Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano
Published: 10th, October 2025 GMT
Rundunar ƴansanda ta Jihar Kano ta ce ta ceto mutane uku da aka sace a yayin wani aiki biyu da ta gudanar a Kano da Kaduna, tare da ƙwato babur da wasu shaidu. Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a.
A cewar Kiyawa, a ranar 7 ga Oktobar 2025, rundunar daƙile garkuwa da mutane (Anti-Kidnapping) tare da tawagar sa-ido daga ofishin ƴansanda na Bebeji sun gudanar da sumame bayan samun bayanan sirri kan wani mutum da ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutane.
A wani sumame daban, rundunar ta ce a ranar 9 ga Oktoba 2025, ta kuma ceto wani matashi, Ashiru Murtala, mai shekaru 19, wanda aka sace daga Beli, a ƙaramar hukumar Rogo da ke Kano, a ranar 5 ga Oktoba. An same shi a gonar rake a Hunkuyi da ke ƙaramar hukumar Kudan ta Kaduna bayan masu garkuwar sun gudu.
Kwamishinan Ƴansanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya umurci a bai wa waɗanda aka ceto kulawar likita tare da ci gaba da bincike domin kama waɗanda ke da hannu a garkuwar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro
Sufeton ƴansanda na Ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, ya maye gurbin Kwamishinan ƴansandan birnin tarayya, CP Ajao Adewale, sakamakon ƙaruwar matsalolin tsaro a Abuja. Wannan mataki ya biyo bayan matsin lamba da yake fuskanta saboda rashin gamsuwa da aikinsa tun bayan karɓar ragama daga CP Benneth Igwe.
Majiyoyi daga cikin rundunar sun bayyana cewa sauya shi ya shafi yadda matsalolin tsaro ke ƙaruwa a Abuja, musamman bayan harin fashi da makami da ya yi sanadin mutuwar mai gabatar da shirye-shiryen gidan talabijin ɗin ARISE, Somtochukwu Maduagwu, da mai gadi Barnabas Danlami, a Katampe, ranar 29 ga Satumba, 2025.
Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna NAFDAC Ta Rufe Manyan Shaguna 2 Na Ƴan China A AbujaWata wasiƙar cikin gida daga shalƙwatar ƴansanda ta tabbatar da cewa CP Miller Gajere Dantawaye ne aka naɗa sabon kwamishinan ƴansanda na FCT, yayin da DCP Wilson Aniefiok Akpan aka tura shi zuwa jihar Kogi.
Wasiƙar, mai lamba TH.5361/FS/FHQ/ABJ/SUB.6/213, ta bayyana cewa wannan sauyin na ɗan lokaci ne har sai hukumar aiyukan ƴansanda ta ƙasa (PSC) ta amince da cikakken naɗin.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA