2025-11-25@00:25:03 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3093
«Yankwashi»:
Ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na gyaran tattalin arziƙi da kuma dawo da amincewa ga tsarin kwangilolin gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru...
Daga Khadijah Aliyu An fara shirye-shirye gudanar da taron shekara-shekara karo na 2 da bikin shigar da sabbin mambobi na Ƙungiyar Masana Harkokin Yada Labarai ta Najeriya (SNB), bayan an kaddamar da Kwamitin Shirya Taron (LOC) a Kano. An tsara gudanar da taron ne daga ranar 20 zuwa 21 ga watan Nuwamban 2025. Shugaban Ƙungiyar,...
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kwara ta ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su ba tare da wata illa ba, a kauyen Igbonla. A cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta rundunar, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi, ta fitar, ta ce rundunar ta samu kiran gaggawa cewa wasu ’yan bindiga sun kutsa cikin...
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin dan majalisar tarayya mai wakiltar Mazabar Agwara/Borgu a Jihar Neja, Honarabul Jafaru Mohammed Ali. Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne a jiya, a kauyen Kubul, kan hanyar Agwara zuwa Babana, a cikin Karamar Hukumar Borgu, yayin da dan majalisar ke hanyarsa ta...
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa rundunar Sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa gaggawar daukar mataki kan hare-haren ‘yan bindiga da suka faru a wasu sassan jihar. Gwamnan ya yi wannan yabo ne a lokacin da Babban Hafsan Runduna ta 1, wato GOC 1 Division da ke Kaduna, Major Janar Abubakar...
Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi tsokaci game da matakin Amurka na sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake da damuwa a kansu, inda ta jaddada matsayin Sin na matukar goyon bayan gwamnatin Najeriya, wajen jagorantar al’ummarta zuwa turbar neman ci gaba bisa yanayin da kasar ke ciki. A ’yan kwanakin...
A yau Talata ne firaministan Sin Li Qiang, ya gana da kakakin majalisar wakilan tarayyar Najeriya Tajudeen Abbas, wanda ya isa birnin Shanghai don halartar baje kolin CIIE karo na takwas. Yayin zantawarsu, Li Qiang ya bayyana aniyar kasar Sin ta karfafa salon wanzar da ci gaba bisa manyan tsare-tsare tare da Najeriya, da zage...
Majalisar Wakilai ta dakatar da zamanta na tsawon mako guda, sakamakon zanga-zangar da wasu ’yan kwangila suka gudanar a ƙofar shiga ginin majalisar dokoki ta ƙasa da ke Abuja, saboda rashin biyan kuɗaɗen ayyukan da suka kammala tun shekarar 2024. Rahotanni sun ce ’yan kwangilar sun yi dandazo ne a ƙofar shiga majalisar a ranar...
Kakakin Dakarun Kare Juyin Juya Halin Mususluni na bayyana yaƙin kwanaki 12 kan Iran ya tabbatar da cewa ba za a taɓa amincewa da Amurka ba Kakakin Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ya tabbatar da cewa: Yakin kwanaki 12 da aka yi da Iran ya nuna rashin amana ga masu yanke shawara na...
Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon ya bayyana cewa; Gwagwarmaya ta tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila rashin girke sojojinta a kan iyakar da ke tsakanin Isra’ila da Lebanon Kakakin Majalisar Dokokin Lebanon Nabih Berri ya tabbatar da cewa: “Gwagwarmaya ta yi cikakken biyayya ga sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma sojojin Lebanon sun tura sojoji da jami’ai sama da...
Yayin da yake gabatar da motocin, Gwamna Zulum ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na samar da tallafin kayayyaki ga jami’an tsaro a kowane lokaci. Ya jaddada cewa, tsaro wani bangare ne na muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba. Zulum ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu da jami’an tsaro kan kokarin...
Ya ƙara da cewa yana cikin farin ciki ganin yadda Gwamna Douye Diri ya fice daga jam’iyyar, inda ya ce, “Shi da Makinde sun taɓa cewa ba za su bari a lalata PDP ba ko a jawo ta ƙasa, amma ga su yanzu; su ne suka faɗi ƙasa.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kalaman...
Natasha ta bayyana dakatar da ita a matsayin mataki wanda ba na doka ba, tana mai cewa hakan ya nuna yadda tsoro da barazanar siyasa ke rinjayar halayen jami’an gwamnati. An dakatar da Sanata Natasha a watan Maris saboda zargin da ya shafi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, amma ta koma kujerarta a watan Satumba...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na fadada ayyukan ci gaban karkara, tare da aiwatar da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’umma. Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin jami’in kula da shirin rage radadin illar da annobar cutar Korona ta haifar,...
Wasu rahotanni na cewa dakarun RSF a kasar Sudan, sun hallaka fararen hula kusan 2000 a birnin El Fasher, fadar mulkin jihar arewacin Darfur. Kuma tuni MDD, da kungiyar tarayyar kasashen larabawa ta AL, da kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da ma wasu karin hukumomin kasa da kasa suka fara mayar da hankali kan yanayin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano November 3, 2025 Manyan Labarai Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso November 3, 2025 Manyan Labarai Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta ayyana ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo. Wannan mataki da rundunar ta ɗauka na zuwa ne bayan zargin Sowore da yunƙurin ta da zaune tsaye da kawo hargitsi da sunan zanga-zanga a Jihar Legas. Kano Pillars ta...
A ranar Litinin jami’an tsaro da dama sun hallara a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja yayin da Abdulrahman Mohammed Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa (Arewa ta Tsakiya), ya yi ikirarin cewa, ya karɓi mukamin Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar na Kasa a yayin da rikicin shugabancin Jam’iyyar ke kara tsananta. Kwamitin gudanarwar jam’iyyar na ƙasa (NWC)...
Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na NNPP a zaben 2023, ya fitar da wata sanarwa mai karfi yana gargadin cewa kalaman Trump na iya kara ruruta wutar rikicin addini da kuma kara ta’azzara rashin tsaro a kasar. A shafinsa na X, tsohon gwamnan ya yi Allah-wadai da matakin Trump na...
Daga Aminu Dalhatu Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa Shugaban Karamar Hukumar Gusau, Alhaji Abubakar Imam, bisa shirin tallafawa jama’a domin dogaro da kai da kuma inganta rayuwarsu. Ta yi wannan yabo ne yayin bikin kaddamar da kayan tallafi a Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Hajiya Huriyya Dauda Lawal...
Daga Aliyu Muraki Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Kasa reshen Jihar Nasarawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya Lafia ta bi umarnin ƙungiyar ta ƙasa wajen shiga yajin aiki na ɗindindin. Wakilinmu wanda ya ziyarci asibitin koyarwar, ya bayar da rahoton cewa likitocin sun bar wuraren aikinsu domin matsin lamba ga gwamnatin tarayya ta...
“Wannan yajin aikin yana nan yana gudana, har sai an biya duk buƙatunmu mafi ƙaranci,” in ji shi. NARD ta fara yajin aiki na sai baba-ta-gani a duk faɗin ƙasar a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, bayan abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnati na cika jerin “mafi ƙanƙancin buƙatunta.” Wannan...
Daga Usman Mohammed Zaria Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Injiniya (Dr.) Muhammad Uba, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa amincewa da sabbin ayyukan gina hanyoyi a fadin jihar, ciki har da na Birnin Kudu. Ya ce wannan mataki na cikin ajandar gwamnati 12, musamman wajen inganta ci gaban ababen more rayuwa....
Wani magidanci, Malam Jibrin Rabi’u, ya bayyana yadda matarsa, Khadijat Ado, ta ɓace a gidansu da ke unguwar Life Camp a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata, sannan kuma aka gano ta a Sakkwato washegari. Ya shaida wa wakilinmu da yammacin Lahadi, cewa ya dawo gida a ranar Alhamis, sai ya tarar da matarsa...
