Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar
Published: 9th, October 2025 GMT
A bana, bikin Tsakiyar Kaka da Ranar Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin sun hadu, inda suka haifar da hutun tsawon kwanaki takwas. An yi hasashen cewa, adadin mutanen da suka yi tafiya a yankuna daban daban na kasar zai kai biliyan 2.432, tare da karuwar kashi 6.2% a kowace rana idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Duniya ta ga ci gaban Sin na dogon lokaci. A daidai wannan lokacin hutu, wasu tsirarun kasashe sun fara daukar sabbin matakan buga haraji, yayin da kasar Sin ke shirya sabbin damarmaki na bude kasuwarta ga duk duniya. Bugu da kari, a watan Oktoba da muke ciki, za a gudanar da cikakken zama na 4 na kwamitin tsakiya na 20 na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin a birnin Beijing, inda za a tsara shirye-shirye da dabarun ci gaban kasar na shekaru biyar masu zuwa, sannan a watan Nuwamba mai zuwa, za a sake bude baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su daga ketare zuwa nan kasar Sin karo na 8, inda kasashe da kungiyoyin duniya da dama suka tabbatar da halartar baje kolin, kuma kamfanoni sama da 3,200 daga kasashe da yankuna sama da 110 sun tabbatar da halarta. Kamar yadda kamfanoni na duniya da yawa suka bayyana cewa, kasuwar kasar Sin ta bambanta da ta sauran kasashe, wanda ke nuna damarmakin kasuwanci masu yawa da ba za a iya kubuce ba. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
Daga Bello Wakili
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa dawowar ’yan mata 24 da ’yan ta’adda suka sace a Maga, Jihar Kebbi.
’Yan ta’addan sun kai hari makarantar ranar 17 ga wantan Nuwamban 2026, inda suka yi awon gaba da ’yan matan, jim kaɗan bayan wata rundunar soji ta bar harabar makarantar.
Lamarin Kebbi ya haifar da wasu sace-sace makamanta a Eruku da ke Jihar Kwara da kuma Papiri a Jihar Neja.
An sako dukkan mutune 38 da aka sace a Eruku ranar Lahadi, inda a wannan ranar ce shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Jihar Neja ya ce an samu yara 50 daga cikin ɗaliban makarantar Katolika da suka ɓace a gidajen iyayensu.
Shugaba Tinubu ya yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suka yi wajen ganin an kubutar da dukkan mutanen da ’yan ta’adda suka sace.
Ya umarci jami’an tsaro da su ƙara ɗaukar matakan gaggawa don ceto sauran ɗaliban da har yanzu ke hannun ‘yan bindiga.
“Ina farin cikin cewa an samu dukkan ’yan mata 24. Ya zama wajibi mu ƙara tura jami’an tsaro yankunan da ke da rauni don hana sake faruwar irin wannan lamari. Gwamnatina za ta bayar da dukkan tallafin da ake buƙata don cimma haka,” in ji Shugaba Tinubu.