Ma’aikatan jami’a sun yi zanga-zanga a Jami’ar Bayero
Published: 9th, October 2025 GMT
Mambobin Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i ta Najeriya (SSANU) da Ƙungiyar Ma’aikatan da ba Malamai ba (NASU) reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK), sun gudanar da zanga-zangar lumana.
Mambobin sun yi zanga-zangar ne a ranar Alhamis kan riƙe wasu haƙƙokinsu da suka zargi gwamnatin tarayya da yi.
Zanga-zangar da aka gudanar a cikin harabar jami’ar ta biyo bayan umarnin shugabannin ƙasa na ƙungiyoyin biyu, bayan ƙarewar wa’adin mako guda da ƙarin makonni biyu da suka ba gwamnatin tarayya.
Da yake jawabi ga manema labarai yayin zanga-zangar, Mataimakin Shugaban SSANU na Ƙasa shiyyar Arewa maso Yamma, Kwamared Sabo Balarabe Wudil, ya ce matakin ya zama dole sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen cika alkawuran da suka dade ana jira.
“Mun fito zanga-zanga ne saboda an yi watsi da bukatunmu na tsawon lokaci. Gwamnatin tarayya ta hana mu albashin watanni biyu da aka dakatar a lokacin yajin aikin 2022, ta gaza aiwatar da yarjejeniyar da muka cimma da ita a 2009, sannan ta yi watsi da biyan bashin albashinmu daga watan Janairu zuwa Disamban 2023,” in ji shi.
Wudil ya kuma koka kan rashin sakin Naira biliyan 40 na alawus-alawus ɗin da suke bi, inda ya ce gwamnati ta biya biliyan 10 ne kacal daga cikin biliyan 50 da aka amince da su tun 2022.
Ya ƙara da cewa, duk da yarjejeniyoyin fahimtar juna da aka rattaba hannu da gwamnati, ba a aiwatar da ko ɗaya daga cikinsu ba.
“Mu ƙungiyoyi ne masu son zaman lafiya. Muna so zaman lafiya ya wanzu, amma muna bukatar a yi mana adalci. Wannan zanga-zangar mataki ne na farko. Idan gwamnati ta gaza ɗaukar mataki ta hanyar share mana hawaye, shugabannin ƙasa na ƙungiyoyinmu za su yanke shawarar mataki na gaba,” in ji shi.
Da take karɓar takardar ƙorafin ma’aikatan a madadin Shugaban Jami’ar, Mataimakiyar Shugaban Jami’ar mai kula da Bincike da Ci gaba, Farfesa Amina Mustapha, ta tabbatar wa da ƙungiyoyin goyon bayan jami’ar.
“Ina so in tabbatar muku cewa Shugaban Jami’ar yana tare da ku a wannan fafutukar. Za mu isar da ƙorafinku ga hukumomin da suka dace,” in ji ta.
Aminiya ta rawaito cewa masu zanga-zangar na ɗauke da alluna masu rubuce-rubuce daban-daban kamar “Ku girmama ma’aikatan da ba malamai ba”, “Mun yi aiki, kun ki biyan mu. Ku saki albashin watanni biyu”, “Bashin albashi na 25%/35% haƙƙinmu ne” da “Ba ma son wani alkawari, a dauki mataki yanzu”, da sauransu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jami ar Bayero Kano zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka
An kulle Fadar Shugaban Kasar Amurka ta White House tare da wasu gine-ginen gwamnati da dama, sakamakon harbin ɗan bindigar da ya raunata sojoji biyu a kusa da fadar.
A yayin, an harbe masu tsaron fadar biyu har lahira.
Gwamna Patrick Morrisey da farko ya ce an kashe sojojin, amma daga baya ya ce yana samun “rahotanni masu karo da juna” game da halin da suke ciki, yana mai da cewa za a fitar da ƙarin bayani idan an tabbatar.
A cikin wani rubutu a shafin X, ya ce, “Yanzu muna samun rahotanni masu cin karo da juna game da halin sojojin biyu, kuma za mu bayar da ƙarin bayani idan mun samu cikakken rahoto.
“Addu’o’inmu suna tare da waɗannan jarumai, iyalansu, da dukan al’ummar Amurka.”
A cewar rahotanni, Shugaba Donald Trump yana gidansa na hutu a Mar-a-Lago da ke Palm Beach, Florida, a lokacin da lamarin ya faru.
Mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce cikin wata sanarwa: “Fadar White House ta san da wannan mummunan lamari kuma tana bin diddigi. Shugaban kasa ya samu cikakken bayani.”
’Yan sandan birnin Washington DC sun ce an kama wanda ake zargi da harbin.
Sojojin National Guard sun kasance a Washington DC tsawon watanni a matsayin wani bangare na matakin Trump na yaki da laifuka a babban birnin ƙasar.
A cikin wani rubutu a dandalinsa na Truth Social, Trump ya ce: “Dabban da ya harbi mambobin National Guard biyu, wanda dukkansu suka ji rauni mai tsanani kuma yanzu suna a asibitoci daban-daban, shi ma ya ji rauni sosai, amma duk da haka, zai ɗanɗana kuɗarsa.”