Majalisa ta yi watsi da zargin Amurka na yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya
Published: 9th, October 2025 GMT
Majalisar Wakilai, ta yi watsi da zargin da Ƙasar Amurka, ta yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.
Wannan martani na zuwa ne bayan wani Sanatan na Amurka, Ted Cruz, ya gabatar da ƙudirin doka a Majalisar Dattawan ƙasar, inda ya ce ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.
Sauye-sauyen Tinubu ba su rage talauci a Najeriya ba — Bankin Duniya Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahoton Bankin Duniya kan yawan talakawa a NajeriyaA yayin gabatar da ƙudirin ya buƙaci a ƙaƙaba wa wasu jami’an Najeriya takunkumi.
Cruz ya ce: “ Ana kashe Kiristocin Najeriya saboda addininsu… lokaci ya yi da za a ɗauki mataki na gaske kan jami’an Najeriya da ke taimaka wa irin waɗannan ayyuka.”
Sai dai ’yan majalisar Najeriya sun yi watsi da wannan batu.
Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu, ya ce wannan iƙirarin ba gaskiya ba ne game da halin da Najeriya ke ciki.
“Matsalar tsaro a Najeriya tana da yawa, ta’addanci, ‘yan fashi, rikicin manoma da makiyaya, kuma tana shafar mutane na kowane addini,” in ji Kalu.
“Ba daidai ba ne a fassara waɗannan matsaloli a matsayin hare-haren da gwamnati ke kai wa addini ɗaya ba.”
Majalisar ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta aike wa Amurka mar6a hukumance, tare da tattaunawa don fahimtar juna kan wannan lamari.
Haka kuma, ’yan majalisar sun buƙaci a gaggauta naɗa jakadun Najeriya a Amurka da Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, shi ma ya yi watsi da zargin Cruz, inda ya ce “ba gaskiya ba ne kuma babu wata hujja da ta tabbatar da hakan.”
“Ba gaskiya ba ne cewa an ƙome coci sama da 20,000 ko kuma an kashe Kiristoci 52,000,” in ji shi.
“Najeriya ƙasa ce mai addinai da dama. Babu wani jami’in gwamnati da zai goyi bayan tashin hankali a kan addini.”
Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta tabbatar da cewa an kai wa wasu Kiristoci hare-hare, amma ta ce matsalar tana shafar kowa, don haka gwamnati ta tabbatar da adalci.
“Kiristoci da dama sun rasa rayukansu a wuraren ibada,” in ji Archbishop Daniel Okoh, shugaban CAN.
“Muna kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su kare raykan dukkanin ‘yan ƙasa baki ɗaya, kuma a hukunta masu laifi.”
Majalisar ta jaddada cewa Najeriya na da ’yancin yin addini kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, tare da kira ga haɗin kai da fahimtar juna don kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ke shafar kowa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Wakilai Najeriya Watsi zargi yi watsi da
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan Najeriya miliyan 60 na fama da taɓin hankali – Likita
Wani Likitan ƙwaƙwalwa a Asibitin Neuropsychiatric Aro, a Abeokuta, Jihar Ogun, Dokta Emmanuel Abayomi ya ce kimanin mutane miliyan 60 ne ke fama da taɓin hankali a halin yanzu.
Ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma’a a Abeokuta a wajen wani taron ƙarawa juna sani da Ƙungiyar likitoci ta NAS ƙarƙashin Ƙungiyar masu ruwa da tsaki ta ƙasa ta shirya domin tunawa da ranar kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa ta duniya ta bana.
Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe ’Yan sanda sun ceto mutum 3 da aka sace a Kano da KadunaShirin da Ash Montana Deck tare da haɗin gwiwar Atlantis, Americana 1 da Longhorn Deck suka yi wanda ya ja hankalin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar.
Da yake bayani game da “Samar da kayan kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa a cikin yanayin agajin gaggawa,” Abayomi ya bayyana damuwa game da ƙaruwar matsalolin ciwon taɓin hankali a tsakanin ‘yan Najeriya.
Da yake ambaton Ƙididdigar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, masanin likitancin ya ce ɗaya daga cikin mutane takwas na fama da matsalar taɓin hankali.
Sai dai a Najeriya Abayomi ya ce adadin ya fi haka inda aka ƙiyasta kimanin ‘yan ƙasar miliyan 60 ne ke fama da matsalar taɓin hankali.
“A Najeriya, adadin ya haura, a gaskiya kimanin ’yan Najeriya miliyan 60, bisa ga ƙididdigar baya-bayan nan, suna fama da matsalar taɓin hankali.
Kuma idan aka dubi adadin ƙidayar ’yan ƙasar zuwa miliyan 200 ko miliyan 240, wannan na nuna ɗaya cikin mutum biyar ko ɗaya cikin mutane shida da ke da matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa.
“Don haka, yana da yawa kuma abin damuwa ne a Najeriya,” in ji shi.