Gwamnatin Neja Ta Bayyana Shirintan Hada Gwiwa Da NSME Domin Bunkasa Hako Ma’adinai
Published: 9th, October 2025 GMT
Gwamnatin jihar Neja ta bayyana shirinta na yin hadin gwiwa da kungiyar injiniyoyin ma’adanai ta Najeriya a matakin jiha da tarayya domin tabbatar da aiwatar da kudurorin da aka cimma a karshen taron kasa da kasa karo na ashirin da hudu.
Gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana bude taron shekara-shekara da taron kasa da kasa na shekara ashirin da hudu da aka gudanar a Minna babban birnin jihar Neja.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikata Injiniya Idris Abubakar ya bayyana cewa hakan ya zama dole domin dorewa da aikin hakar ma’adanai na da matukar muhimmanci wajen kare shirin makamashi maras illa a matsayin Jigon gwamnatin sa.
A nasa jawabin shugaban kungiyar injiniyoyin ma’adanai ta kasa ta Najeriya Dakta Umar Hassan ya ce duk da cewa akwai dokoki da ka’idoji amma aiwatar da su na da rauni sosai, wanda hakan ya faru ne saboda rashin isassun kudade na gudanar da ayyuka na ma’aikatun da hukumomin tare da yin kira da a dauki matakin don magance irin wadannan matsalolin.
Dokta Umar Hassan ya bayyana cewa ba za a iya gudanar da aikin hakar ma’adinai ba sai da isasshen tsaro domin ana samun ma’adanai a lunguna da sako na kasa sannan kuma masu hakar ma’adinai su yi aiki yadda ya kamata akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta yi duk abin da ya kamata don inganta a irin wannan yanayin.
Ita ma da take magana shugabar ma’adinan Najeriya ta kasa, Ms Rose Ndong wacce ta yabawa masu shirya taron kan shirya irin wannan taro mai tasiri wanda ta bayyana a matsayin wanda ya dace kuma a kan lokaci, ta ce dole ne Najeriya ta dauki jagoranci ta hanyar sarrafa arzikinta na ma’adinai yadda ya kamata.
Taken taron shi ne “Dorewar Ayyukan Hako Ma’adanai A Matsayin Mahimmancin Tallafawa Don Canjin Nijeriya Zuwa Tushen Makamashi”. a yayin da Gwamna Umar Bago na jihar Neja da wasu ‘yan Najeriya masu kishin kasa suka samu lambar yabo ta ‘yan uwa na Cibiyar, saboda hidimar da suke yi wa bil’adama.
COV Aiyu Lawal.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa
A yau Jumma’a 10 ga watan Oktoba, an kaddamar da wani shiri na aikin hadin gwiwa mai lakabin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” na rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) na shekarar 2026 a birnin Beijing.
Shen Haixiong, babban darektan CMG, ya gabatar da jawabi a wajen taron, inda ya bayyana cewa, CMG ya samu damar zamowa kan gaba a fagen yada labarai na kasa da kasa bisa kayayyakin aiki da ma’aikata, kuma shi ne muhimmin dandali na tallata kayayyakin kasar Sin. Kamfanin a shirye yake ya dauki shirin a matsayin wata damar yin aiki kafada da kafada da abokan kawance daga kowane bangare na rayuwa, tare da rubuta sabon babi a fagen gina kasa mai kunshe da kayayyakin kamfanonin da suka kasance a kan gaba. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA