Shugaban ya ci gaba da cewa, a karkashin shugabancinsa, Hukumar za ta yi namijin kokari wajen bayar da goyon bayanta, wajen fitar da kayan da ba su shafi dangogin Mai ba, zuwa kasar waje, musamman ta hanyar cin giyar albakatun yanayin na Abuja da kuma na bangaren aikin noma, da birnin ke da shi. Ya kara da cewa, ta hanyar wadannan alkatun kasar da birnin ke da su, Hukumar za ta kara bayar da gudunmwarta, wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar nan da kuma kara fitar da kayan da ba su shafi Man ba, zuwa ketare.

 

A cewarsa, domin Hukumar ta tabbatar da na kara mayar da hankalin wajen ganin ana bin ka’ida da kuma tabbatar da ingancin gudanar da ayyukanta, ta kirkiro da tsare-tsare na fasahar zamani na bai daya da ake kira a turance, PCS da kuma NSW.

A cewarsa, wadannan fasahar ta zamani, za su taimaka wajen hada masu ruwa da tsaki a fannin da ke fitar da kaya zuwa ketare tare da kuma rage jinkiri wajen fitar da kayan waje da kuma samar da kyakyawan yanayi ga masu fitar da kayan ketare.Shugaban ya sanar da cewa, Hukumar na alfaharin danganta manta da ayyukan da Cibiyar ta kolin kasuwanci ta Abuja ke ci gaba da gudanarwa musamman a bangaren kara habaka tattalin arzikin kasar nan.

Dantsoho ya kuma gayyaci masu ruwa da tsaki a fannin kar su bari a barsu a baya, wajen cin gajiyar saukin da Hukumar ta samar na fitar da kaya daga cikin kasar nan, zuwa ketare.

Kazalika, Shugaban ya bayyana cewa, Hukumar ta kuma samar da tsarin fasahar zamani na fitar da kaya a cikin sauki a Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar wato EPT.

Ya kara da cewa, wannan fasahar ta taimaka matuka wajen fitar da kaya waje ba tare da wani tarnaki ba.

Shugaban ya ci gaba da cewa, Hukumar ta kuma fadada fasahar ta EPT, domin samar da saukin fitar da kaya ga kananan da matsakaitan masana’antun kasar suka sarrafa, domin fitar da su ketare.

Hakazalika, Shugaban ya bayyana cewa, domin ayyukan Hukumar su tafi kafada da kafada da kudurin Gwamnatin Tarayya NPA ta saita gudanar da ayyukanta ta hanyar yin amfani da fasahar ta zamani ta PCS.

A cewarsa, wannan zai tabbatar da samar da wani ginshike ga fasahar NSW, inda za a rinka fitar da kayan waje, ba tare da wata matsala ba.

Dantsoho ya yi nuni da cewa, fasahar ta NSW aba ce, da ake yin amfani da da ita, a daukacin fadin duniya, wajen samar da saukin fitar da kaya waje.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa, Hukumar na daukar Malamai wajen ganin cewa, ayyukanta, sun kai da lungu da sako, da ke da wuyar isa a kasar.

Ya kuma bai wa masu ruwa da tsaki a fannin cewa, ako da yau, kofar Hukumar a bude take domin yin hadaka da su.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tattalin Arziki An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi  October 10, 2025 Tattalin Arziki Arewa Ta Daina Zama Ci-Ma Zaune A Tattalin Arziƙi – Gwamnan Bauchi October 10, 2025 Tattalin Arziki Bayan Shekara 20 Nijeriya Ta Sake Dawo Da Tsarin Bayar Da Hayar Kananan Jiragen Sama October 3, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: fitar da kayan fitar da kaya Shugaban ya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida

Ministar wadda ta je kamfanin domin daukar sabuwar motarta ta alfarma kirar Nord Demir SUB da kamfanin ya hada nataimakin Shugaban jami’ar na sashen kula da ilimi da gudanar da bincike Farfesa Bola Oboh da kuma Shugaban kamfanin Mista Oluwatobi Ajayi ne, suka karbi bakuncinta.

 

A jawabin da ta gabatar a lokacin ziyarar ministar ta bayyana cewa,Duba da yarjejeniyar hada-hadar kasuwanci wajen fitar da kaya zuwa ketare kamfanin zai iya yin amfani da wannan samar waken fitar da motocinsa zuwa ketare.

 

Ta kara da cewa, Nijeriya na da gurare biyu ne da ake hada motoci da suka hada da, na wannan jami’ar da kuma na EPs, inda ta yi nuni da cewa, karfin da kamfanin ya ke da shi, zai iya cike gibin bukatar da ake da ita, ta ‘yan kasar na bukatar motocin.

 

Ya ci gaba da cewa, za mu ci gaba da kara karfafa kwarin guwair ‘yan kasar domin da kuma sauran kamfanoni masu zaman kansu domin su rinka sayen kayan da kamfanonin kasar, suka sarrafa da kuma hada su.

 

Ta ce, wannan babban abin alhari ne, ganin cewa, a wannan jami’ar ce, aka hada wannan mortar.

 

Shi kuwa a na sa jawabin Farfesa Oboh ya bayyana cewa, muna Myrna da wannan shirin na Gwamnatin Tarayya wanda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ke jagorantar bai wa ‘yan kasar kwarin guwair sayen kayan da aka sarrafa a cikin kasar

A cewarsa, jami’ar ta UNILAG, ba wai kawai na yin alfahari da samun wannan wajen hada motocin ba ne, kadai amma ta na alharin da cewa, an samar da wajen a jami’ar.

Shi ma, Shugaban kamfanin Mista Oluwatobi Ajayi, a yayin da ya ke nuna jin dadinsa kan gudunmwar da ministar ke bai wa kamfanin ya a bayyana cewa, na yi matukar farin ciki ganin cewa, ministar ta kasance daya daga cikin abokan cinikayyar mu

Kazalika, Shugaban ya kuma gode wa mahukunta jami’ar ta UNILAG kan yin hadaka da kamfanin.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tattalin Arziki Birnin Tarayya Zai Taimaka Da Tara Kudin Shiga Daga Fannin Da Bai Shafi Mai Ba — Dantsoho October 10, 2025 Tattalin Arziki An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi  October 10, 2025 Tattalin Arziki Arewa Ta Daina Zama Ci-Ma Zaune A Tattalin Arziƙi – Gwamnan Bauchi October 10, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Labarin Xinjiang A Zane: Aikin Yawon Shakatawa Na Kara Samar Da Arziki Ga Al’ummar Xinjiang
  • Kasar Sin Ta Kare Matakinta Na Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth
  • An Wallafa Ra’ayoyin Shugaba Xi Kan Batutuwan Da Suka Shafi Mata Da Yara Cikin Karin Harsunan Waje
  • Yajin Aikin ASUU:  Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya
  • Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025
  • Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe
  • Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida
  • Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata