Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
Published: 2nd, November 2025 GMT
A yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da ke zargin gwamnatin Nijeriya da watsi da batun kisan Kiristoci a ƙasar, Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta bayyana cewa ta fara shirin kai farmaki a Nijeriya.
Sakataren Ma’aikatar, Pete Hegseth, ne ya tabbatar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, yana mai cewa ma’aikatarsa “na shirye-shiryen ɗaukar mataki” bayan umarnin da Trump ya bayar.
“Muna shirye-shirye don ɗaukar mataki a Nijeriya. Idan gwamnatin Nijeriya ba ta kare Kiristoci ba, za mu kai hari, mu kawar da ‘yan ta’addan Musulmai da ke aikata wannan ta’asar,” in ji Hegseth.
Trump dai ya yi wannan barazanar ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a Truth Social, inda ya ce Amurka za ta dakatar da duk tallafin da take bai wa Nijeriya, kuma tana iya “shiga ƙasar da ƙarfin soji domin share ‘yan ta’addan da ke kashe Kiristoci.”
“Idan gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da duk wata tallafi, kuma mai yiwuwa ta shiga wannan ƙasar, ta cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’addan Musulmai masu zafin kishin addini,” in ji Trump.
Ya kuma gargaɗi gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta ɗaukar mataki, yana cewa idan Amurka ta kai farmaki “za ta yi shi cikin sauri, da tsananin ƙarfi, da gamsuwa.”
Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan Trump ya mayar da Nijeriya cikin jerin ƙasashen da za a sanyawa ido, yana zargin cewa “ana yi wa Kiristoci kisan gilla” a hannun ƙungiyoyin Musulmi masu tsattsauran ra’ayi.
Sai dai a martanin da ya mayar, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasa mai dimokuraɗiyya wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ‘yancin yin addini da haƙuri tsakanin mabambantan addinai.
“Tun daga shekarar 2023, gwamnatinmu tana gudanar da tattaunawa sosai da shugabannin addinai na Kiristanci da Musulunci, tare da ci gaba da magance matsalolin tsaro da ke shafar ‘yan ƙasa daga addinai da yankuna daban-daban,” in ji Tinubu.
A cewar mai ba wa Tinubun shawara na musamman kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala, za a yi ganawa tsakanin Shugaba Tinubu da Shugaba Trump “a cikin kwanaki kaɗan masu zuwa” domin tattaunawa da warware wannan saɓanin fahimta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Nijeriya gwamnatin Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
Daga Usman Muhammad Zaria
Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne.
Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar.
Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban birnin jihar, kara habaka ci gaban birane, tare da samar da ayyukan yi ga matasan jihar.
Ya ce an tsara wannan asusu ne domin tabbatar da dorewa, ta yadda za a ci gaba da zuba jari a ayyukan samar da gidaje masu araha a fadin jihar.
Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana da kudirin ci gaba da inganta rayuwar al’ummarta, ta hanyar ayyuka masu amfani da jama’a, da ke inganta walwala, karfafa tattalin arziki, da tallafa wa matasa.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gyara da inganta gidan baki guda biyu (Malam Adamu Chiroma House da kuma Senator Francis Ella House) da ke cikin G9 Quarters a Dutse, da kudin sama da naira miliyan 219.7.
Ya ce aikin zai haɗa da cikakken gyara da inganta gine-ginen, gyaran hanyoyin ruwa da kuma girka tankokin ruwa ga kowanne daga cikin gidajen biyu.
Ya ce hakan na da nufin tabbatar da wadataccen ruwan sha mai dorewa a wuraren.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, amincewar da aka yi da wannan kwangila na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da dukiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa gine-ginen gwamnati suna cikin yanayi mai kyau da nagarta.