Kwankwaso ya kuma buƙaci gwamnatin Tarayya da ta ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da Amurka ta hanyar naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin kare muradun Nijeriya a matakin ƙasa da ƙasa. “Ya kamata gwamnatin Nijeriya ta naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin wakiltar muradunmu yadda ya kamata a kasashen waje,” in...
Allah Ya yi wa fitaccen jarumin Kannywood, Mato Na Mato, wanda aka fi sani da Malam Nata’ala a cikin shirin Dadin Kowa rasuwa. Wannan na cikin wani saƙo da fitacciyar marubuciya, Fauziyya D. Sulaiman ta wallafa a shafinta na Facebook a daren ranar Lahadi.
An ture Mataimakin Gwamna Gefe, Tsarin karba-karba Na Goyon Bayan Kwara ta Arewa. Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak, zai kammala wa’adinsa na biyu a shekarar 2027, amma babu wata alamar cewa mataimakinsa, Mista Kayode Alabi, zai gaje shi. Yanayin siyasa a jihar na nuna cewa yankin Sanatocin Kwara Arewa ne ake sa ran zai samar...
Manajar ofishin na NIWA, da ke a jihar ta Legas Injiniya Sarat Braimah ta bayyana cewa, tura ma’ikatan hukumar domin yin aikin, zai taimaka wajen gudanar da aikin a cikin inganci. Kazalika, ya sanar da cewa, hakan zai kuma bayar da damar yin safarar kaya a cikin sauki da kuma safarar matafiya da ke bin...
A yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da ke zargin gwamnatin Nijeriya da watsi da batun kisan Kiristoci a ƙasar, Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta bayyana cewa ta fara shirin kai farmaki a Nijeriya. Sakataren Ma’aikatar, Pete Hegseth, ne ya tabbatar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa...
Bug da kari Tinubu ya jinjina wa Shugaban jami’ar, Farfesa Wahab Olasupo Egbewole (SAN)da ‘yan tawagarsa wajen maida hankalin da suka yi na bunkasa Jami’ar da kumna kudurinta na muradun ci gaban da ake bukata. Shi ma anashi jawabin Shugaban Jami’ar Sarkin Katsina, Alhaji. Abdulmumin Kabir Usman, wanda Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Idah ya wakilta,...
Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da cewa daga lokacin da aka tsayar da wuta zuwa yanzu adadin Falasdinawan da HKI ta kashe sun kai 200, yayin da wasu kusan 600 sun jikkata. Sanarwar ta ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta kuma ci gaba da cewa; A cikin sa’o’i 48 da su ka gabata,an...
Daga Abdullahi Shettima Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna. Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin...
A wani bidiyo daban da PUNCH Metro ta gani a Facebook, wanda Mc Pee ya wallafa, wani mutum da ake zargin dalibi ne na jami’ar ya bayyana abin da ya faru. A cewarsa, marigayin ya roki a bar shi ya rayu kafin daga bisani wanda ake zargin ya kashe shi. Ya ce: “Nanpon ya riga...
Daga Usman Muhammad Zaria Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar. Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne...
Daga Usman Muhammad Zaria Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar. Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne...
Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar nuna goyan baya ga wani kudiri da ya jaddada cewa shirin da Morocco ta gabatar kan Yammacin Sahara shi ne mafita ‘’mafi dacewa” ga yankin da ake takaddama a kai. Kudirin ya nuna goyan bayan kasashe mambobin kwammitin ga shirin na Morocco, tare da bayyana cewa...
Harkokin siyasa na Kudancin Kaduna ya dauki wani salo yayin da dan majalisar da ke wakiltar mazabar Jema’a/Sanga a majalisar tarayya, Hon. Dan Amos, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP, yana mai cewa ya dauki wannan mataki ne domin ya hada kai da gwamnatocin jiha da na tarayya don cigaban...
Sanata Sunday Marshall Katung, wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, ya sanar da hukuncin da ya yanke na komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai cewa wannan mataki ne da ya dace domin inganta aikin wakilci da kuma tabbatar da ƙarin haɗin kai ga al’ummar mazabarsa. A cikin wata sanarwa...
A wani rahoto da miami herald ya wallafa a jiya jumaa ya nuna cewa kasar Amurka na shirin kaiwa kasar Venuzuwela hare hare, yayin da Donald trump shugaban kasar Amurka yake musantawa cewa babu wani shiri na daukar matakin soji a kasar ta latin Amurka. Yace gwamnatin trump ta yanke shawarar kai hari kan wasu...
A cewarsa, ta hanyar wadannan shirye-shirye, kasar Sin ta nuna goyon baya mai dorewa ga kasashe masu tasowa kuma tana ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban duniya a karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada...
Ya kuma bayyana cewa kasar Sin wuri ne mai kyau ga harkokin zuba jari ga ‘yan kasuwa na duniya. Ya ce hadin gwiwa da kasar Sin yana nufin hadin gwiwa da damammaki, imani da kasar Sin yana nufin imani da kyakkyawar makoma, zuba jari a kasar Sin yana nufin zuba jari mai riba ta...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da fasinjoji a cikin wasu motocin bas Toyota guda biyu a titin Itobe zuwa Ajegwu-Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi. An samu rahoton cewa, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 5 na asubahi a tsakanin...
A jawabinsa yayin taron, Gwamna Sani ya gabatar da kasida mai taken: “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa”, inda ya bayyana yadda Jihar Kaduna ke ci gaba da samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma, da tsarin tallafiwa jama’a. Gwamnan Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne...
Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede
“Iyakar kasa ba wai kawai yanki ne na tsaro ba. Yanki ne na al’adu; yanki ne na tarihi; haka nan ma yanki ne na tattalin arziki. Kula da shige da fice na da matukar amfani ga ci gabanmu. Wajibi ne Nijeriya ta zuba jari a kan kula da nau’in mutanen da take tacewa wajen shiga...
Sudan ta yi kira ga Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya sanya rundunar Rapid Support Forces (RSF) a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda bisa ga ka’idojin yaki da ta’addanci na duniya, sannan ya dauki mataki a kan duk wanda ya yi mu’amala da ita, ko ya samar mata da makamai da sojojin haya, ko jiragen...
Gwamna Inuwa ya kuma jaddada bukatar bin ka’idojin kariya a harkokin sufurin ruwa, inda ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomi, da shugabannin al’umma, da direbobin kwale-kwale da hukumomin da ke da ruwa da tsaki da sauran wadanda suka dace su kara kaimi wajen ganin ana kiyaye duk ka’idojin kariya don magance sake afkuwar ibtila’in...
Idan ka duba tarihin duniya gabadaya da tarihin annabawa, tarihi ne na wayewar duniya tun daga Annabi Nuhu (S.A.) har zuwa Manzon Allah (S.A.W.) kamar duniya tana ‘yar makaranta ce ta fara da Nazare, ta zo Firamare zuwa Sakandire har zuwa Jami’a, sannan aka yaye ta, yanzu da zuwan Manzon Allah an yaye duniya, yanzu...
Shugabannin Rundunar tsaro da Tinubu ya sallama sun hada da shugaban rundunar tsaro ta kasa Janar Christopher Musa da shugaban sojojin ruwa, Emmanuel Ikechukwu Ogalla da shugaban sojojin sama Hassan Abubakar. Wadanda suka maye gurbin su da idanu ya koma kan hobbasar kwazon da za su nuna su ne shugaban rundunar tsaro Olufemi Oluyede, shugaban...
Madagascar ta sanar da kafa sabuwar gwamnati wadda ta kunshi fitattun ‘yan adawa guda uku a manyan mukamai na ministoci. An gabatar da majalisar ministoci mai mambobi 29, wacce ta kunshi mata 10, a wani biki da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Yavoloha da ke babban birnin kasar, Antananarivo. Shugaban rikon kwarya Michael Randrianireina ya...