2025-11-18@09:04:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 11717
«Fareti»:
Iyayen ɗalibai ’yan mata 25 ’yan bindiga sace ɗakunan kwanansu a Jihar Kebbi sun bayyana irin tashin hankali da suka shiga bayan abin da ya faru. “Ita kaɗai gare ni,” in ji Malam Muhammad Maga, mahaifin Nafisa, wadda ita kadai ya haifa, kuma take cikin ɗaliban da ’yan bindiga suka sace a makarantar. Malam Muhammad...
“Cikin hukuncin Allah, sojojin Daularmu sun kama ‘Kwamandan Runduna’… bayan ya gudu daga harin kwantan-ɓauna… Bayan mun yi masa tambayoyi, Mujahidai suka kashe shi.” An kuma wallafa wani hoto a kafafen sada zumunta da ya nuna Janar Uba a ɗaure. Har yanzu rundunar sojin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa game da wannan lamari...
Ministan tsaron Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya kai ziyarar aiki a Hadaddiyar Daular Larabawa don inganta dangantakar soja da kuma huldar tsaro a yankin. Nasirzadeh ya jagoranci wata babbar tawaga, wadda ta isa Dubai a ranar Litinin bisa gayyatar takwaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa. Ministan tsaron Iran yana shirin yin tattaunawa da jami’an Hadaddiyar...
Masu gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) a ranar Litinin din nan sun bukaci kotun da ta zartar da hukuncin daurin rai da rai kan Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman, wanda aka fi sani da Ali Kushayb, kwamandan rundunar Rapid Support Forces (RSF), saboda rawar da ya taka a...
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da daftarin kudurin Amurka, don ba da izinin kafa Rundunar Tsaro ta Kasa da Kasa (ISF) a Zirin Gaza. Mambobi 13 daga cikin 15 na Majalisar sun amince da kudurin, inda Rasha da China suka kaurace wa kada kuri’ar. Kudurin yana da nufin tura sojojin kasashen waje...
Gwamna Ahmed Idris na Jihar Kebbi ya ba da tabbacin cewa jami’an tsaro za su ƙwato ’yan matan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kwalejin ’Yan Mata ta GGCSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasu ta jihar cikin ƙoshin lafiya. Gwamnan ya bayar da tabbacin ne a yayin ganawarsa da iyayen...
Ma’aikatar ma’adinai a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta sanar da tsawaita dokar hana fataucin ma’adinai na tsawon watanni shida daga wuraren hakar ma’adinai da dama a lardunan Kivu ta arewa da ta kudu da ke fama da rikici. Sabunta haramcin zai kara kawo tsaiko da cikas wajen samar da wasu ma’adanai a duniya, musamman ma’adaanai irin...
Kafofin yada labaran kasar Rasha sun rawaito a jiya Litinin cewa an dakile wani yunkurin kisan gilla kan sakataren majalisar tsaron kasar Rasha Sergei Shoigu a makabartar Troyekurov da ke birnin Moscow. Kafofin yada labaran kasar Rasha sun rawaito majiyoyi suna bayyana cewa wadanda suka aikata laifin sun yi yunkurin tayar da bam ne a...
Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana November 17, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing November 17, 2025 Daga Birnin...
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka kan sabon harin da ’yan bindiga suka kai makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, wanda ya kai ga sace ɗalibai mata sama da 25 tare da halaka mai gadi da mataimakin shugaban makarantar. A wata sanarwa da ta...
Alkaluman da suka fito daga kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin sun nuna cewa, adadin motocin da kasar Sin ke fitarwa waje ya karu da kashi 15.7 bisa dari a cikin watanni 10 na farkon shekarar 2025 bisa na makamancin lokacin bara. Kasar ta fitar da motoci sama da miliyan 5.6 a tsakanin...
Hukumar ƙwallon ƙafar Afirka CAF, ta bayyana cewa bayan tankade da rairaya da ta yi, a yanzu ’yan wasa uku kacal ne suka rage a takarar gwarzon nahiyyar na bana. A wata sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana Achraf Hakimi da Mohamed Salah da Victor Osimhen, a matsayin sauran ukun da...
A yau ne aka bude taron tattaunawa game da wayewar kai takanin Sin da kasashen Larabawa karo na 11, wanda sashen cudanya da kasashen waje na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin da sakatariyar kawancen kasashen Larabawa suka dauki nauyin shiryawa a Beijing. A gun taron, shugabanni na jam’iyyu da kungiyoyin siyasa, ‘yan majalisa, jami’an...
