Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro
Published: 11th, October 2025 GMT
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da kyautar motoci ƙirar Hilux guda shida da babura 30 domin taimaka wa sojoji wajen yaƙi da ’yan bindiga a faɗin jihar.
Gwamnan, ya miƙa motocin da baburan ga Kanal Hussaini Rabi’u Toro na rundunar sojoji ta takwas a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi.
’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a KebbiYa ce wannan kyauta na cikin ƙoƙarin gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da walwalar al’umma.
“Tsaro shi ne babban abin da gwamnatina ta mayar da hankali a kai. Ba za mu yi wasa da harkar tsaro ba.
“Za mu ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da dukkanin abin da suke buƙata,” in ji Gwamna Idris.
Ya ƙara da cewa, an fara bai wa sojoji ne kyautar, amma sauran hukumomin tsaro su ma za su samu irin wannan tallafi nan ba da jimawa ba.
Da yake bayani a wajen taron, Kanal Hussaini Toro, ya gode wa gwamnan bisa wannan taimako, inda ya cewa hakan zai ƙara musu ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
“Sojoji sun yi matuƙar farin ciki da wannan tallafi. Zai taimaka wajen inganta aikinmu na tabbatar da tsaro a Jihar Kebbi,” in ji Kanal Toro.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babura Gwamna Idris kyauta Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Wata Ba’amurkiya Da Ta Ziyarci Saurayinta A Jihar Delta
Rundunar ‘yansanda ta tabbatar da cewa ana gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwarta.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA