga cikin Kwanturololi da za su yi ritaya a 2026, akwai: D. Abubakar, da O.Y. Shuaibu, F.A. Bodunde da P.C. Chibuoke, da kuma O.O. Akingbade, da A. Salihu, da wasu da dama.
A matsayin shiri kafin ranar ritayar 2026, Hedikwatar Hukumar Kwastam da ke Abuja ta bayar da umarni ga dukkan jami’an da abin ya shafa su fara shirye-shiryen barin aiki kamin ranar ta isko su.
Hakazalika, An umurce su da su mika sanarwar izinin hutu na watanni uku kafin ritaya ga Babban Kwanturola Janar na Kwastam (CGC).
A cikin takardar da wakilinmu ya gani mai taken “Jerin karshe Na Jami’ai da Ma’aikata Don Ritaya A Shekarar 2026”, wacce aka fitar ranar 19 ga Satumba, 2025, kuma Kwanturola A.A. Bazuaye ya sanya hannu a madadin DCG na Sashen Albarkatun Dan Adam (HR), an bukaci jami’an da abin ya shafa da su bi doka da tsari.
Kamar yadda takardar ta ce: “A bisa Dokar Aikin Gwamnati (PSR No. 100238) da kuma Sanarwar Gwamnati mai lamba 36216/S.1/D/T: CR1/2001/5 na 20/3/2001, dukkan jami’an da suka cika shekarun ritaya a 2026 za su bar aiki kuma su tafi hutu na watanni uku kafin ranar da ritayar za ta fara aiki.”
Haka kuma, an umurci dukkan jami’an da abin ya shafa su tabbatar da bin umarnin, tare da tura takardar sanarwar hutun ritayarsu ga Babban Kwanturola Janar yadda ya dace.
Takardar ta kuma bukaci Koordinetocin Yankuna da Kwamandojin Yankuna su sanar da duk jami’an da abin ya shafa a yankunansu.
Da wannan yawan ma’aikata da za su bar aiki a 2026, har yanzu ana cikin tunanin irin dabarar da shugabancin kwastam zai yi amfani da ita don cike gibin da zai biyo baya, tare da tabbatar da ci gaba da sabbin domin gudanar da ayyukan hukumar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: jami an da abin ya shafa an mataimaka Kwanturola Kwanturola Janar
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun kashe Civilian JTF 8 a Zamfara
Aƙalla mutum takwas ’yan Ƙungiyar tsaro ta Civilian JTF ko ’yan ƙato da gora aka sanar an kashe a ƙauyen Dan Loto da ke Ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.
Harin dai na zuwa ne makonni biyu kacal bayan da wasu ’yan bindiga suka kai hari a wani masallaci tare da kashe wasu masallata biyar ciki har da wani Limami a ƙaramar hukumar.
’Yan Najeriya miliyan 60 na fama da taɓin hankali — Likita Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a GombeDan Loto yana cikin yankin Yandoton Daji, unguwar da ’yan bindigar suka kashe masu ibada biyar a ranar 26 ga Satumba, 2025.
Binciken Daily Trust ya nuna cewa, ’yan bindigar sun yi wa ’yan ƙungiyar ta CJTF kwanton ɓauna ne a lokacin da suke amsa kiran da ‘yan bindigar ke yi na tayar da ƙayar baya ga al’ummar garin Dan Loto.
Usman Yusuf Tsafe ya shaida wa Daily Trust cewa an kashe jami’an CJTF ne a lokacin da suke musayar wuta da ’yan bindigar.
“Akwai yuwuwar ’yan binigar sun samu labarin zuwan jami’an CJTF, don haka suka yi musu kwanton ɓauna.
“’Yan bindigar sun kashe su, suka tsere sai dai sun auka wa jami’an CJTF ne, bayan sun kashe biyar daga cikinsu, sai suka koma daji, ba su kai farmaki ga mazauna garin ba,” in ji shi.
Aliyu Danlami, mazaunin unguwar Yandoton Daji, ya ce sun shiga cikin ruɗani sakamakon harin.