Trump Ya ce An Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Yakin Gaza
Published: 9th, October 2025 GMT
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa Isra’ila da Hamas sun amince da matakin farko na yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
A wani sako da ya wallafa a kafarsa ta sada zumunta ya ce hakan na nufin nan ba da jimawa ba za a saki dukkanin wadanda ake garkuwa da su, sannan Isra’ila za ta janye dakarunta.
Ya ce wannan mataki ne na farko na tabbatar da zaman lafiya mai dorewa. “Za a yi wa kowane bangare adalci,” in ji Trump. Kungiyar Hamas ta tabbatar da cimma yarjejeniyar ta kawo karshen yakin Gaza bayan tattaunawa kan yarjejeniyar Donald Trump.
Hamas ta ce yarjejeniyar ta kunshi janyewar Isra’ila daga yankin da kuma musayar fursunoni da kuma mutanen da aka yi garkuwa da su.
Trump ya ce wannan babbar rana ce ga kasashen Larawaba da na Musulmi da Isra’ila da dukkanin kasashe da kuma Amurka. Sannan ya gode wa kasashen Qatar da Masar da Turkiya da ke shiga tsakani a tattaunawar tsakanin Hamas da wakilan Isra’ila da na Amurka.
Wannan na zuwa a daidai lokacin da shugaba Trump ya ce yana tunanin kai ziyara yankin Gabas Ta Tsakiya a karshen mako domin ganawa da kasar Masar a inda ake tattaunawar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka M D D Ta yi Kira Da A Kawo Karshen Yakin Gaza Da Aka Kwashe Shekaru 2 Ana Yi. October 9, 2025 Iran da Rasha Sun Tattauna Kan Yadda Za su Inganta Yin Aiki Tare A Bangaren Nukiliya. October 9, 2025 Natanyahu Ya Ce Makamai Masu Linzami Masu Keta Nahiyoyi Na Iran Barazana Ce Ga Amurka October 8, 2025 Iran Da Sauran Kasashe Na Bakin Tekun Caspian Sun Rattaba Hannu Kan Yarjeniyar Tsaron Tekun October 8, 2025 HKI Ta Kai Farmaki Kan Jiragen Ruwan ‘Sumud’ Kusa Da Gaza October 8, 2025 Iran Ta Bukaci Karin Taimako Daga MDD Don Kula Da Yan Gudun Hijiran Afganistan October 8, 2025 Burtaniya: An Ci Gaba Da Zanga-Zangar Goyon Bayan Falasdinawa Duk Tare Da Gargadin Jami’an Tsaro October 8, 2025 Qalibaf: Iran Ba Za Ta Yi Sassauci Kan Tsibiran Kasar Guda Uku Ba October 8, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Gayyaci Jakadun Kasashen Turai Don Gargadarsu October 8, 2025 Iran Ta Bayyana Aniyarta Ta Rashin Daina Samar Da Magunguna Ta Hanyar Fasahar Makamashin Nukiliya October 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila da
এছাড়াও পড়ুন:
China Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Harajin Trump A Kanta Na 100%
Kasar China ta maida martani kan kasar Donal Trump na kasar Amurka, wanda ya karawa kasar kudaden fito 100% na kayakin kasar da ke shigowa Amurka.
SHafin yanar gizo na ArabNews ya nakalto kasar China a jiya Asabar tana cewa zata dauki matakan da suka dace kan Karin kudanen fito na 100% wanda shugaban Trump yayi. Kuma ta yi kira ga Trump kan cewa ya rungumi tattaunawa da kasar China ya fi masa kan barazana gareta.
Ma’aikatar kasuwanci na kasar China ta bayyana cewa, basa son yakin kudaden fito amma basa tsoronta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Yi Girgizar Kasa Mai Daraja 5 A Ma’aunin Richter A Kasar Habasha October 12, 2025 Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta October 12, 2025 An Yi Musayar Wuta A Tsakanin Masu Tsaron Iyakokin Kasashen Afghanistan Da Pakistan October 12, 2025 Afirka Ta Kudu Ta Ce Babu Wata Makarkashiya A Mutuwar Jakadanta A Kasar Faransa October 12, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Yunkurin Balair Na Yiyuwar Shiga Gwamnatin Gaza. October 11, 2025 Cuba Ta Bayyana Bada Kyautar Noble Ga ‘Yar Kasar Veunzuelas machado A Matsayin Abin Kunya. October 11, 2025 Kasar Indunusiya Ta Hana Tawagar wasan Jiminastik din Isra’ila Visar Shiga Kasarta October 11, 2025 Ammar Hakim Ya Gargadi Kasashen Yamma Da su Kiyayi Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Kasar. October 11, 2025 Sarkin Morocco Ya yi Magana Tun Bayan Barkewar Zanga-zanga A Kasar . October 11, 2025 Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Iran Ya Ja Kunnen Amurka Kan Taba Jiragen Dakon Man Kasa October 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci