A yau Jumma’a 10 ga watan Oktoba, an kaddamar da wani shiri na aikin hadin gwiwa mai lakabin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” na rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) na shekarar 2026 a birnin Beijing.

 

Shen Haixiong, babban darektan CMG, ya gabatar da jawabi a wajen taron, inda ya bayyana cewa, CMG ya samu damar zamowa kan gaba a fagen yada labarai na kasa da kasa bisa kayayyakin aiki da ma’aikata, kuma shi ne muhimmin dandali na tallata kayayyakin kasar Sin.

Kamfanin a shirye yake ya dauki shirin a matsayin wata damar yin aiki kafada da kafada da abokan kawance daga kowane bangare na rayuwa, tare da rubuta sabon babi a fagen gina kasa mai kunshe da kayayyakin kamfanonin da suka kasance a kan gaba. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka October 10, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata   October 10, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Gabatar Da Shawarwari Shida Game Da Karfafa Tsarin Shari’a Da Inganta Shugabanci A Duniya October 10, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya- Shugaba Tinubu

Daga Bello Wakili

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi cikin alhini da jimami.

Fitaccen malamin da ke Bauchi ya rasu ne a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2026, yana da shekaru 101.

Shugaban Ƙasan ya yi jimamin rasuwar jagoran Darikar Tijjaniyya, yana bayyana shi a matsayin ginshiƙin ɗabi’a wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da wa’azi.

Shugaba Tinubu ya ce rashinsa babban rashi ne ba ga iyalansa da dimbin mabiyansa kaɗai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.

Shugaban Ƙasa ya tuna da albarka da goyon bayan da ya samu daga marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a lokacin yakin zaɓen 2023.

“Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba, mai cike da natsuwa da hikima. A matsayinaa na mai wa’azi kuma masani kan tafsirin Alƙur’ani Mai Girma, yana da’awar zaman lafiya da tsoron Allah. Rasuwarsa ta bar babban gibi,” in ji Shugaban Ƙasa.

Shugaba Tinubu ya yi ta’aziyya ga mabiyan Shehun a ci da wajen ƙasa  bisa wannan babban rashi.

Haka kuma ya ja hankalinsu da su girmama sunansa ta hanyar bin koyarwarsa ta zaman lafiya, ƙarfafa dangantakarsu da Allah, da kuma kasancewa masu taushin zuciya ga jama’a.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya- Shugaba Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya
  • Gwamna Kefas Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta
  • Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta
  • Abbas Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Titi Mai Tsawon Kilomita 13 a ‘Yankwashi