Gobara ta laƙume rayukan wasu yara biyu ’yan gida ɗaya a unguwar Rumuola da ke ƙaramar hukumar Obio/Akpor a Jihar Ribas. Bayanai sun ce ibtila’in ya auku ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Lahadi, lokacin da gobarar ta tashi a ɗaya daga cikin wasu ɗakunan haya da mahaifiyar yaran ta kulle ’ya’yanta...
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa birnin Moscow na kasar Rasha a yau Litinin domin halartar taro karo na 24 na majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO). Bisa gayyatar da firaministan kasar Rasha Mikhail Mishustin ya yi masa, Li zai halarci taron na SCO a ranakun 17 da 18...
Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun kashe wani babban kwamandan rundunar sojin Najeriya bayan wani harin kwantan ɓauna da aka kai wa tawagarsa a hanyar Damboa–Biu da ke Jihar Borno. Lamarin ya faru ne bayan da tawagar sojojin tare da dakarun haɗin gwiwa na Civilian Joint Task Force (CJTF) suka kai wani samame a yankin, inda suka...
Ya bayyana cewa, zaman bitar ya yi daidai da umarnin Sufeto Janar na ‘Yansanda, IGP Kayode Egbetokun, musamman kan karfafawa jami’an rundunar. Don haka, CP Bakori ya umurci Kwamandojin da su zurfafa wayar da kan jama’a a yankunan karkara da birane domin sanar da su irin rawar da suke takawa wajen wanzar da zaman...
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya bayyana cewa: Iran tana da kyakkyawar alaƙa ta musamman da kuma al’adu da membobin ƙungiyar haɗin gwiwa ta Shanghai Mataimakin Shugaban Kasa na Farko na Iran ya ce, “Iran tana da alaƙar haɗin gwiwa na musamman da al’adu da dukkan ƙasashe membobin Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai (SCO), kuma...
Na’ini: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Da Kansa Ya Jagoranci Yaki Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran
Jagoram juyin juya halin Musulunci da kan sa ya jagoranci yaki da harkokin al’umma a lokacin yakin wuce gona da iri na karshe kan Iran Kakakin Rundunar Tsaron kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), Brigadier Janar Ali Mohammad Na’ini, ya tabbatar da cewa: Maƙiya ‘yan sahayoniyya ba su da yanayin sabon yaƙi, kuma abin da...
Wata sanarwa da gwamnati ta fitar a Gaza ta yi gargadin cewa: Akwai wani bala’i da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin jin kai Ofishin Yada Labarai na Gwamnati a Zirin Gaza ya fitar da Sanarwar Manema Labarai Mai Lamba (1021) a yau, Litinin, inda ya yi magana kan sabbin ci gaba da...
Babban sakataren Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta HIzbullahi ta kasar Lebanon ya jaddada cewa: Gwamnatin Lebanon zata yi babban kuskure idan ta bi hanyar sassauci Babban Sakataren Kungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah Na’im Qassem ya bayyana cewa: Amincewa da yin shawarwari da gwamnatin mamayar Isra’ila da kuma amincewa da sharuddan da wakilin Amurka Tom Barrack ya...
Rushewar ramukan hako ma’adinai ta kashe ma’aikata 32 a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai 32 ne suka mutu a ranar Asabar sakamakon zaftarewar ƙasa a wani ma’adinan cobalt a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, yayin da ake ci gaba da neman waɗanda har yanzu ba a same su ba a yankin. Zaftarewar ƙasa...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama ƙunshi 66 na ganyen tabar wiwi a wani samame da ta kai a garin Deba, bayan samun wasu sahihin bayanan leƙen asiri. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ranar 16 ga Nuwamba,...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama ƙunshi 66 na ganyen tabar wiwi a wani samame da ta kai a garin Deba, bayan samun wasu sahihin bayanan leƙen asiri. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ranar 16 ga Nuwamba,...
Ya kuma yi Allah wadai da kisan wani jigo na Jam’iyyar APC, Umar Moriki, da kuma sace-sacen jama’a da aka yi a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, inda aka sace iyalai baki daya, ciki har da mata da yara. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda...
An sanya hannu kan yarjejeniyoyin cinikayya na biliyoyin kudi, a yayin baje kolin hajojin fasahohin zamani na kasar Sin ko CHTF, wanda aka kammala a jiya Lahadi a birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin. Wannan ne karo na 27 da aka gudanar da baje kolin na CHTF, inda aka kai ga daddale huldodin cinikayya da...
Shugaba Bola Tinubu a ranar Litinin ya gargadi jami’an shari’a a fadin kasar cewa dole ne a tabbatar da adalci ga kowa – Talaka da mai kudi, ba tare da nuna wata wariya ba, ko karɓar cin hanci, “bai dace adalci ya zama na sayarwa ba.” Da yake jawabi a yayin bude taron alkalan Nijeriya...
Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce hauhawar farashin kayyayaki a ƙasar ya ragu zuwa kashi 16.05 cikin 100 a watan Oktoban 2025. Cikin rahoton wata wata da hukumar ke fitarwa, ta ce hauhawar farashin ya ragu ne da kashi 1.97 idan aka kwatanta da kashi 18.02 da aka samu a watan Satumba. ’Yan Majalisar...
An ɗaura auren Sanatan Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila, da Aisha Isah, wata jami’ar soji a Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, a wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar sali-alin a Rano. Ɗaurin auren wanda jama’a kaɗan ne suka halarta ya gudana ne da safiyar Litinin ɗin nan a fadar Sarkin Rano da ke...
Ma’aikatar raya al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta fitar da sanarwa a jiya Lahadi, wadda ke kira ga al’ummunta da su yi taka-tsantsan a kwanakin nan wajen zuwa yawon bude ido kasar Japan. Game da hakan, masani a kwalejin bincike ta Nomura Takahide Kiuchi, ya bayyana a jiyan cewa, raguwar yawan Sinawa...
Bonzena ya ƙara da cewa duk da cewa kafin yanzu APC ce ke da rashin rinjaye a majalisar, an ci gaba da aiki cikin zaman lafiya, amma yanzu yana farin cikin ganin cewa dukkan mambobin majalisar sun haɗe ƙarƙashin tsari daya da ya yi daidai da hangen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA...
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Taraba, Rt Hon. Kizito Bonzena, tare da ’yan majalisar 15 sun sauya sheka daga jam’iyyarsu ta PDP zuwa APC. A saifyar Litinin ne Rt Hon. Kizito Bonzena ya gabatar da takardarsa ta ficewa daga PDP tare da sauran mambobin zuwa APC. Ya bayyana cewa da sauyin shekar tasu, yanzu APC ce...
Wasu masu ibadar Umara 42 sun mutu bayan da motarsu ta yi taho-mu-gama da wata tankar mai a kusa da birnin Madina da ke kasar Saudiyya. Dukkan masu ibadar ’yan kasar Indiya ne, kuma hatsarin ya ritsa da su ne a kan hanyarsu ta zuwa Makka bayan kammala ziyara a birnin Madina. Ministan harkokin wajen...
Tahotanni sun nuna cewa alummar kasar Ecodo sun yi fatali da shawarar bada damar dawo da sansanin sojin Amurka a kasar a wani zaben raba gardama da aka gudanar a kan batun. Dubban alummar kasar Ecodo ne suka hallar a gaban akwatunan zabe don bayyana ra’ayinsu na amincewa ko rashin amincewa da dawo da sansanin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi November 17, 2025 Manyan Labarai Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka November 17, 2025 Manyan Labarai Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar...
Rahotanni da suka fito daga yankin falasdinu sun tabbatar da cewa sojojin Isra’ila sun kai hari a sansanin yan gudun hijira dake gabar yammacin kogin Jodan kuma sun kashe wasu matasa guda biyu,da suka hada da jadalla jihar jumaa dan shekara 15 dake sansanin yan gudun hijira na fara’a a yammacin garin Tubas. Hukumar bada...
Tawagar wasannin Wushu na kasar Iran ta nuna rawar gani sosai a gasar hadin kan kasashen musulmi da ake yi a kasar saudiya inda ta samu lambobin yabo guda 4 wato Azurfa 1 tagulla 1 da kuma zinariya 2 a ranar karshe na gasa a wannan bangaren. A bangaren mata kuma Sara shafi’I wacce ta...
Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta kasar iran Mohammad Eslami ya bayyana cewa harin da Amurka da isra’ila suka kai kan tashohin nukiliyar ta a tsakiyar watan yuli ya nuna cewa Amurka da kawayenta ciki har da isra’ila suna harin naurorin kimiyya na jamhuriyar musulunci ta iran ne. Shugaban ya fadi hakan ne a wata hira...
Hamas Da Sauran Bangarorin Falasdinawa Sun yi Watsi Da Shirin Aikewa Da Dakarun Kasashen Waje A Yankin Gaza
Rahotanni sun bayyana cewa bangarorin falasdinawa sun yi watsi da kudurin da aka kaddamar ga kwamitin sulhu na majalsar dinkin duniya na shirin aikewa da sojojin ketare zuwa yankin Gaza sun yi kira ga kasar Aljeriya da sauran mambobin da ba na dindin ba a kwamitin sulhu da su kalubalance shi. Daftarin kudurin an tsara...
Ƴan bindiga sun kai hari a makarantar Government Girls Comprehensive Senior Secondary School (GGCSS), Maga, da ke ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a Jihar Kebbi, inda suka kashe Mataimakin Shugaban makarantar, Hassan Yakubu Makuku, tare da sace wasu ɗalibai mata da ba a san adadinsu ba. Al’ummar yankin sun ce harin ya sake tayar da hankula a...
’Yan ta’adda sun harbe Mataimakin Firinsifal har lahira, sa’annan suka yi garkuwa da dalibai 25 a Makarantar ’Yan Mata ta Gwamnati (GGCSS) da ke yankin Maga a Karamar Hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun bindige Malam Hassan Yakubu Makuku ne a yayin da yake kokarin kare daliban, a...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda November 17, 2025 Manyan Labarai Sarki Sanusi Ya Shawarci Unguwannin Da Suka Fuskanci Matsalar Tsaro Su Sa Idon November 17, 2025 Manyan Labarai Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja November 16, 2025...
Rundunar Ƴansandan birnin tarayya ta bayyana cewa babu wani rahoto ko bayanin da ta samu game da yunkurin kashe laftanar Ahmed Yerima, jami’in Sojin ruwa da ya yi taƙaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kan wani fili da ake jayayya kansa a Abuja kwanakin baya. Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar, SP Josephine Adeh, ta...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja November 16, 2025 Manyan Labarai Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su November 16, 2025 Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa za ta dauki mataki idan idan Kwamitin Gwamnonin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ya amince da wani sabon kuduri da bai dace da Iran ba. Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran Kazem Gharibabadi, ne ya bayyana hakan, a gefen taron kasa da kasa mai taken ‘’yancin kasa da...
A wani lokaci yau Litini ce kwamitin tsaro na MDD, zai kada kuri’a kan daftarin kudirin zaman lafiya na shugaban Amurka Donald Trump na Amurka kan Gaza. Kafin hakan Amurka ta sha matsin lamba ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya don amincewa da daftarin kudurin na Trump. Amurkar da wasu kawayenta na kasashen Larabawa...
’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu ’yan bindiga biyar tare da ƙwace tarin makamai a hannunsu a yankin Zuru–Tadurga da ke Jihar Kebbi. Rundunar ’yan sanda ta musamman da ta kama su, ta bayyana cewa, ’yan bindiga suna cikin waɗanda suka kai hare-hare a kan al’ummomin Zuru a kwanakin baya. Ta ƙara da cewa...
’Yan bindiga sun kashe mutum 3 tare da yin garkuwa da wasu 64 a ranar Asabar a Karamar Hukumar Tsafe ya Jihar Zamfara. Cikin waɗanda ’yan ta’addan suka kashe har da wani jigon jam’iyyar APC, Hon. Umaru Moriki wanda aka bindige a kan hanyar Gusau zuwa Tsafe, waɗanda aka yi garkuwa da su kuma har...
Kungiyar Ansarullah a Yemen ta yi Allah wadai da sabunta takunkumin Majalisar Dinkin Duniya Kan kasar tare da dake tabbatar da goyon bayanta ga Falasdinu. Kungiyar ta yi tir da matakin da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Dauka Na sabunta takunkumin Kan Yemen na wata Shekara, ta kuma yi Allah Wadai da son zuciyar...
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya ce kasarsa na binciken wani jirgin sama da ya kawo ‘yan gudun hijirar Falasdinawa 153 kasar ba tare da takardun shiga ba. “Wadannan mutane ne daga Gaza wadanda, ta wata hanya, suka tsinci kansu cikin jirgin sama da ya tashi daga Nairobi (babban birnin Kenya) kafin su...