ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tattalin Arziki Arewa Ta Daina Zama Ci-Ma Zaune A Tattalin Arziƙi – Gwamnan Bauchi October 10, 2025 Tattalin Arziki Bayan Shekara 20 Nijeriya Ta Sake Dawo Da Tsarin Bayar Da Hayar Kananan Jiragen Sama October 3, 2025 Tattalin Arziki Tashoshin Jiragen Ruwa Sun Samar Da Kashi 19.

6 Na Fitar Da Kayan Da Ba Su Shafi Mai Ba—Dantsoho October 3, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ebonyi, ta kama wani mutum mai suna Chukwuma Onwe, ɗan Ƙaramar Hukumar Izzi, bisa zargin sayar da ɗan da aka haifa masa kwanaki biyar kan Naira miliyan 1.5.

An gano cewa Onwe ya sayar wa wata mata mai suna Chinyere Ugochukwu jaririn, wacce ake zargin tana cikin ƙungiyar safarar yara zuwa ƙasashen waje.

ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja

Dukkaninsu suna hannun ’yan sanda.

Wata majiyar ’yan sanda ta bayyana cewa matar Onwe, mai suna Philomena Iroko, ce ta fallasa shi bayan ta samu labari daga maƙwabta cewa mijinta ya sayar da jaririn da suka haifa.

Da ta tabbatar da hakan, sai ta garzaya ta kai rahoto ofishin ’yan sanda, inda aka kama Onwe ba tare da ɓata lokaci ba.

Kakakin rundunar jihar Ebonyi, SP Joshua Ukandu, ya tabbatar da cewa an ceto jaririn daga hannun wacce ta saya shi.

Ya ce an kama Onwe da Chinyere Ugochukwu a ranar Juma’a a unguwar Azugwu, Ƙaramar Hukumar Abakaliki, kuma suna tsare a hannun ’yan sanda domin ci gaba da bincike.

Matar Onwe, Philomena, ta ce ta yi mamaki matuƙa cewa mijinta ya sayar da jaririn nasu.

Ta bayyana cewa tun bayan haihuwarta, Onwe, ya ce zai kai jaririn wajen ’yar uwarsa domin ta sa masa albarka, sai dai daga baya aka gano cewa ya sayar da shi.

Ta ce, “Yaronmu bai wuce kwanaki biyar da haihuwa ba, amma mijina ya sayar da shi.

“Ban taɓa tunanin zai yi haka ba. Ina roƙon jama’a da masu hannu da shuni su taimaka min a wannan hali da na tsinci kaina.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi
  • Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh
  • Yadda Ake Gurasa Ta Semovita
  • Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
  • Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi
  • Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
  • Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe
  • Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha
  • Haramcin Haƙar Ma’adanai: Majalisa Za Ta Kawo Ƙarshen Asarar Dala Biliyan 9 Duk Shekara